Anthony Joshua ya gwabje Andy Ruiz Jr a babban wasan damben Duniya

Anthony Joshua ya gwabje Andy Ruiz Jr a babban wasan damben Duniya

Anthony Joshua ya karbe kambunsa na babban wasan dambe a wata gagarumar karawa da ya yi a Saudi Arabiya inda ya nunawa Andy Ruiz Jr bajintarsa wannan karo a duka zagayen 12.

‘Dan wasa Anthony Joshua ya samu ramuwar gayyar da ya ke nema tun a lokacin da Andy Ruiz ya doke sa a Birnin New York a farkon bana. Wannan karo Joshua ya nunawa Ruiz da sauransa.

Bayan wannan nasara, Joshua ya samu kambu 2, daidai da Muhammad Ali, Mike Tyson da Lennox Lewis. An yi wannan wasa ne a kasar Sahara a Diriyah, a wani fili mai cin mutum 15, 000.

Anthony Joshua ya fito da shirinsa. A zagaye na takwas, Ruiz ya nemi ya yi wa Joshua irin dukan da ya taba yi masa. ‘Dan wasan bai karaya ba, inda a zagayen karshe ya koyawa Ruiz Jr. hankali.

KU KARANTA: A matse na ke in samu Miji in yi aure - Jarumar Hausa

A tashin farko, Joshua ya toshe Ruiz Jr. har jini ya fito masa a fuska. A zagaye na biyu shi ma Joshua ya samu rauni a saman idanunsa a dalilin wani mummunan nushi da Ruiz ya kai masa.

Rahotannin Sky Sports sun ce damben jiya ya na cikin wasanni mafi kyau da Anthony Joshua ya yi a rayuwarsa. Fitaccen ‘Dan damben Turan ya natsu ya kwantar da hankalinsa a wannan karo.

A zagaye na hudu, kararrawa ce ta cecei Joshua inda Ruiz Jr. ya nemi ya kai Joshua kasa. Joshua ya na tsakiyar jin wuju-wuju a hannun wanda ya doke shi a baya kenan, sai aka buga kararrawa.

Daga baya Joshua ya yi nasarar jefa Abokin fadan na sa a tarkonsa kamar yadda Mai horas da shi, Rob McCracken ya nuna masa. Gwarzon ya na da tatso da jinin Yarbawa a Kudancin Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel