'An Riga An Rubuta Sakamakon Zaben 2027," Kalaman Kakakin Majalisa Sun Tada Ƙura
- Rt. Hon. Udeme Otong, ya yi ikirarin cewa an riga an kammala rubuta sakamakon zaben majalisar dokokin Akwa Ibom na 2027 tun yanzu
- Otong ya ce tikitin APC guda 26 na majalisar jihar suna hannunsa, kuma babu wanda zai zama dan majalisa ba tare da yardarsa ba
- Wata kungiyar APC ta yi Allah-wadai da kalaman na shugaban majalisar jihar, tana mai cewa ya sabawa dimokuradiyya da dokokin APC
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Uyo - Kakakin majalisar Akwa Ibom, Rt. Hon. Udeme Otong, ya jawo ce-ce-ku-ce da fushin jama’a bayan ikirarin da ya yi cewa an riga an rubuta sakamakon zaben ‘yan majalisar jihar na 2027.
Udeme Otong ya yi ikirarin cewa shi ne ke da ikon yanke hukunci kan wanda zai samu tikitin takara karkashin jam’iyyar APC don shiga majalisar dokokin jihar.

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Source: Twitter
Shugaban majalisa ya bugi kirji kan 2027
A cikin wani bidiyo da Legit Hausa ta gani a shafin Facebook na wani Itoro Etti, an ga Udeme Otong yana buga kirji da cewa babu wanda zai zama dan majalisar dokokin Akwa Ibom sai da amincewarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin majalisar ya fadi hakan ne a yayin wata ziyarar girmamawa da wata kungiyar siyasa ta Ibom-DGI ta kai masa a gidansa da ke Abak Itenge, domin murnar cikar sa shekaru a 2025.
Otong ya ce:
“Dukkan tikitan takarar majalisar suna aljihuna. Tikiti 26 duk suna wurina. Ni kadai na yi sulhu na samo su. Ni ne zan zabi wanda zai zama dan majalisa, in ciro tikitin daga aljihuna in ba shi.”
Sauye-sauyen sheka daga PDP zuwa APC
Jihar Akwa Ibom na da ‘yan majalisa 26. Da fari dai, dukkaninsu ‘yan jam’iyyar PDP ne, amma dai a watan Yuni, 2025, ‘yan majalisa 24 sun sauya sheka tare da Gwamna Umo Eno zuwa APC.
Gwamna Eno ya ce ya tuntubi bangarori daban-daban, ciki har da majalisar dokoki, kafin yanke shawarar ficewa daga PDP, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Bayan sauya shekar, jita-jita suka fara yawo cewa an yi wa ‘yan majalisar alkawarin komawa kai tsaye kujerunsu a zaben 2027 domin su bi gwamnan zuwa APC.
Akwai sahihanci a kalaman kakakin majalisar?
Jaridar Premium Times, ta rahoto cewa shugaban majalisar dokokin, Otong, wanda ke bugin kirji game da zaben, ya na wakiltar mazabar Abak ne, kuma yana wa’adinsa na biyu a majalisar.
A cikin bidiyon, Otong ya kara da cewa ba wanda zai fito takarar majalisa sai da yardarsa, yana mai cewa za a ba da tikitin ne ga mutanen da gwamna zai ji dadin aiki da su.
Har yanzu dai ba a tabbatar ko gwamna Umo Eno ko APC sun amince da irin wannan yarjejeniya ba, wadda za ta iya sanya zabukan fitar da gwani na jam'iyyar su zama marasa ma’ana.
Shugabar APC a jihar, Stephen Ntukekpo, da kakakin jam’iyyar, Otoabasi Udo, ba su amsa kiran manema labarai domin yin karin bayani ba.

Source: Original
Kungiyar APC ta yi Allah-wadai
Kungiyar APC Media Network, wadda ke da alaka da jam’iyyar APC a Akwa Ibom, ta fitar da sanarwa tana sukar furucin kakakin majalisar.
Daraktan kungiyar, Iniobong John, ya bayyana cewa kalaman Otong na nuna rashin bin ka’idar dimokuradiyya, tare da bata sunan jam’iyyar APC.
Kungiyar ta ce Otong ba shi da ikon kundin tsarin mulki da zai ba shi damar tantance ‘yan takarar jam’iyyar, tana jaddada cewa irin wannan iko yana hannun hukumomin jam’iyya ne kadai.
Mutane sun soki dan majalisar Akwa Ibom
A wani labarin, mun ruwaito cewa, dan majalisar wakilan tarayya, Hon. Clement Jimbo daga jihar Akwa Ibom ya fara shan suka daga ƴan Najeriya kan haɗakar ADC.
Hon. Clement Jimbo ya kwatanta haɗakar da ƴan dawa suka ƙulla a ADC da mummunan hatsarin jirgin ADC Airline da ya faru a 2006, hakan ya harzuƙa jama'a.
Mutane sun maida wa dan majalisar masa martani mai zafi kan wannan kalamai da ya yi, suna cewa bai kamata ya yi ba'a da hadarin da aka rasa rayukan 'yan kasa ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

