Jerin Jihohin da Suka Taba Yin Kasafin Kudin da Ya Haura Naira Tiriliyan 1 a Najeriya
Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta gabatar da kasafin kudin shekara mai kamawa watau 2026 a gaban Majalisar Dokokin Jihar.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wannan shi ne kasafin kudi mafi tsoka da aka taba yi a tarihin jihar Kano, wanda zai lakume sama da Naira tiriliyan 1.3.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Kano ce ta fara kasafin kudi akalla N1trn?
Yayin gabatar da kasafin, Gwamna Abba ya jaddada kudirin gwamnatinsa na gudanar da mulki a bude tare da maida hankali kan ayyukan da za su inganta walwalar al'umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da ba Kano ce jiha ta farko da ta yi kasafin kudin da ya haura Naira tiriliyan daya ba, amma ba kasafai ake samun jihohi sun yi irin haka ba a Najeriya.

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka, Trump ya kara daukar zafi, ya kira Najeriya da kalma mara dadin ji
Jihar Legas ita ce a sahun farko a karfin tattalin arziki a tsakanin jihohin Najeriya, wanda ya sa ta yi kasafin kudi na sama da Naira tiriliyan daya sau da dama.
Jihohin da suka taba kasafin akalla N1trn
A Arewa, za mu iya cewa Kano ce ta farko ta tabo wannan adadi bayan jihar Neja, wannan ya sa muka tattaro muku duka jihohin da suka yi kasafin da ya kai N1trn a Najeriya.
1. Jihar Legas
Jihar Legas ce ta farko daga cikin jihohin Najeriya da ta fara karya wannan tarihi, ta yi kasafin kudin da ya haura Naira tiriliyan daya akalla sau hudu.
Gwamna mai ci, Babajide Sanwo-Olu, wanda ya hau mulki a shekarar 2019, shi ne ya fara gabatar da kasafin kudin shekara wanda ya zarce Naira tiriliyan guda a tarihin Legas.
A 2022, Gwamna Sanwo-Olu ya yi kasafin kudin da ya lakume Naira tiriliyan 1.758, yayin da a 2023 kuma ya yi wanda ya kai N1.768trn, sai kuma a 2024 da kasafin ya ci N2.268trn.

Source: Facebook
A wannan shekara da muke ciki ta 2025, Legas ta sake kafa tarihi, inda ta zama jiha ta farko a Najeriya da ta yi kasafin kudin da ya kai Naira tiriliyan 3.367.
Gwamnatin Legas ta yi kiyasin samun kudin shiga Naira tiriliyan 2.968, wanda ya kunshi Naira tiriliyan 2.230 daga kudaden shiga na cikin gida (IGR), Naira biliyan 111.839 daga hannayen jari, da Naira biliyan 626.137 daga asusun tarayya.
2. Jihar Ribas
Jihar Ribas, wacce ta sha fama da rikicin siyasa a farkon wannan shekara, na cikin wadanda suka yi kafin kudin da ya haura Naira tiriliyan guda a Najeriya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya dokar ta baci a Ribas tare da dakatar da gwamna mai ci, Siminalayi Fubara da 'yan Majalisar dokoki na tsawon watanni shida.
Sakamakon takaddamar da aka yi tsakanin Gwamna Fubara da 'yan Majalisa kan kasafin kudin 2025, Shugaba Tinubu ya jagoranci sake gabatar da kasafin ga Majalisar tarayya.

Source: Twitter
Bussiness Day ta rahoto cewa a watan Mayu, Majalisar dokokin kasa ta zartar da kudirin kasafin kudin jihar Ribas na Naira tiriliyan 1.48 na shekarar 2025, wanda shi ne karo na farko da ya kai wannan adadi.
3. Jihar Neja
A karon farko a tarihi, Gwamna Mohammed Umaru Bago ya yi kasafin kudin da ya kai adadin N1.558 a shekarar 2025, kamar yadda This Day ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Kiraye kiraye sun yawaita, ana son Tinubu ya yi murabus daga shugabancin Najeriya
Gwamna Bago ya gabatar da wannan kasafi a gaban Majalisar dokokin jihar Neja a watan Disamba, 2024 kuma majalisa ta amince da shi mako guda bayan haka.

Source: Twitter
A cewar gwamnan, kasafin kudin 2025 na da nufin karfafa ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin jihar da kuma dorewar tubalin da ya kafa na gina sabuwar Neja.
Wannan ya sa Neja ta zama jiha ta farko a jihohin Arewacin Najeriya da ta fara yin kasafin kudin da ya haura Naira tiriiliyan daya.
4. Jihar Ogun
A 2025, Gwamnatin Ogun karkashin Gwamna Dapo Abiodun ta yi kasafin kudi na Naira tiriliyan 1.05, wanda ta ce an yi shi ne don aiwatar da ayyukan da za su sanya jihar a kan hanyar ci gaba da wadata.
Kwamishinan Kudi na jihar, Dapo Okubadejo ya ce kudin shigar Ogun ya karu daga Naira biliyan 335 a 2020 zuwa Naira tiriliyan 1.1 sakamakon gyare-gyaren da aka yi da kuma toshe hanyoyin fitar da kudi ba bisa ka'ida ba.

Source: Facebook
Ya ce gwamnatin Abiodun ta ƙara yawan kuɗin shiga na cikin gida (IGR) ta hanyar gyare-gyare da yawa a fannoni kamar su filaye, biyan kuɗi, masana'antu, ciniki da saka hannun jari.
Vanguard ta ruwaito kwamishinan ma cewa:
"Mun kuma yi gyare-gyare da yawa na cikin gida don haɓaka inganci da kuma canza tsarin ayyukan samun kuɗin shiga na cikin gida ta hanyar fasahar zamani."
5. Jihar Kano
A ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamba, 2025, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kudin 2026 wanda zai lakume Naira tiriliyan 1.368 ga majalisar dokokin jihar Kano.
Wannan shi ne karo na farko a tarihin jihar Kano da aka yi kasafin kudi mai girman da ya haura Naira tiriliyan daya.

Source: Facebook
Kasafin kudin ya ƙunshi kashi 68 cikin 100 na manyan ayyuka, wanda ya kai N934.6bn, yayin da kudin gudanar da gwamnati ya tsaya a N433.4bn, wato 32%.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa shafinsa na Facebook, Abba ya ce gwamanatinsa na sa ran tara kudin kasafin daga bangarori da dama.
"Mun inganta hanyoyin tara kudin cikin gida kuma mun rufe kofofin ɓarna, lamarin da ya ba mu damar tsara manyan ayyukan ci gaba a shekarar 2026," in ji Gwamna Abba.
6. Jihar Delta
Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya shirya gabatar da kasafin kuɗi da ya haura Naira tiriliyan ɗaya (N1tn) a shekarar kuɗi ta 2026.
Gwamnan ya ce manufar hakan ita ce inganta ci gaban tattalin arziki da gina muhimman ayyukan raya ƙasa a fadin jihar, kamar yadda The Nation ta kawo.

Source: Facebook
Oborevwori ya bayyana hakan ne jiya yayin wani taron jin ra'ayoyin jama’a kan tsara kasafin kuɗi, wanda aka gudanar a Unity Hall, Fadar Gwamnatin jihar da ke Asaba.
Kwamishinan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Mr. Sonny Ekedayen, ne ya wakilci Gwamna Oborevwori a wurin taron.
Ya bayyana cewa an ware kashi 67% na kasafin kuɗin ga ayyukan ci gaba, yayin da kashi 33% za su tafi ga bangaren harkokin gudanar da gwamnati.
Kasafin 2025: Najeriya za ta ciyo bashi
A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta kammala muhawara kan bukatar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta sake dauko wa Najeriya bashin makudan kudi.
Tun farko, Shugaba Bola Tinubu ya nemi izinin Majalisar Dattawa na sake karbo lamunim Naira tiriliyan 1.15 daga kasuwar bashi ta cikin gida domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2025.
A cewar Tinubu, za a yi amfani da kudintaimaka wajen cike gibin kuɗi da tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen gwamnati da ayyuka da ke cikin kasafin kuɗin shekarar 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



