Trump: Minista Ya Fadi dalilin Tinubu na Ba Shi Muƙami, Ya Ƙaryata Kisan Kiristoci
- Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya, Festus Keyamo SAN ya rubuta wasika da kuma martani da Donald Trump
- Ya ce Tinubu na girmama addinai, ya nada shi saboda shi Kirista ne, sannan yawancin shugabannin tsaro a Najeriya Kiristoci ne
- Hakan ya biyo bayan barazanar da Trump ya yi ga Najeriya na daukar matakin soji kan zargin yi wa Kiristoci kisan gilla
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya rubuta budaddiyar wasika ga Shugaba Donald Trump.
Festus Keyamo ya yi kira ga Donald Trump ya kara bincike kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Source: Twitter
Keyamo ya rubuta wasika inda ya ce Najeriya ba kasa ba ce da gwamnati ke zaluntar Kiristoci, kuma shi Kirista ne mai tsayin daka, cewar Leadership.

Kara karanta wannan
Kisan kiristoci: Ministan Tinubu, Keyamo ya tura budaddiyar wasika ga Shugaba Trump
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dalilin Tinibu na nada ni minista' - Keyamo
Keyamo ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada shi ne minista ne saboda kyakkyawar dabi'a, kishin kasa da tushensa a matsayin Kirista.
Ya ce ba zai taba yarda ya yi aiki a gwamnati mai cin zarafin Kiristoci ba, saboda hakan saba wa imani da dabi’u ne.
Ya yi bayanin cewa Tinubu Musulmi ne mai matsakaicin ra’ayi kuma yana da matarsa Kirista wacce take fasto a babban coci.
Haka nan, ya ce yawancin ‘ya’yansa Kiristoci ne, yana nuna kyakkyawan misalin zaman lafiya tsakanin addinai.
Yadda rashin tsaro ya shafi dukan addinai
Keyamo ya kara da cewa matsalolin tsaro a Najeriya na faruwa tun shekaru da dama, ciki har da Boko Haram, makiyaya da barayin shanu.
Amma ya ce wadannan rikice-rikice ba wai na addini ba ne, suna shafar Musulmi da Kiristoci irin guda.
Ya bayyana cewa shugaban kasa ya gaji wadannan matsaloli amma ya dauki matakai masu karfi don magance su.
Ya ce mafi yawancin manyan hafsoshin tsaro Kiristoci ne, don haka ba za a ce suna yarda da zalunci ga Kiristoci ba.
Keyamo ya ce doka ta tabbatar Najeriya kasa ce madaidaiciya wacce ba ta daukar addini daya a matsayin na gwamnati.
Ya ce kundin tsarin mulki ya bai wa kowa ‘yancin addini da ikon gudanar da ibada cikin kwanciyar hankali.

Source: Getty Images
Rokon Keyamo ga Donald Trump
Ministan ya bayyana cewa akwai yan adawa ma suna yarda cewa babu wani shiri na kisan Kiristoci a Najeriya.
Ya ce gwamnatoci na baya da na yanzu suna yin kokari wajen kare rayukan ‘yan kasa ba tare da wariya ba.
Ya roki Trump da gwamnatin Amurka su yi amfani da ingantattun bayanai kafin yanke hukunci, cewar rahoton Punch.
Ya ce wannan lokaci ne da ake bukatar karfafa hadin kai da goyon baya, ba zargi maras tabbaci ba.
Keyamo ya tunatar da cewa Najeriya na son zaman lafiya da Amurka don cigaba da hadin gwiwa wajen yaki da ta’addanci da bunkasa dimokuradiyya.
Fasto ya gargadi Tinubu game da Trump
Kun ji cewa malamin addini Kirista, Elijah Ayodele, ya gargadi Bola Tinubu bayan Shugaba Donald Trump ya yi wa Najeriya barazana.
Fasto Ayodele ya ce ya dade da gargadin Tinubu game da makircin Amurka kan gwamnatinsa da kuma matsalolin tsaro.
Ayodele ya ce dole ne Tinubu ya magance matsalar tsaro, domin hakan na iya kawo cikas ga nasararsa a zaben 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

