Tsohon Darektan DSS Ya Tsoratar da Najeriya a kan Barazanar Trump, Ya Bada Mafita

Tsohon Darektan DSS Ya Tsoratar da Najeriya a kan Barazanar Trump, Ya Bada Mafita

  • Tsohon darektan DSS, Mike Ejiofor, ya bukaci gwamnati ta dauki maganganun Donald Trump da muhimmancin gaske tare da daukar mataki
  • Ya bayyana cewa daga cikin abin da ya dace Najeriya ta yi, akwai neman hanyoyin diflomasiyya wajen warware sabani da gwamnatin Amurka
  • Ejiofor ya yi gargadin cewa barazanar Trump ba wasa ba ce, dole ne a dauki mataki cikin gaggawa domin kawo afkuwar mummunan lamari

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon darektan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Mike Ejiofor, ya bukaci gwamnatin tarayya ta dauki zargin kisan Kiristoci da muhimmanci.

Ya kuma bukaci kasar ta dauki barazanar harin soja da shugaban Amurka Donald Trump ya yi da matuƙar muhimmanci.

An shawarci Bola Tinubu a kan Amurka
Shugaba Bola Tinubu, Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Bayo Onanuga/Donald J Trump
Source: Twitter

Ejiofor ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels Television a ranar Talata.

Kara karanta wannan

"Najeriya ba ta da damar goyon bayan kisan addini": Minista ya karyata Trump a idon duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Trump: Tsohon darekta a DSS ya gargadi gwamnati

Daily Post ta ce Mike Ejiofor ya jaddada cewa wajibi ne gwamnati ta gaggauta amfani da hanyoyin diflomasiyya domin kaucewa tashin hankali.

Ya kara da cewa:

“Ina ganin ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki Donald Trump da muhimmanci. Ina kira ga gwamnati ta binciki duk hanyoyin diflomasiyya domin magance wannan batu."

Ya kara da cewa ya kamata a damu da barazanar da Trump ya yi na kawo hari Najeriya saboda zargin cewa gwamnati ta bari ana kashe kiristoci da gangan.

Ejiofor: Ba wasa Shugaba Trump ya ke yi ba

Tsohon darektan DSS ɗin ya ce ko da yake tsaron ƙasa alhakin gwamnati ne, dole ne ta kauce wa duk wani rikicin diflomasiyya da zai iya lalata dangantaka da ƙasashen waje.

Ejiofor ya shawarci Najeriya ta bi a hankali
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Twitter

Ya jaddada cewa yin amfani da dabarun diflomasiyya cikin gaggawa shi ne mafita mafi dacewa don kare martabar ƙasar da mutuncinta a idon duniya.

Kara karanta wannan

'Ba na jin tsoron Trump,' An samu sabani tsakanin Barau da Akpabio a majalisa

A kalamansa:

“Donald Trump mutum ne da yake faɗa da cikawa. Wannan ba wasa ba ne, barazana ce da za ta iya janyo matsala idan ba a yi hattara ba."

Baya ga barazanar kawo hari, Trump ya ce zai dakatar da duk wani tallafi da ake kawo wa Najeriya saboda zargin kisan kiristocin.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta zargin, tana mai cewa ba a taba nuna wariyar addini a ƙasar ba, domin kundin tsarin mulki yana kare ‘yancin addini ga kowa.

An gano dalilin Trump na waiwayar Najeriya

A baya, mun wallafa cewa Farfesa Jibrin Ibrahim ya bayyana cewa barazanar Donald Trump ba ta da wata alaka da batun kiristoci a kasar kamar yadda ya bayyana a farko.

Jibrin Ibrahim, wanda ya ke masanin siyasa ne a kasar nan, ya bayyana cewa al'amarin da ake gani yanzu ba wani abu ba ne da ya wuce siyasar duniya da Trump ke bugawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zargin kisan kiristoci: Wike ya zargi 'yan adawa da wuce gona da iri wurin yada karya

Ya kara da cewa daga cikin abubuwan da ya jawo matsala a tsakanin Najeriya da Amurka shi ne alakar kasar nan da China ta fuskar kasuwanci da sauran mu'amala.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng