Yan Majalisar Amurka Sun Nunawa Trump Yatsa, Sun Soki Barazanarsa ga Najeriya
- Lamari ya fara sauya salo a Amurka bayan barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi kan Najeriya a kwanakin nan
- ’Yan majalisar Amurka biyu sun saba da matakin da Trump ke niyyar dauka kan Najeriya bayan zargin kisan Kiristoci
- Mambobin majalisar sun soki barazanar da Trump ya yi ga Najeriya, suna kiran hakan da rashin hankali da ganganci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya fara samun cikas kan barazanar da ya yi ga Najeriya.
’Yan majalisar Amurka biyu sun soki matakin Trump ga Najeriya bayan zargin kisan Kiristoci da aka sha musantawa.

Source: Getty Images
Yan majalisar biyu, Gregory W. Meeks da Sara Jacobs, sun soki barazanar Donald Trump ta dakatar da tallafi da fara harin soja kan Najeriya, cewar rahoton Anadolu Ajansi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barazanar da Trump ya yi ga Najeriya
Hakan ya biyo bayan barazanar daukar matakin soji da Donald Trump ya yi kan Najeriya a kwanakin nan.
Trump na zargin gwamnatin Najeriya da sakaci wanda ya jawo ake kisan Kiristoci ba tare da kakkautawa ba.
'Yan Najeriya da dama musamman manyan siyasa kamar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun nuna damuwa kan kalaman Trump.
Abin da 'yan majalisan Amurka suka ce
Meeks da Jacobs wadanda mambobin kwamitocin harkokin waje da Afirka, sun bayyana furucin Trump a matsayin “rashin hankali da ganganci,” suna jaddada cewa Najeriya tana fuskantar rikici mai sarkakiya.
A sanarwarsu, sun ce sanya Najeriya cikin jerin “kasar da ake damuwa da ita” ya yi watsi da yanayin rikice-rikice da ke da nasaba da ƙalubalen ƙasa da ƙasa.
Sun bayyana cewa rikicin manoma da makiyaya ba na addini kadai ba ne, amma yana da alaƙa da karancin albarkatu da takaddamar mallakar ƙasa a yankuna.
’Yan majalisar sun tunatar da cewa ta’addanci da hare-haren barayin daji sun kashe Kiristoci da Musulmai, musamman yankin Arewa mai fama da hare-haren ’yan ta’adda da barayin daji.

Source: Twitter
'Yan majalisar sun fadi abin da Najeriya ke bukata
Sun ce duk ’yan Najeriya suna bukatar kariya, kuma sun yarda cewa Shugaba Tinubu na kokarin karfafa zaman lafiya tsakanin addinai da magance matsalar tsaro.
Sun yi Allah-wadai da barazanar Trump ta cewa zai “kare Kiristoci” ta hanyar yiwuwar mamayar soja, suna kiran wannan magana ta rikice sakamakon bayanan da ba su da tushe.
Sun bayyana cewa yin barazanar harin soja rashin hankali ne, saboda taimakon tsaro abu ne dabam, amma maganar shiga yaki ba tare da dalili ba abu ne mai hatsari.
’Yan majalisar sun kuma ce yanke tallafi ga Najeriya zai lalata shirin agaji da kawo ci gaba, ciki har da abinci da horon masu yakar tashin hankali.
Barazanar Amurka: Fasto ya sake gargadin Tinubu
A baya, mun ba ku labarin cewa fitaccen malamin addinin Kirista a Najeriya ya gargadi Shugaba Bola Tinubu game da barazanar Amurka a kasar.
Fasto Elijah Ayodele ya gargadi Tinubu kan zargin kisan Kiristoci da Amurka ke ta yadawa, yana cewa akwai shirin kawar da gwamnati.
Ayodele ya ce ya dade yana gargaɗi game da hatsarin Amurka ga gwamnatin Tinubu inda ya ce suna shirya manakisa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


