Bayan Barazanar Trump, Jirgin Shettima Ya Bar Najeriya zuwa Kasar Waje
- Kashim Shettima ya tafi Brazil don wakiltar Shugaba Bola Tinubu a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (COP 30)
- Taron zai gudana daga ranar 6 zuwa 7 ga Nuwamba, 2025 a birnin Belém, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Luiz da Silva
- Shettima zai gabatar da jawabi a madadin Najeriya, zai halarci wasu taruka, ya kuma gana da mataimakin shugaban Brazil
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja — Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi (COP 30).
Za a gudanar da taron COP 30 a ƙasar Brazil, kuma zai gudana ne daga ranar 6 zuwa 7 ga Nuwamba, 2025, a Belém, babban birnin jihar Pará, dake tsakiyar dajin Amazon.

Source: Twitter
Shetima zai halarci taron COP 30 a Brazil
An shirya taron ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, tare da haɗin gwiwar sauran ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare muhalli, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Stanley Nkwocha, mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasa, Shettima zai haɗu da shugabannin ƙasashe, da manyan masu ruwa da tsaki domin tattaunawa kan sauyin yanayi da hanyoyin rage illarsa.
Taken taron bana shi ne "Aiki da Aiwarar da Matakan Sauyin Yanayi", inda za a tattauna batutuwa kamar daidaita muhalli, kare dazuka, da daidaita bukatun yanayi.
Shettima zai gabatar da jawabi a Brazil
A ranar farko ta taron, Shettima zai halarci babban zama na shugabannin duniya, inda ake sa ran zai gabatar da jawabi a madadin Najeriya kan matakan gwamnati na kare muhalli da sauyin yanayi.
Za a tattauna yadda Najeriya ke aiwatar da manufofin rage hayaki da kare albarkatun ƙasa ta hanyar makamashin hasken rana, iska da ruwa.
Shettima zai kuma halarci ƙaddamar da asusun TFFF, karkashin shirin da zai tallafawa ƙasashe masu dazuka wajen kare su daga gobara da kwarar hamada.

Kara karanta wannan
Daga shiga APC, Gwamna Diri ya yi wa Tinubu alkawarin kaso 99 na kuri'u a zaben 2027
Daga nan, Shettima zai shiga tattaunawa da shugaban ƙasar Brazil, Luiz Lula da Silva, a kan yanayi, kafin daga bisani ya halarci liyafar shugabannin ƙasashe da Lula zai shirya.
Tattaunawa kan makamashi da yarjejeniyar Paris
A rana ta biyu, Shettima zai shiga taruka biyu da shugaban Brazil zai jagoranta. Na farko zai mayar da hankali kan sauya tsarin makamashi yayin da na biyu zai tattauna kan yarjejeniyar Paris da yadda ƙasashe ke aiwatar da alkawuransu.
A cikin wannan tattaunawa, Najeriya za ta jaddada bukatar ƙarin tallafi daga ƙasashen da suka ci gaba domin aiwatar da shirin NDCs, domin rage illar hayaki, in ji rahoton Punch.
A yayin zaman, ana sa ran mataimakin shugaban ƙasa zai bayyana sababbin shirye-shiryen gwamnatin Tinubu wajen samar da makamashin sola a yankunan karkara, da kuma bunkasa hanyoyin kasuwanci mai dorewa.

Source: Twitter
Najeriya za ta amfana da kasuwar Carbon
A gefen taron COP 30, Shettima zai gudanar da wasu tarurruka na musamman da abokan hulɗa domin tabbatar da shigar Najeriya cikin kasuwar carbon, wanda zai iya samar wa ƙasar $2.5bn zuwa $3bn a kowace shekara.

Kara karanta wannan
Bayan Tinubu ya naɗa sababbin hafsoshin tsaro, an canjawa Janar sama da 60 wurin aiki
Ana sa ran Shettima zai tattauna da shugabannin ƙasashe da masu saka hannun jari kan yadda kasuwar carbon za ta ƙarfafa tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
Bayan kammala taron COP 30, Mataimakin Shugaban Ƙasa zai zarce zuwa Brasilia, inda zai gana da Mataimakin Shugaban Ƙasar Brazil, Geraldo Alckmin.
Ana sa ran Shettima zai dawo gida bayan kammala wannan muhimmin aiki na diflomasiyya da kare muhalli.
Shettima ya halarci taron WEF a Switzerland
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Kashim Shettima, ya ziyarci birnin Davos na ƙasar Switzerland domin halartar taro kan tattalin arziƙi.
Kashim Shettima ya wakilci Najeriya a wajen taron shekara-shekara kan tattalin arziƙin duniya (WEF) na shekarar 2025 da aka yi a birnin Davos.
Mataimakin shugaban ƙasan wanda ya samu rakiyar manyan jami'an gwamnati da suka haɗa da ministoci ya kuma gana da shugabannin kasashe daban daban.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
