Shugabannin kasashe 10 da suka fi arziki a tarihin duniya
Ba abin mamaki bane cewa manyan shugabanni daga kasashe daban-daban na duniya suna da wadata sosai.
Wasu daga cikinsu an haife su ne a cikin dangin masu arziki, yayin da wasu suka hau tsanin dukiya ta hanyar gaskiya.
Ba tare da la’akari da hanyoyinsu na samu ba, jeranta shugabannin kasashe mafi arziki abu ne mai wahala, sakamakon yadda komai da aka sani a rayuwa ba shi da tabbas.
Domin kuwa masu iya magana na cewa, "idan yau kaine gobe waninka ne". Haka ya ke ko a sha'anin dukiya, yau ka samu, gobe kuma ka rasa. Kazalika idan wani ya fi ka, to kai ma ka fi wani.

Asali: Original
Babu ko jayayya cewa, kudi da samun alfarma na daga cikin muhimman sabubba masu taka rawar gani wajen mutum ya zama shugaban kowace kasa a fadin duniya.
Ana bukatar tsabar kudi wajen yakin neman zabe, da kuma daga daraja da matsayin kowane ɗan siyasa.
Yawancin shugabannin masu arziki, wadanda suka fito daga nahiyoyi daban-daban, sun kasance mutane ne da za su iya daukewa kan su duk wata bukata da jin dadi na rayuwa gwargwadon damar da Mai Duka ya ba su.
A kididdigar da shafin yanar gizo na MSN ya fitar, shugabannin kasashe mafi arziki a tarihin duniya su ne:
10. Zine El Abidine Ben Ali ($10 billion)

Asali: Twitter
Ben Ali shi ne tsohon shugaban kasar Tunisiya. Ana ikirarin cewa shi ya ke sarrafa kashi 30 zuwa 40 cikin 100 na tattalin arzikin kasar. An tube shi daga kujerar mulki a shekarar 2011.
9. Mobutu Sese Seko ($12 billion)

Asali: Instagram
Sese Seko ya kasance tsohon shugaba mai mulkin mallaka kasar Zaire daga shekarar 1965 har zuwa 1997. A yanzu an fi sanin sunan kasar da Jamhuriyar Congo.
Saboda tsananin wadatar sa, ya mallaki manyan gidaje da wuraren shakatawa a Zaire da kasashen waje.
8. José Eduardo dos Santos ($20 billion)

Asali: Instagram
José Eduardo dos Santos, shi ne tsohon shugaban kasar Angola, ya jagoranci kasar tun daga shekarar 1979 zuwa 2017.
Ya tara dimbin dukiya da arziki a lokacin da yake kan karagar mulki. 'Yarsa, Isabel, tana daya daga cikin mata mafi arziki a Afirka a yanzu.
7. Ibrahim Babangida ($22.7 billion)

Asali: UGC
Ibrahim Badamasi Babangida, shi ne tsohon shugaban kasar Najeriya a lokacin mulkin soja. Ya jagorancin kasar daga shekarar 1985 zuwa 1993.
6. Ferdinand Marcos ($53.1 billion)

Asali: Twitter
Ferdinand Marcos ya mulki kasar Philippines daga shekarar 1972 zuwa 1986. An san shi da auren wata matar da ta ke da sha'awar abubuwa mafi kyawu a rayuwa.
5. Suharto ($55 billion)

Asali: Instagram
Suharto, wani tsohon shugaban kasar Indonesia ne, yana daya daga cikin shugabannin kasa mafi karfin iko ta fuskar arziki a duniya.
Ya shugabanci kasar na tsawon shekaru 31 kafin yayi murabus a shekarar 1998. Darajar dukiyar da ya mallaka ta kai dala biliyan 54.2 gabanin ajali ya katse masa hanzari a shekarar 2008.
4. Ali Abdullah Saleh ($64 billion)

Asali: Twitter
Ali Abdullah Saleh shi ne shugaban kasar Yemen tun daga shekarar 1990 har zuwa 2012.
A cewar wani rahoto da kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gabatar a shekarar 2015, Ali Abdullah Saleh yana da kudin da yawansu ya kai dala biliyan 64 tun daga shekarar 2015
3. Hosni Mubarak ($70 billion)

Asali: Instagram
Mubarak ya kasance tsohon shugaban kasar Masar. An hambarar da shi daga mulki a shekarar 2011 a lokacin zanga-zangar guguwar sauyin kasashen larabawa bayan ya shafe shekaru 30 a kan mulki.
2. Vladimir Putin (over $200 billion)

Asali: UGC
Mai shekaru 56 a duniya, shahararren dan siyasa a kasar Rasha kuma tsohon jami'in leken asiri, Vladimir Putin, ya kasance na biyu a jerin manyan shugabannin kasashe 10 mafi arziki a tarihi.
1. Muammar Gaddafi ($200 billion)
Babu tantama tsohon shugaban mulkin mallaka na kasar Libya, Muammar Gaddafi, shi ne ya fi kowane shugaban kasa arziki a tarihin duniya.
Ya jagoranci kasar Libya tun daga shekarar 1977 zuwa 2011. Gabanin a kashe shi a shekarar 2011, ya tara dimbin dukiya da ta kai kimanin dala biliyan 224.8.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng