Shugaban Jami'a a Abuja Ya Bayyanawa Matasa Hanyoyin Magance Talauci

Shugaban Jami'a a Abuja Ya Bayyanawa Matasa Hanyoyin Magance Talauci

  • Shugaban Jami’ar ASE da ke Abuja, Farfesa Mahfouz Adedimeji, ya ja hankalin matasa kan neman na kansu a rayuwa
  • Farfesan ya bayyana ilimi, kwarewa, da samar da kayayyakin da kasuwa ke bukata a matsayin hanyoyin dogaro da kai
  • Malamin ya kuma yaba da manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ce suna da kyau

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban Jami’ar African School of Economics (ASE) da ke Abuja, Farfesa Mahfouz Adedimeji, ya bukaci matasan Najeriya da su fara neman na kansu.

Farfesa Adedimeji ya bukaci matasa su farka daga dogaro da gwamnati su kuma dauki matakan da za su ba su damar gujewa talauci da mawuyacin halin tattalin arziki.

Mahfouz Adedimeji
Shugaban jami'ar ASE, Farfesa Mahfooz Adedimeji. Hoto: Mahfouz Adedimeji's Blog
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Farfesan ya bayyana hakan ne yayin wata takarda da ya gabatar a taron wata-wata na UNILOMGA.

Kara karanta wannan

Trump ya sa Najeriya a jan layi kan zargin kashe Kiristoci, Amurka za ta yi bincike

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya gudanar da takardar ne a ranar Lahadi, 26, Oktoba, 2025, domin tunawa da cika shekaru 50 da kafuwar jami’ar.

Hanyoyin da za a bi a yaki da talauci

Farfesan ya ce tun daga zamanin falsafar Girka an tabbatar cewa manyan bukatun dan Adam su ne abinci, tufafi da muhalli, wanda duk suna karkashin tattalin arziki.

Adedimeji ya bayyana cewa idan aka tabbatar da wadatar wadannan bukatu na farko, da dama daga cikin matsalolin da ke damun jama’a za su ragu.

Leadership ta rahoto ya ce wannan ne ya sa Jami’ar ASE ke horar da dalibai a fannin fahimtar tattalin arziki a kowane mataki.

Shugaban jami'ar ya ce hanyar da mutum zai tsere daga talauci ita ce ta neman ilimi, koyon sana’a da samar da kayayyakin da kasuwa ke bukata.

Hanyar inganta tattalin arzikin matasa

Farfesan ya kara da cewa rage kashe kudi da kuma kara hanyoyin samun kudin shiga na daga cikin dabarun da suke tabbatar da nasara wajen rage matsin tattalin arziki mai cike da kalubale.

Kara karanta wannan

'A tsorace suke': Issa Tchiroma ya zargi gwamnatin Kamaru da sace iyalansa

Ya kuma shawarci matasa su rungumi aikin sa-kai domin samun gogewa da damar da za su amfane su a gaba, yana mai cewa:

“Ba a komai bane ake samun kudi kai tsaye, a wasu ayyukan, kwarewa a ke samu da za ta haifar da damar da ake nema.”

Farfesa Adedimeji ya yaba wa shugaba Tinubu

Farfesa Adedimeji ya bayyana cewa gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa sun fara nuna alamun cigaba.

Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce darajar Naira na kara karuwa, yayin da tattalin arzikin kasar ya tashi daga kaso 3.0 a shekarar 2024 zuwa 4.23 a yanzu (Oktoban 2025).

Ya bayyana cewa hanyar cigaban Najeriya ta ta’allaka ne da sauya tsarin tattalin arziki, inganta ilimi da kiwon lafiya, tsaro, samar da abubuwan more rayuwa, da tabbatar da nagartaccen shugabanci.

Borno ta yi kamfani don habaka tattali

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Borno ta samar da kamfanin hada kayayyakin da ake yi da roba.

Gwamnatin ta bayyana cewa tana hada abubuwa guda biyar a kamfanin kuma ana kai kayan da aka kera wasu jihohi.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fitar da gargadi kan yada labaran yi wa Tinubu juyin mulki

Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce an samar da kamfanin ne domin habaka tattalin arzikin jihar da ya sha kalubale saboda rikicin Boko Haram.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng