Sojoji Sun Ceto Mutanen da 'Yan Bindiga Suka Azabtar, Wasu Sun Gaza Tafiya

Sojoji Sun Ceto Mutanen da 'Yan Bindiga Suka Azabtar, Wasu Sun Gaza Tafiya

  • Dakarun rundunar sojin Najeriya sun ceto mutane 21 da aka yi garkuwa da su a jihohin Kwara da Kogi bayan wani farmaki da suka kai
  • Cikin wadanda aka ceto akwai maza 14, mata 5, jariri daya da kuma ‘yan kasar Sin hudu da aka yi garkuwa da su fiye da watanni hudu
  • Kwamandan rundunar, Manjo Janar CR Nnebeife, ya ce ba za a sake barin masu garkuwa da mutane su sami mafaka a yankin ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.


Jihar Kwara – Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun samu nasarar kubutar da mutane 21 da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai.

An ce an ceto wadanda abin ya shafa ne bayan wani shiri na hadin gwiwa tsakanin runduna ta 12 a Lokoja da wasu sojoji a Ilorin.

Kara karanta wannan

Baya ta haihu: Akwai yiwuwar Tinubu ya janye afuwa ga wasu 'yan Najeriya

Sojoji da mutanen da suka ceto
Wasu daga cikin mutanen da sojoji suka ceto. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda sojojin suka ceto mutanen ne a wani sako da rundunar ta wallafa a shafinta na X.

Mutanen da aka ceto a Kwara da Kogi

Rahotanni sun tabbatar da cewa cikin wadanda aka kubutar akwai maza 14, mata 5, jariri daya da kuma ‘yan kasar Sin hudu da aka sace daga wurare daban-daban.

Wasu daga cikin mutanen da aka ceto sun bayyana cewa sun shafe fiye da watanni hudu a hannun masu garkuwa da su kafin sojojin su kai musu dauki.

Bayan an ceto su, an garzaya da su zuwa asibitin rundunar domin kula da lafiyarsu, inda aka ce wasu daga cikinsu sun kasa tafiya saboda gajiya da tsananin azabar da suka sha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji za su cigaba da kai farmaki

Kwamandan runduna ta 2 kuma kwamandan sashen Operation Fansan Yamma, Manjo Janar CR Nnebeife, ya jajanta wa wadanda aka kubutar.

Yayi magana yana mai tabbatar da cewa za su ci gaba da kai hare-hare don kawar da masu laifi daga yankin.

Kara karanta wannan

Bayan shan suka, gwamnatin Tinubu ta yi magana kan sakin Maryam Sanda da sauran masu laifi

Sojoji sun ceto mutane a Kwara
Wasu mutanen da sojoji suka ceto a Kwara. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Nnebeife ya kuma tabbatar da cewa dakarun sun yi amfani da dabarun zamani wajen gano wuraren da ake boye mutanen da aka sace kafin su kai farmaki.

An yaba wa sojojin Najeriya

Manjo Janar Nnebeife ya gode wa rundunar sojin saman Najeriya bisa taimakon da ta bayar ta hanyar sintiri da kai farmaki ta sama.

Ya kuma yaba wa sauran hukumomin tsaro bisa hadin kai wajen yaki da aikata laifuffuka a yankin, yana mai cewa wannan nasara ba za ta yiwu ba da babu su.

A cewarsa, dakarun sun nuna jajircewa da kishin kasa, kuma an umurce su da su ci gaba da gudanar da aikin har sai an dawo da cikakken zaman lafiya a jihohin Kwara, Kogi da sauransu.

An karyata kashe Kiristoci a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa hadimin shugaba Donald Trump ya ce maganar cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato

Hadimin Trump ya bayyana haka ne bayan gana wa da shugaba Bola Ahmed Tinubu a kasar Italiya ranar Juma'a.

A kwanakin baya aka fara ikirarin cewa an yi sakaci ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya, musamman a Arewa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng