'Yan Bindiga Sun Sace Matar Babban Jami'in Gwamnati, Suna Neman Miliyoyin Naira

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Babban Jami'in Gwamnati, Suna Neman Miliyoyin Naira

  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun sace Ladi Abel, matar babban jami’in hukumar shige da fice (NIS), a Legas
  • Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi mijin Ladi, CSI Abel Mada ta wayarta, sun fara da neman N7m, daga baya suka rage zuwa N3m
  • An kai rahoton lamarin ga ’yan sanda a tashar Badagry da ofishin Area kuma rundunar ’yan sandan Legas ta tabbatar da fara bincike

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - ‘Yan bindiga sun sace Ladi Abel, matar babban jami’in hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS), a kan hanyar Badagry–Mile 2 a jihar Legas.

Mai magana da yawun hukumar NIS na shiyyar Seme, Isaac Elijah ne ya tabbatar da lamarin a ranar Talata, yana mai cewa an sace matar mai shekara 45 ne a safiyar Litinin.

Kara karanta wannan

Yanayin da aka gano gawar wata budurwa, Fatima Salihu ya tada hankulan mutane a Bauchi

Hukumar NIS ta ce masu garkuwa da mutane sun sace matar daya daga cikin manyan jami'an hukumar a Legas
Hoton shugabar hukumar shige da fice, Kemi Nanna Nandap zaune a ofishinta. Hoto: @nigimmigration
Source: Twitter

An sace matar babban jami'in gwamnati

Isaac Elijah ya sanar da wannan mummunan labari ne a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa, watau NAN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, Ladi, matar babban sufuritanda (CSI) Abel Mada, ta bar gidanta da ke Sawmill, Badagry, da misalin karfe 7:00 na safe, domin zuwa kantin sayayya na TFC da ke karamar hukumar Ojo don sayen kaya, amma ba ta koma gida ba.

Elijah ya bayyana cewa wadanda suka sace Ladi, sun kira mijinta ta wayar matar don neman kudin fansa, inda suka fara da Naira miliyan bakwai, sannan daga baya suka rage zuwa Naira miliyan uku.

“Da misalin karfe 6:00 na safiyar yau (Talata), daya daga cikin ‘yan bindigan ya sake kira yana cewa idan mijin yana son matar ta rayu, to ya kawo Naira miliyan uku.”

- in ji Isaac Elijah.

An fara bincike kan sace matar jami'in NIS

Kara karanta wannan

PENGASSAN ta hukunta rassanta 2 kan rashin hana Dangote gas a yajin aiki

Ya ce an riga an kai rahoton lamarin ga ’yan sanda a ofishin Badagry da kuma sashen Area K, domin fara bincike da sa ido kan inda aka kai matar.

Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta tabbatar da cewa ta fara bincike kan sace matar jami’in NIS, domin tabbatar da an ceto ta cikin aminci.

Wani jami’in ’yan sanda da ya bayyana wa The Nation cewa bincike na ci gaba don gano dalilin sace matar da kuma sanin inda aka kai ta.

Jami'in ya ce"

“Mun samu korafi game da wata mata da ta fita daga gidanta a Badagry zuwa kasuwa amma ba ta dawo gida ba. A halin yanzu, muna bincike don tabbatar da cewa ta dawo lafiya."
Rundunar 'yan sanda ta ce ta fara bincike kan matar jami'in hukumar NIS da aka sace a Legas.
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun yana aiki a ofishinsa. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

An roki jama’a su taimaka da bayanai

Jami'in dan sandan ya ƙara da cewa ’yan sanda ba sa son bayyana cikakken bayani domin gujewa bata shirin ceto matar da kare lafiyarta.

Mai magana da yawun hukumar NIS ya bukaci jama’a da ke da bayanai game da inda matar take da su tuntubi iyalanta a lambar 0808 088 3848.

Kara karanta wannan

Bayan rage kudin Hajji, Tinubu ya ba malamin Musulunci kyautar babbar mota

Isaac Elijah ya kara da cewa duk wani taimako ko bayanin sirri zai taimaka wajen kubutar da Ladi Abel cikin koshin lafiya.

Tsohon shugaban NIS ya mutu a otal

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwar David Parradang, tsohon shugaban hukumar NIS, a wani otal.

An ce Parradang ya sauka a otal ɗin Joy House, ya biya N22,000 kudin kwana ɗaya, amma aka tsinci gawarsa a ɗakin washe gari da aka je duba shi.

‘Yan sanda sun musanta jita-jitar cewa kashe shi aka yi, inda ake yin bincike don gano matar da suka shiga dakin tare da dalilin mutuwarsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com