Tsohon Hafsan Tsaro Ya Fadi Babban Kalubalen da Ya Fuskanta a Mulkin Buhari
- Tsohon Hafsan tsaron Najeriya, Lucky Irabor ya yi magana kan kalubale da ya fuskanta a lokacin jagorancinsa a mulkin Muhammadu Buhari
- Irabor ya bayyana cewa harin jirgin kasa da aka kai na Abuja zuwa Kaduna a 2022 shi ne abu mafi wahala wanda ya rikita shi a lokacin jagorancinsa
- Irabor ya ce ya rubuta littafi mai suna 'Scars. 'bayan ritaya, inda ya tattauna tabon wahalhalun da ke cikin yaki da Boko Haram da tsaro
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Babban Hafsan Tsaro na Najeriya (CDS), Laftanar Janar Lucky Irabor mai ritaya ya bayyana irin kalubalen da ya fuskanta a lokacin jagorancinsa.
Irabor ya ce harin da aka kai wa jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a 2022 shi ne abu mafi muni da kuma kalubale da ya fuskanta a lokacin da yake rike da mukaminsa.

Source: Facebook
Da yake magana a shirin Politics Today na Channels TV a jiya Litinin 6 ga watan Oktobar 2025, Irabor ya ce lamarin ya jefa harkar tsaro cikin wani irin yanayi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abuja-Kaduna: Yadda yan ta'adda suka kai hari
A ranar 28 ga Maris, 2022, ‘yan ta’adda sun kai hari kan jirgin kasa da ke kan hanyar Abuja–Kaduna, inda suka kashe mutane da dama, suka raunata wasu, kuma suka sace mutane 61.
Daga baya an saki dukkan wadanda aka sace, wasu bayan watanni bakwai cikin wani irin yanayi da dan Adam ba zai iya kwatantawa ba.
Daga baya, a 2024, rundunar ‘yan sanda ta kama wani da ake zargi da jagorantar harin, Ibrahim Abdullahi, wanda aka fi sani da Mande, bayan dogon bincike.
Irabor dai ya yi aiki a matsayin hafsan tsaro daga Janairu 2021 zuwa Yuni 2023 a karkashin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Source: UGC
Abin da sojoji suka yi kan harin yan bindiga
Janar Irabor ya ce an tura sojoji da shirin dabaru na musamman don ceto fasinjojin da ‘yan ta’adda suka sace a wancan lokaci.
Ya ce:
“Wannan harin ya kasance gwaji na kwarewa da jarumtaka a lokacin da nake rike da mukamin hafsan tsaro.”
Janar Irabor ya kara da cewa, yaki da ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas da kare albarkatun mai suma sun kasance manyan kalubale a aikinsa.
Ya ce bayan ritayarsa, yanzu yana jin dadi da ‘yanci, inda ya bayyana cewa abubuwan da ya gani a rayuwa sun sa ya rubuta littafinsa mai suna “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum.”
Rahin tsaro: Irabor ya soki Bello Matawalle
A baya, kun ji cewa Shugaban ma'aikatan tsaro a wancan lokaci, Janar Lucky Irabor ya kalubanci maganar da gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, na ba mutanen jihar damar mallakar bindigogi.
A cewar Irabor, kiran bai kyautu ba saboda akwai jami'an tsaro da sauran hukumomin tsaro da ke kula da kalubalen tsaron da ya addabi jihar.
Sai dai, ya cigaba da bayyana yadda Antoni-janar na tarayya ke da alhakin duba kundin tsarin dokoki don ganin idan gwamna na da wannan ikon.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


