Irabor: Za mu magance tsoro, zaman lafiya zai dawo kasar nan

Irabor: Za mu magance tsoro, zaman lafiya zai dawo kasar nan

- Shugaban ma'aikatan tsaro, Lucky Irabor, ya baiwa ƴan Najeriya tabbacin ƙoƙarinsu wurin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan

- Irabor ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Litinin a wani taro na jami'an tsaro da suka yi don ɓullowa rashin tsaro

- A cewarsa, a tsaye jami'an tsaron Najeriya suke suna ayyuka tuƙuru don kawar da ta'addanci, garkuwa da mutane da sauransu

Shugaban ma'aikatan tsaro na Najeriya, Lucky Irabor, ya baiwa ƴan Najeriya tabbacin yin aiki tuƙuru don basu kariya.

Kamar yadda The Cable ta wallafa, ya yi wannan furucin ne a ranar Litinin a Abuja yayin jawabi a wani taron jami'an tsaro mai taken "Cigaban bunkasa ayyukan samar da tsaro da ta'addanci a Najeriya".

A cewarsa, jami'an tsaron Najeriya a tsaye suke, tsayin-daka domin tabbatar da zaman lafiya a kasar nan musamman ganin halin rashin tsaro, ta'addanci, garkuwa da mutane da sauran matsalolin da suka addabi kasa.

KU KARANTA: Ga su can a daji: Ortom ya bukaci Buhari yayi maganin ƴan ta'addan Binuwai

Irabor: Za mu magance tsoro, zaman lafiya zai dawo kasar nan
Irabor: Za mu magance tsoro, zaman lafiya zai dawo kasar nan. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

A ranar 5 ga watan Maris, shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa hafsosin sojin Najeriya wa'adin kawar da ta'addanci bayan naɗasu da yayi kwanakin baya duk don baiwa ƙasar nan tsaro.

"Na baku makonni ƙalilan don nan da damuna jama’a zasu fara ƙoƙarin komawa gonakinsu da ƙarfin guiwa don yin noma. Saboda kada a samu matsalar rashin abinci a kasar nan," cewar Buhari.

A jawabin hafsin sojan, "Yanzu haka mun jajirce wurin tabbatar da tsaro a gaba daya ƙasar nan daga birane har ƙauyaku da dajiki. Muna ta ƙoƙarin samar da kwanciyar hankali yadda ya dace, don haka sojoji suna buƙatar goyon bayan da ƙoƙarin al'umma.

"A maimakon duk sojojin dake ƙasar nan, maza da mata, ina mai tabbatar muku da bayar da jininmu don samar da zaman lafiya a ƙasar Najeriya.

"Zamu yi aiki da gaskiya, riƙon amana da adalci a ƙasarmu. Za a sake samun tsaro da zaman lafiya a Najeriya nan ba da jimawa ba."

KU KARANTA: Ubangiji da 'yan Najeriya ku Yafe min, Melaye yayi Nadamar Goyon Bayan Buhari a 2015

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom a ranar Asabar yayi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da jami'an tsaro da su tsamo ƴan ta'addan da suka addabi jiharsa.

Ortom yayi magana da manema labarai bayan tsallake harin da ake zargin makiyaya ne suka kai masa a garin Makurdi.

Channels Tv ta ruwaito cewa, ya je kai ziyara wata gona yayin da maharan suka far masa amma jami'an tsaro dake tare da shi sun yi nasarar fatattakarsu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel