Malaman Musulunci da Aka Yi Zargin Sun Taba Kimar Annabi Muhammad SAW a Najeriya
A Najeriya, an sha zargin wasu malamai da kalamai da ake ganin ba su dace a jingina su da fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW ba.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - An zargi manyan malaman Musulunci da dama daga Arewacin Najeriya masu akidu daban-daban wanda ya jawo maganganu.
Na baya bayan nan shi ne Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph wanda a yanzu haka haka ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan lamarin.

Source: Facebook
Wasu malamai da aka zarga da taba Annabi
Dalilin haka, gwamantin jihar Kano ta kafa kwamitin Shura domin kaddamar da bincike da kuma daukar matakin da ya dace, kamar yadda Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta yi duba kan wasu malaman Musulunci daga Arewacin Najeriya da aka taba zargi kan lamarin.
1. Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
Shekaru hudu da suka wuce Malam Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi wasu kalamai da suka tayar da kura a tsakanin Musulmai.
Ana zargin ya danganta wasu halaye marasa kyau ga Annabi SAW da har ya jawo aka kai korafi ga gwamnati domin daukar mataki.
Daga bisani, an yi zama da shi domin sanin dalilansa game da lamarin wanda Abduljabbar ya nuna bai yi haka domin taba Annabi ba, ya yi ne saboda kore kazantar da aka danganta shi da su.
Bayan haka, kotu ta yanke hakuncin kisa ta hanyar rataya, inda Alkalin kotu ya kuma ba da umarnin gaggawa na kwace dukkanin littafan malamin.

Source: UGC
2. Marigayi Idris Abdulazizi Dutsen Tanshi
Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya sha fama da hukumomi bayan zargin kalamai marasa dadi ga Annabi SAW.
Malamin kafin rasuwarsa, ya sha kare kalamansa na cewa 'bai neman taimakon kowa sai Allah' wanda wasu ke ganin ya munana ladabi ga Manzon Allah SAW.
Kotun Majistare a Bauchi ta ba da umarnin tsare malamin, Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi a wancan lokaci a gidan yari, cewar BBC Hausa.
Rundunar 'yan sandan jihar ce ta gurfanar da malamin a gaban kotu bayan ta gayyace shi game da wani ƙorafi da aka shigar gabanta.'

Source: Facebook
3. Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib 'Triumph'
A kwanan nan, an ta da jijiyoyin wuya kan kalaman Sheikh Lawan Triumph wanda ake ganin an munana ladabi ga Annabi SAW.
Bayan haka, gwamnatin Kano ta kafa kwamitin Shura domin tabbatar da gudanar da bincike da daukar matakin da ya dace.
Kwamitin ya dakatar da malamin daga tsokaci kan lamarin domin tabbatar da zaman lafiya da kuma samun damar kammala bincike.
A halin yanzu, ana ta kira ga gwamnatin ta dauki mataki kan malamin yayin da wasu ke neman gwamnatin ta yi adalci ba tare da son zuciya ba.

Source: Twitter
4. Sheikh Imam Mansur Kaduna
Malaman Ahlus Sunnah sun taso Malam Mansur Kaduna kan kwatanta Annabi SAW da hankaka wanda ake ganin rashin mutunta fiyayyen halitta ne.

Kara karanta wannan
"Tinubu ya yi abin da muke ta kira," Sarki Sanusi II ya hango goben tattalin arziki
An yada wani bidiyo wanda aka gano Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah na yi wa malamin raddi wanda Dahiru Garba Turawa ya wallafa a Facebook.
Abin da Mansur Kaduna ya ce:
"Manzon Allah shi ne 'Eagle', Sarkin tsuntsaye, shugaban tsuntsaye, Muhammadur rasulullah, shi ne 'hankaka'
Sheikh Sani Rijiyar Lemu ya yi suka ga wasu kalamai da ake zargin malamin ne ya yi, ya rika kamanta siffofin Annabi SAW da kasa, duwatsu da sauransu.
5. Sheikh Nazifi Al-Karmawy Kano
Har ila yau, mutane da dama sun bayyana rashin jin dadi bayan kalaman Sheikh Nazifi Al-Karmawy wanda ya kwatanta Annabi SAW da 'rakumi'.
Alaramma Ismail Maidguri ya wallafa bidiyon malamin a Facebook inda yake maganar idan ka yi mafarki ka ga rakumi to Manzon Allah SAW ka gani.
A bidiyon, malamin ya ce:
"Idan ka ga shehinka wanda ka rike, ka yi mafarki to ba shi ba ne Manzon Allah ne, ko kuma ka yi mafarki ka ga wani katon rakumi to Annabi ne."
Wasu mutane da dama sun yi ta kiran a gayyaci malamin domin daukar matakin da ya dace kamar yadda ake zargin Malam Lawan Triumph.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun tare babbar hanya a Zamfara, sun sace shugaban majalisar Malamai

Source: Facebook
Batanci: Bala Lau ya yabawa rawar hukumar DSS
Mun ba ku labarin cewa Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Bala Lau, ya yi magana kan abin da ke faruwa game da Sheikh Shu'aibu Lawan Triumph.
Bala Lau ya yaba da rawar da shugaban DSS, Mr. Oluwatosin Ajayi, ya taka wajen sasanta rikicin Kano cikin ruwan sanyi.
Malamin ya bayyana haka a Ibadan, inda ya ja hankalin mabiya su ci gaba da tallafa wa zaman lafiya da haɗin kan Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

