Kai tsaye: Yadda mukabala ke gudana tsakanin Malaman Kano da Sheikh AbdulJabbar Kabara

Kai tsaye: Yadda mukabala ke gudana tsakanin Malaman Kano da Sheikh AbdulJabbar Kabara

Bayan kai komo da aka yi kan batun mukabalar Sheikh Abduljabbar, an sanya ranar da za a caccaka tsinke tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano

Zasu zauna zaman mukabala a yau ranar Asabar, 10 ga watan Yuli.

An tashi: An kammala mukabala tsakanin Malaman Kano da Malam AbdulJabbar Kabara

Bayan kimanin awanni biyar ana tattaunawa kan maganganun da ake zargin Malam AbdulJabbar Kabara da yi, na kawo karshen zaman.

An bukaci Malam AbdulJabar ya tuba ya nemi gafara, yace sam ba zai yi ba

Malam Abubakar Madatai ya yi kira ga Malam Abduljabbar ya tuba kuma ya nemi gafarar al'ummar Musulmi su yafe masa bisa taba mutuncin Annabi (SAW) da yayi.

Malam Abduljabbar a martaninsa ya ce ba zai tuba a wajen wannan muƙabala ba saboda ba'a bi hanyar da zai tuba ba, rahoton BBC.

“Amma yanzu mutum ba zai tuba ba bayan yana kan gaskiya,” in ji Abduljabbar

Ya ce sai an kawo masa hujjojin da suka fi nasa.

A shirya mana sabuwar mukabala, AbdulJabbar ya bukaci gwamnati

Malam Abduljabbar ya yi kira ga gwamnati ta sake samar da wani lokaci daban domin sake wata mukabalar.

BBC ta ruwaitoshi da cewa yana buƙatar lokacin da zai fito da “matsalar yadda take”

Sannan ya roki idan za a sake yi a nuna muƙabalar kai tsaye duniya na gani

Da litattafai har 500 na zo mukabalar nan

Malam AbdulJabbar yace minti goma da aka basa sun yi masa kadan saboda ya zo da littafai da yawa

Ya ce ba a sanar da shi tsarin da aka yi na cewar miniti 10 aka ba bayar ba:

Yace:

“Da na sani ba zan zo da lattafai har 500 ba,” in ji shi.

Na yadda nayi laifi, a yi min hukunci: Malam AbdulJabbar

Bayan karban korafin AbdulJabbar kan tambayoyin da ake masa, an saurari jawabin da malaman Kano suka gabatarwa gwamnatin Kano kan kalaman Abduljabbar Nasir Kabara wanda ya sabbaba dakatar da shi.

A cikin tuhumar da suka gabatar akwai inda Malam Abduljabbar ke cewa annabi yana da kawaliya

Sannan da inda yake cewa wasu haddisai da ya ƙaryata sun ce annabi ya biya wa wata mata bukata ta saduwa

Malam AbdulJabbar ya amsa cewar ya yi laifi a yi masa hukunci.

Majiyar BBC Hausa.

Alkalin mukabala ya karbi korafin Malam AbdulJabbar na kin amsa tambayoyi

Bayan korafin da Malam AbdulJabbar yayi na cewa ayi masa tambaya ne kan korafin da Malaman Kano suka yiwa gwamnati kansa, Alkalan zaman sun amince.

Daga yanzu mukabalar za ta koma kan tuhumar da Malamai suka yiwa Abduljabbar wajen gwamnati.

Malam Kabir Bashir AbdulHamid ya gabatar da tambaya ga Malam AbdulJabbar

Malam Kabir Bashir AbdulHamid ya yace a kunna masa karatun Malam Abduljabbar inda yace cikin Sahihul Bukhari akwai wata mata da ta je wajen Manzon Allah tana yi masa kwarkwasa kuma ya biya mata bukata a boye.

Sai dai.Mallam Abduljabbar ya ƙi badaamsa inda ya ce ba a yi masa adalci ba, saboda shi ba a ba shi damar da zai kunna murya ba kamar yadda abokan mukabalar sa suke yi.

Ya ce ba zai sake amsa wata tambaya kan wata murya da aka kunna ba sai dai waɗanda aka kai wa gwamna da Sarki da har ta kai ga kotu ta rufe masa masallacinsa aka hana shi wa'azi.

Rahoton BBC Hausa

An fara mukabalar

A cewar BBC Hausa, Sheikh Rabiu Rijiyar Lemo ne ya fara yi wa Abduljabbar tambaya kan auren Annabi SAW da Safiyatu da kuma batun yin fyade da tsirara.

Malam Rabiu ya nemi Abduljabbar ya kawo masa hadisin a Sahihul Bukhari.

AbdulJabbar ya bada amsa da cewa Anas ɗan malik shi ya kore hadisin "kore wa ma’aiki kalaman da ake masa batanci yake yi"

Sai dai an Malam Rabi’u Rijayar lemo ya ce bai bayar da amsar dai dai ba, inda ya ce hadisin ya bambanta da abin da ya faɗa.

Farfesa Salisu Shehu ne Alkalin mukabalan

Shugaban jami'ar Al-Istiqama Sumaila, Farfesa Salisu Shehu, ne Alkalin mukabala

Kai tsaye: Yadda mukabala ke gudana tsakanin Malaman Kano da Sheikh AbdulJabbar Kabara
Kai tsaye: Yadda mukabala ke gudana tsakanin Malaman Kano da Sheikh AbdulJabbar Kabara
Asali: Facebook

Malamai sun shirya tsaf don fara mukabala

Sheikh AbdulJabbar Kabara da tawagarsa sun dira wurin mukabalar.

Hakazalika sauran Malamai sun Isa wurin da aka shirya mukabala a yau Asabar.

Daga ciki akwai Ustaz Kabir Bashir Abdulhamid, Dr Muhammad Rabiu Rijiyan Lemo, Malam Lawal Triumph, dss.

Online view pixel