Mamman Shata da Wasu Fitattun Mawaƙan Hausa 4 da Aka Karrama da Digirin Girmamawa

Mamman Shata da Wasu Fitattun Mawaƙan Hausa 4 da Aka Karrama da Digirin Girmamawa

A 'yan kwanakin baya ne shafukan sada zumunta suka cika da ce-ce-ku-ce bayan an ruwaito cewa Jami'ar European-American ta karrama Dauda Kahutu Rarara da samu digirin girmamawa.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

An rahoto cewa an gudanar da bikin karramawar a Abuja, inda 'jami’ar' ta ba mawaki Rarara digirin girmamawar a gaban manyan baki masu yawa, ciki har da gwamnan Katsina.

Fitattun mawakan Hausa biyar ciki har da Mamman Shata ne aka taba karramawa da digirin girmamawa
Hoton Dr. Mamman Shata, Dr. Aminu Ladan Abubakar da Dr. Ɗan Maraya Jos. Hoto: Uzairu M Abubakar
Source: Facebook

Takaddamar digirin karramawar Dauda Rarara

Sai dai jim kadan bayan bikin, wata sanarwa da ake dangantawa da jami’ar ta European-American ta bayyana cewa babu wani digiri da ta taɓa bai wa Rarara, inji rahoton BBC Hausa.

Wannan sanarwa ta tayar da ƙura sosai a kafafen sada zumunta, inda jama’a suka rabu gida biyu — wasu na kare Rarara, wasu kuma na tuhumarsa da neman daukaka ta hanyar da ba ta dace ba.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun tilasta rufe makarantu 180 a Arewa

Wasu daga cikin magoya bayan mawakin sun ce Rarara ya cancanci digirin saboda irin rawar da ya taka wajen amfani da waƙa a siyasa da ilimantar da jama’a.

Sun jaddada cewa mawaki Rarara ya taimaka wajen bunkasar waƙoƙin Hausa na zamani, musamman ta hanyar amfani da salo wayar kan ga jama’a.

Sai dai wasu sun ce Rarara bai kai matsayin irin wannan yabo ba tukuna, suna masu jaddada cewa jami’o’i kan ba mutanen da suka shahara da tasiri a fannoni na kimiyya, adabi ko aikin al’umma, ba kawai saboda farin jini a kafafen sada zumunta ba.

Mawaƙan Hausa da suka samu digirin girmamawa

A tarihi, mawaƙan Hausa da dama sun taɓa samun irin wannan karramawa daga jami’o’in cikin gida da waje saboda gudunmawarsu wajen bunkasa adabin baka da ci gaban al’umma.

1. Mamman Shata — Jami’ar ABU, Zaria

Jami'ar ABU Zariya ta karrama Mamman Shata da digirin girmamawa a 1991.
Hoton fitaccen mawakin Hausa, marigayi Dr. Mamman Shata Katsina. Hoto: Haruna Uba / Facebook
Source: Facebook

A shekarar 1991, Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta ba Alhaji Mamman Shata digirin girmamawa saboda gudunmawar da ya bayar wajen raya adabin Hausa da waƙar baka.

An haifi Mamman Shata a garin Musawa, jihar Katsina, a 1923, ya kuma rasu a shekarar 1998, yana da shekara fiye da 70 a lokacin da ya bar duniya, cewar bayanin da aka wallafa a Wikipedia.

Kara karanta wannan

'Yan siyasan da ADC za ta bukaci su yi murabus, su shigo cikin jam'iyya gaba daya

Waƙoƙinsa irin su Bakandamiya, Kudi A Kashe Su Ta Hanya Mai Kyau da Na Tsaya Ga Annabi Muhammadu da wasu fiye da 10, 000 sun zama ginshiƙai na tarihi, har ma ana nazarin su a jami’o’in Najeriya da ma wasu ƙasashen Turai.

2. Ɗan Maraya Jos — Jami’ar Jos

Jami'ar Jos ce ta karrama mawaki Dan Marayan Jos da digirin girmamawa.
Fitaccen mawakin Hausa, marigayi Adamu Muhammadu Wayya (Dan Maraya Jos). Hoto: Abbas Maiyama
Source: Facebook

Adamu Muhammadu Wayya (Ɗan Maraya Jos) ya shahara da waƙoƙinsa masu ɗauke da nasiha da nishaɗi.

Waƙoƙinsa kamar Karen Mota, Auren Dole, da Mai Akwai da Babu sun karɓu sosai saboda saƙon da ke kunshe a cikin su.

Jami’ar Jos ta karrama shi da digirin girmamawa saboda irin tasirinsa wajen amfani da waƙa don faɗakarwa da kuma jawo haɗin kan jama'a, cewar rahoton Daily Trust.

An haifi Adamu Dan Maraya a shekarar 1946 a garin Bukur da ke cikin jihar Plateau kuma ya rasu a ranar Asabar 20 ga watan Yunin shekara ta 2015.

3. Akilu Aliyu — Jami’ar BUK, Kano

Jami'ar BUK ce ta karrama mawaki Akilu Aliyu da digirin girmamawa saboda raya adabi
Fitaccen mawakin Hausa, marigayi Alhaji Akilu Aliyu. Hoto: Taskar Labarai
Source: Facebook

Alhaji Akilu Aliyu fitaccen marubuci ne kuma mawaƙin Hausa daga garin Jega, jihar Kebbi, kamar yadda rahoton WikiTree ya nuna.

Waƙoƙinsa sun shafi zamantakewa, aure, da halayyar Bahaushe. A cikinsu akwai waƙar Najeriya, Matan Aure, da Bahaushe Mai Ban Haushi.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun yi ta'addanci a Borno, an kona fadar basarake, an kashe mutane

Saboda irin wannan gudunmawa, Jami’ar Bayero (BUK) da ke jihar Kano ta karrama shi da digirin girmamawa.

Har ila yau, Akilu Aliyu ya kasance malami kuma marubucin littattafai da dama da suka shafi harshen Hausa, ciki har da Fasaha Alkaliya.

4. Aminu Ladan Abubakar — Jami’ar HEGT, Benin

Jami'ar HEGT da ke Jamhuriyyar Benin ce ta karrama Aminu Ladan Abubakar da digirin girmamawa
Fitaccen mawaki, Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Alan Waka) rike da shaidar digirin girmamawa. Hoto: Aminu Ladan Abubakar
Source: Facebook

Aminu Ladan Abubakar, wanda aka fi sani da Alan Waƙa, na daga cikin mawaƙan zamani masu amfani da waƙa wajen isar da saƙon addini, zamantakewa, da siyasa.

An haife shi a Kano a 1973, kuma ya wallafa littattafai da dama, kamar Jirgi Ɗaya Ke Dauke da Ni da Ceto Ko Cuta?

A shekarar 2020, Jami’ar HEGT ta Jamhuriyar Benin ta ba shi digirin girmamawa saboda irin rawar da yake takawa wajen sabunta adabin baka da fasaha ta zamani, cewar rahoton Blue Print.

5. Nura M. Inuwa — Jami’ar Jagora, Faransa

Jami'ar Jagora da ke Faransa ce ta ba Nura M Inuwa digirin girmamawa.
Fitaccen mawawaki, Nura M Inuwa yana karbar shaidar digirin girmamawa daga jami'ar Jagora. Hoto: Dr. Nura M Inuwa
Source: Facebook

Nura Musa Inuwa na daga cikin matasan mawaƙan Hausa masu farin jini a wannan ƙarni, kuma tauraruwarsa ta haska sosai.

Waƙoƙinsa irin su Aisha Humaira, Garkami, da Badi Ba Rai da sauransu sun shahara sosai a sassa daban-daban na Najeriya da maƙwabta.

Kara karanta wannan

An shigar da 'yan sanda kotu, za a fara shari'a kan takaita hawa babur a Gombe

A shekarar 2023, ya sami digirin girmamawa daga Jami’ar Jagora ta Faransa kamar yadda ya wallafa bidiyon karramarwar a shafinsa na Facebook.

Tasirin karrama mawaka da digirin girmamawa

Masanin waƙoƙin Hausa, Malam Ibrahim Sheme, ya bayyana cewa irin wannan karramawa na ƙara daraja da martaba ga mawaki a idon jama’a da hukumomi.

A cewarsa:

“Digirin girmamawa ba wai kawai takarda ba ce, hujja ce ta cewa an amince da gudunmawar mutum ga al’umma. Lokacin da jami’a ta ba mawaki lambar yabo, tana nufin tana kallon aikinsa a matsayin wani bangare na ilimi da ci gaba.”

Sheme ya ce lokacin da aka ba Shata digirin girmamawa, abokan hamayyarsa irin su Ɗankwairo da Ahmadu Doka sun yi sulhu da shi saboda ganin gwamnati da jami’a sun tabbatar da matsayinsa.

Haka kuma, irin wannan yabo yana ƙara ƙarfin gwiwa ga mawaki ya ɗauki sana’arsa da muhimmanci.

“Da zarar mawaki ya sami karramawa daga jami’a, sai ya fahimci cewa abin da yake yi na da daraja, yana ƙoƙarin yin abin da ya fi inganci, domin ya san ana kallonsa a matsayin jagora a fagen fasaha.”

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Dakarun sojoji sun cafke masu hada baki da 'yan ta'adda a Katsina

- Malam Ibrahim Sheme.

Digirin girmamawa: Za a share hawayen Rarara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sadaukin Bauchi, Abdurahman Sade, ya bayyana shahararren mawaki, Dauda Kahutu Rarara, a matsayin gwarzo.

Abdurahman Sade ya bayyana cewa mawaki Rarara a matsayin wanda ya cancanci digirin girmamawa daga kowace jami’a a duniya.

Basaraken wanda ya ce shi ne ya jawo hankalin jami’ar da aka ce ta ba Rarara digiri a baya, ya yi alkawarin ci gaba da kokari har sai mawakin ya samu sahihiyar karramawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com