UNGA80: Abubuwa 7 Masu Muhimmanci da Shettima Ya Gabatar a Taron Majalisar Dinkin Duniya
Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Babban Taron Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 a Amurka.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kashim Shettima ya gabatar da jawabin Najeriya a madadin Shugaba Bola Tinubu a taron wanda aka yi wa taken UNGA80 a takaice.

Source: Twitter
Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha ya wallafa cikakken jawabin da Shettima ya yi a shafinsa na X ranar Alhamis da ta gabata.
Abubuwan da Shettima ya gabatar a UNGA80
Jawabin Najeriya dai ya maida hankali kan batutuwa da dama ciki har da batun 'yancin Falastinawa, tsarin kudi, hakar ma'adanai da sauransu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku muhimman abubuwan da Najeriya ta gabatar a taron UNGA80 a birnin New York na kasar Amurka.

Kara karanta wannan
Gwamna ya lallaba ya gana da Tinubu, za a saki jagoran 'yan ta'adda da Buhari ya kama a 2021
1. Samar da kasar Falasdinu
Daya daga cikin abubuwan da suka ja hankalin 'yan Najeriya a jawabin da Shettima ya yi a taron UNGA80, shi ne batun rikicin Isra'ila da Falasdinawa.
Shettima ya fadawa shugabannin duniya cewa Najeriya na goyon bayan mafitar kasashe biyu, ma'ana a bai wa Falasdinawa 'yanci ta hanyar kafa kasar Falasdinu.
Ya ce bai kamata a ci gaba da tauye ’yancin Falasdinawa ba, domin su ma su na da hakkin rayuwa cikin ’yanci da mutunci kamar kowa.
“Muna faɗa ba tare da boye-boye ko shakka ba cewa samar da ƙasashe biyu ita ce mafitar da za ta kawo zaman lafiya mai ɗorewa ga al’ummar Falasɗinu.”
"Mutanen nan su na da daraja da kima kamar kowa, kuma sun cancanci yanci da mutuntawa kamar yadda ake bai wa kowace al'umma a duniya.
- Kashim Shettima.
Wannan ya nuna cewa Najeriya na goyon bayan matsayar Birtaniya, Faransa, Kanada, Australia, Portugal da wasu ƙasashe wajen neman a amince da Ƙasar Falasɗinu.

Kara karanta wannan
Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi
2. Neman kujera a kwamitin tsaro
A taron, Najeriya ta sake nanata bukatar a ba ta kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, tana mai kokawa kan rashin wakilci daga Afirka.
A cewar wakilin Najeriya, rashin wakilcin Afirka a matakin yanke shawara na duniya babban gibi ne da ya kamata a cike domin tabbatar da adalci.
Shettima ya ce rawar da Najeriya ke takawa wajen samar da zaman lafiya ya cancanci a ba ta gurbi na dindindin a kwamitin tsaro, The Cable ta rahoto
3. Yin adalci a harkokin hakar ma'adanai
Najeriya ta soki tsarin fitar da ma'adai daga kasashen Afirka ba tare da kawo abubuwan ci gaba da za su amfani al'umma ba.
A jawabin da ya gabatar a taron, Kashim Shettima ya fito fili ya nuna damuwarsa kan yadda ake fitar da ma’adanan Afirka ba tare da ci gaban al’ummomin da suka mallake su ba.
Mataimakin Shugaban Najeriya ya nemi a samar da masana’antu da ayyukan yi a wuraren da ake hakar ma’adinai a nahiyar Afirka domin al’umma su amfana kai tsaye.

Source: Twitter
4. Inganta fasaha a nahiyar Afirka
Najeriya ta tabo batun fasahar zamani a taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ta nuna damuwa kan yadda sauran yankuna suka yi wa Afirka fintinkau a fannin fasaha.
Shettima ya gabatar da shirin haɗin gwiwar duniya don rage tazarar fasaha da ke tsakanin Afirka da sauran yankuna.
Ya jaddada buƙatar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci, masana, da kamfanonin fasaha masu zaman kansu na duniya domin inganta harkokin fasahar zamani a Afirka.
5. Gyara tsarin kuɗi na Duniya
Najeriya ta buƙaci a sake fasalin tsarin kuɗi na duniya, musamman tsarin bashi da jarin waje, saboda yadda suke jefa ƙasashe masu tasowa cikin mawuyacin hali.
Walikin Najeriya a taron kuma mataimakin Shugaban Kasa ya caccaki tsarin karbo bashi da zuba hannun jari, yana mai cewa yana tauye kasashe masu tasowa musamman a Afirka.
Don haka ya roki a sake fasalin tsarin domin samar da hanya mai sauki da za ta yi daidai da halin da kasashe kamar Najeriya ke ciki, cewar rahoton Bussines Day.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta yi martani kan zargin jefa 'yan Najeriya miliyan 15 a bakin cikin talauci
6. Bukatar kafa kotun kudi ta duniya
Wani abu da Najeriya ta ba Majalisar Dinkin Duniya shawarar a kirkiro shi ne Kotun Kudi, wacce za ta rika warware rikice-rikicen kudi tsakanin kasashe.
Kashim Shettima ya ce kafa kotun kuɗi ta duniya domin magance batutuwan da suka shafi kuɗi tsakanin ƙasashe, zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya da bin doka a harkokin tattalin arziki.
7. Kawo karshen yada labaran karya
Mataimakin Shugaban ya gargadi duniya kan haɗarin da ke tattare da kirkira da yada labaran ƙarya, musamman a ƙasashen da tsarin dimokuraɗiyya ke da rauni.
Najeriya na daya daga cikin kasashen da yada labaran karya ke karuwa musamman a kafafen sada zumunta na zamani.
A cewar Aminiya, hakan ya sa Shettima ya gabatar da batun a zauren Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bukaci a kirkiro sababbin tsare-tsaren da za su tabbatar da sahihanci fa gaskiyar kowane irin bayani

Source: Twitter
Shettima ya kwantar hankalin 'yan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu na aiki tukuru domin ceto tattalin arzikin Najeriya.
Sanata Shettima ya bai wa yan Najeriya cewa gwamnati mai ci zata yi iya bakin kokarinta wajen samar da tsaro da kawo karshen cin hanci rashawa.
Ya ce shugabannin da aka zaba a Najeriya suna da babban nauyi na tallata dimukuradiyya ta hanyar ingantaccen shugabanci da tabbatar da tsaron kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

