'Yan Bindiga Sun Sace Sanannen 'Dan Siyasa da Wasu Mutum 2 a Jihar Kaduna
- Yan bindiga sun shiga kauyuka biyu a kananan hukumomin Makarfi da Kudan da ke cikin jihar Kaduna jiya Alhamis
- Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan sun sace mutane uku a hare-haren da suka kai lokaci guda, ciki har da sanannen dan siyasa
- Har yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Kaduna ko rundunar 'yan sanda kan wannan lamarin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai hari kan jama'a a yankunan kananan hukumomin Kudan da Makarfi da ke cikin jihar Kaduna.
A hare-haren biyu da ake ganin kamar shiri ne da aka tsara, 'yan bindigar sun yi awon gaba da mutane uku, ciki har da wani sanannen dan siyasa a yankin.

Source: Original
Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ne ya tabbatar faruwar hare-haren biyu a shafinsa na X yau Juma'a, 12 ga watan Satumba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce 'yan ta'addan sun aikata wannan babban laifi ne a jiya Alhamis, 11 ga watan Satumba, 2025, yana mai cewa maharan sun kuma sace shanun jama'a.
Yan bindiga sun kai hari yankin Kudan
Rahotanni daga yankin sun nuna cewa harin farko ya auku ne a kauyen Taban Sani da ke karamar hukumar Kudan, mahaifar tsohon dan takarar gwamnan PDP, Isah Muhammad Ashiru.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun afka wa kauyen ne da dare, ba tare da tsammani ba, inda suka bude wuta a iska don tsorata jama'a.
A yayin harin, ’yan bindigar sun yi nasarar yin garkuwa da mutane biyu daga cikin mazauna kauyen tare da yin awon gaba da shanu masu yawa.
An yi garkuwa da sanannen dan siyasa
A lokaci guda kuma, a karamar hukumar Makarfi da ke makwabtaka da Kudan, wasu yan bindigar sun kai hari a kauyen Gazara.
A wannan harin, 'yan bindigar sun sace wani sanannen ɗan siyasa na yankin mai suna Zaharadeen Magaji.

Kara karanta wannan
Katsina: Yan bindiga sun afka wa masallata, sun sace musulmai a sallar isha, an rasa rai
Shaidu sun bayyana cewa a yayin hare-haren biyu, ’yan bindigar sun rika harbi a sama don tsoratar da jama’a da kuma hana yunkurin kawo wa wadanda suka sace agaji.

Source: Twitter
Wane mataki hukumomi suka dauka?
Har zuwa lokacin da muka hada wannan rahoton, gwamnatin jihar Kaduna ko hukumar 'yan sanda ba su fitar da wata sanarwa ba kan lamarin.
Sai dai shugabannin al’umma sun roƙi gwamnatin jiha da ta tarayya da su ƙara tsaurara sintirin tsaro a yankunan karkara masu domin hana sake faruwar irin wannan mummunan lamari.
'Yan ta'adda sun kashe mutum 8 a Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa 'yan bindigan sun kai hare-hare daban-daban a kananan hukumomin Kauru da Kudan na jihar Kaduna.
Mutane takwas sun rasa rayukansu, yayin da wasu takwas kuma suka samu raunuka sakamakon hare-haren da 'yan bindiga suka kai kan bayin Allah.
Mazauna yankin da abin ya faru sun roki hukumomin tsaro da su zurfafa bincike domin kamo masu hannu a harin tare da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin jama'a, musamman na karkara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
