Matashi Ya Yi Tafiyar Kilomita 600 don Ya Gana da Gwamna, Ya Samu Kyautar N10m
- Wani matashi ya yi tafiyar kafa ta tsawon kwanaki 17 daga Ikorodu zuwa Abakaliki domin ya gana da Gwamna Francis Nwifuru
- Matashin ya ce ya yi tattaki na kimanin kilomita 600 ba tare da fargabar haduwa da masu garkuwa ba, don yi wa gwamna godiya
- An ce matashin ya samu kyaututtuka daga masoya, ciki har da mota, fili, kuɗi, da kuma tallafin Naira miliyan 10 daga gwamna Nwifuru
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ebonyi - Kwamared Jeremiah Obaji, wani dan asalin Ebonyi da ke zaune a Ikorodu, jihar Legas, ya bayyana yadda ya yi tattaki na tsawon kwanaki 17.
Matashin ya yi tafiyar kilomita 600 daga Ikorodu zuwa Abakaliki domin nuna godiya ga Gwamna Francis Nwifuru bisa samar da zaman lafiya a garinsu.

Source: Facebook
Matashi ya yi tafiyar kilomita 600
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa Kwamared Jeremiah Obaji, dan asalin garin Effium ne da ke karamar hukumar Ohaukwu, jihar Ebonyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce Kwamared Obaji ya bar Ikorodu a ranar 21 ga watan Agusta, 2025, ya kuma isa Abakaliki a ranar 7 ga Satumba, bayan ya yi tafiyar sama da kilomita 600 a kafa.
A cewar matashin, ya sha fama da yunwa, gajiya, da cizon kwari a kan hanyarsa. Haka kuma ya ce ya jefar da wandonsa na gayu saboda yana fargabar sace shi a hanya.
“Ban san cewa ina sukar mai cetona ba. Na taba yi masa kaca kaca a shafukan sada zumunta, amma shi ne ya kawo zaman lafiya a garinmu. Wannan tattaki tukuici ne ta godiya. Lallai zaman lafiya abu ne mai daraja."
- Kwamared Jeremiah Obaji.
Gwamna ya kawo karshen rikicin Effium
Ya bayyana yadda rikicin Effium ya raba shi da iyalansa da sauran jama’a, abin da ya jefa su cikin mawuyacin hali.
Sai dai, ya ce da zuwan Gwamna Nwifuru, ya kawo ƙarshen zubar da jini na shekaru da dama ta hanyar kafa garuruwa biyar masu cin gashin kansu.

Kara karanta wannan
Romon siyasa: Kansila ya naɗa sababbin hadimai 18, ya raba masu wurin aiki a Kaduna
Ya kara da cewa wannan tattakin ya ba shi damar haduwa da tsofaffin abokai da kuma haduwa da matasan Ebonyi da rikici ya tilasta su yin sana’o’in masu hatsari maimakon yin karatu.

Source: Twitter
Gwamna ya gana da matashi mai tattaki
Da labarin tafiyar tasa ta bazu a shafukan sada zumunta, masoya da magoya baya sun yi masa alkawarin kyaututtuka, ciki har da mota, fili, da kuɗaɗe.
A yayin tarbar sa, Gwamna Francis Nwifuru ya yaba da wannan tukuici, yana mai cewa wannan shaida ce ta nasarar manufar gwamnatinsa ta People’s Charter of Needs.
Tribune ta rahoto gwamnan ya kuma ba Obaji tallafin kuɗi har Naira miliyan 10 domin taimaka masa ya murmure da kuma ci gaba da yada aikin zaman lafiya a jihar.
Sai dai matashin ya fadawa gwamna cewa burinsa yanzu shi ne kafa gidauniyar zaman lafiya da kuma taimakawa yaran da rikice-rikice suka raba da gidajensu.
Matasa sun yi tafiyar kilomita 205 don 'dan siyasa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu matasa biyu masu jini a jika, sun yi tafiyar kilomita 205 domin ganawa da dan takarar gwamnan Bauchi a 2023.
Matasan, Abu Samaila da Abubakar Yusuf, sun yi tattakin ne daga karamar hukumar Katagum zuwa cikin kwaryar Bauchi, don gana wa da Air Marshal Abubakar Saddique mai ritaya.
Shugaban kungiyar yakin neman zaben Saddique na APC ya tarbi matasan biyu tana mai cewa abin da suka yi abin yaba wa ne kuma ya gode musu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

