Gwamna Uba Sani Ya Taso da Batun Kisan da Aka Yi Wa 'Yan Daurin Aure a Plateau
- Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sha alwashi kan kisan da aka yi wa masu zuwa daurin aure a Plateau
- Uba Sani ya bayyana cewa ya cika alkawarin da ya dauka ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a lamarin
- Gwamnan ya tunatar da cewa nauyin kare rayuka da dukiyoyin jama'a wani abu ne da Allah ya dora a kansa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya sake taso da batun mutanen da aka kashe wajen zuwa daurin aure a Plateau.
Gwamna Uba Sani ya yi alkawarin tabbatar da adalci ga mutanen da suka rasa rayukansu a kisan gillan da aka yi a watan Yuni, a karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa Gwamna Uba Sani ya yi alkawarin ne a ranar Talata, 9 ga watan Satumban 2025.
Uba Sani a kan kisan 'yan daurin aure?
Gwamna Uba Sani ya yi alkawarin ne yayin kaddamar da aikin titi mai tsawon kilomita shida da zai haɗa kwanar Hunkuyi zuwa Basawa a kananan hukumomin Kudan da Sabon Gari.
Uba Sani ya bayyana cewa kare rayuka da dukiyoyi nauyi ne da Allah ya dora masa, tare da jaddada cewa ba zai huta ba sai an tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa.
A kwanakin baya ne dai aka kashe matafiya 13 daga jihar Kaduna a harin da aka kai a Mangu, ciki har da mutane 11 daga Unguwan Dantsoho.
An kashe mutanen ne a lokacin da suke kan hanyar zuwa wani daurin aure a karamar hukumar Qua’an Pan ta jihar Plateau.
Gwamna Uba Sani ya cika alkawari
Jaridar TheCable ta ce Gwamna Uba Sani ya tunatar da alkawarin da ya yi tun farko na tallafawa iyalan waɗanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan
Bayan tsawon lokaci, gwamna ya tabbatar da fara tattaunawar sulhu da 'yan bindiga
Ya bayyana cewa ya riga ya cika alkawarin bayar da tallafin kuɗi da kuma samar da gidaje.
"Allah ya dora alhakin kare rayuka da dukiyoyin jama'a a kaina, kuma ba zan yi kasa a gwiwa ba har sai na sauke wannan nauyin."
- Gwamna Uba Sani

Source: Twitter
Gwamna Uba Sani ya ce aikin gina sabon titin ya samo asali ne daga koke-koken da al’ummar yankin suka gabatar masa a lokacin ziyarar ta’aziyya da ya kawo.
Ya kara da cewa Kudan na daga cikin kananan hukumomi 12 a jihar da ba su amfana da samun hanya ba fiye da shekara 10.
Ya soki tsofaffin ‘yan siyasar yankin da suka gaza kawo ci gaban da ya dace.
Gwamnan ya yabawa al’ummar yankin bisa kiyaye zaman lafiya tare da kiransu da su ci gaba da hakan, yana mai jaddada cewa ci gaba mai ma’ana ba zai tabbata ba sai an samu yanayi na kwanciyar hankali.
Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya yi shagube
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi shagube ga 'yan siyasa.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa wasu 'yan siyasa ba abin da su ka sanya a gaba sai zuwa gidajen talabijin suna yin kurin sun tara biliyoyi.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta hayaniya ba ce, illa dai tana mayar da hankali wajen yi wa jama'a aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

