Tirkashi: El Rufai Ya Kai Ƙarar Kwamishinan Ƴan Sanda da Wasu Jami'ai ga Hukumar PSC

Tirkashi: El Rufai Ya Kai Ƙarar Kwamishinan Ƴan Sanda da Wasu Jami'ai ga Hukumar PSC

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya rubuta takardar ƙara a gaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC)
  • A cikin takardar, ya zargi kwamishinan 'yan sandan Kaduna da wasu jami’an rundunar da "rashin gaskiya da cin amanar aiki"
  • El-Rufai ya ce ya ɗauki wannan matakin ne bayan da ya kasa samun adalci a wata wasiƙa da ya rubuta wa IGP Kayode Egbetokun

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Rikici tsakanin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da rundunar ‘yan sanda a jihar ya ɗauki sabon salo a makon nan.

Tsohon gwamnan ya kai ƙarar wasu jami'an ‘yan sanda a gaban Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) bisa zargin "rashin ƙwarewa, cin zarafin ofis, da kuma keta dokokin 'yan sanda."

Kara karanta wannan

'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki

El-Rufai ya kai karar rundunar 'yan sandan Kaduna gaban hukumar PSC
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da kwamishinan 'yan sandan Kaduna, CP Rabiu Muhammad. Hoto: @elrufai, @kadunapoliceHQ
Source: Twitter

Nasir El-Rufai ya kai karar 'yan sandan Kaduna

Jaridar Punch ta ce an samu wannan sabon bayanin ne a cikin takardar ƙarar da El-Rufai ya aika wa PSC kuma ya bayyana wa manema labarai a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya ce kwamishinan 'yan sandan Kaduna da wasu jami’an rundunar sun aikata laifuffuka da ba su dace da matsayinsu ba tun lokacin da suka fara aiki a ranar 30 ga Disamba, 2024.

Tsohon gwamnan, wanda rundunar ‘yan sandan Kaduna ta gayyace shi a kwanan nan amma ya ƙi amsa gayyatar, ya ce:

"Dole in sanar da hukumar PSC game da lamarin bayan wata wasiƙa da na aike wa babban sufeton ‘yan sanda (IGP) Kayode Egbetokun ba ta sa an dakatar da mummunan cin zarafin doka da jami’an suka yi ba."

Dalilin El-Rufai na kai karar 'yan sanda ga PSC

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Muyiwa Adekeye, ya fitar a Kaduna a ranar Litinin, El-Rufai ya ce rundunar ’yan sanda ce garkuwar Najeriya, don haka dole ne PSC ta tabbatar da tsafta da ladabi a rundunar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gayyaci El Rufai da wasu ƴan siyasa 6 kan abin da ya faru a Kaduna

El-Rufai ya bayyana cewa:

“Hakki ne na dukkanin ’yan kasa su isa ido don ganin cewa jami’an tsaro suna aiki da gaskiya da bin doka.”

Tsohon gwamnan ya zargi wasu jami’an ‘yan sanda da cewa suna “aiki domin buƙatun da ba na doka ba,” yana mai cewa irin wannan hali na ɓata sunan rundunar da kuma rage amincewar jama’a ga jagororinta.

Sahara Reporters ta rahoto El Rufai ya ce:

“Ana iya samun sauyi mai kyau ne kawai idan aka ci gaba da sanar da hukumar game da duk wani mugun hali na bara gurbin jami'ai, wandaya ya saba wa doka ta tanadin Sashe na 4 na Dokar ‘Yan Sanda ta 2020. Irin mugun wannan hali na shafar sunan ‘yan sanda kuma yana raunana amincewar jama’a ga jagororin rundunar."
El-Rufai ya ce ya kai karar 'yan sandan ga hukumar PSC ne bayan da IGP Kayode Egbetokun ya ki daukar mataki kan korafinsa.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a gidan gwamnati lokacin yana gwamna. Hoto: @elrufai
Source: Facebook

'Yan sandan Kaduna ba su ce uffan ba

Sai dai, a cikin takardar da aka rabawa manema labarai, El-Rufai bai bayyana cikakkun bayanai na laifuffukan da ya ce 'yan sandan sun aikata ba.

Kara karanta wannan

Rasuwar tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya ta bar baya da kura, an samu bayanai

Amma dai wasu na kusa da shi sun ce ƙarar tana da alaƙa da wasu matakai da ‘yan sandan Kaduna suka ɗauka a cikin ‘yan watannin nan, da ake zargin suna farautar wasu abokan siyasarsa.

Har zuwa lokacin da ake rubuta wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba ta ce komai a hukumance kan ƙarar ba, yayin da kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, bai amsa kira ko mayar da sako ba.

Kaduna: 'Yan sanda sun gayyaci su El-Rufai

Tun da fari, mun ruwaito cewa, rundunar ’yan sanda ta gayyaci tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da wasu manyan jiga-jigan ADC a jihar.

An gayyaci El-Rufai da kusoshin ADC ne kan zargin hada baki, tada zaune-tsaye, ɓarnatar da dukiya da kuma jikkata mutane a wani taron siyasa.

Nasir El-Rufai ya yi martani ga 'yan sanda kan abin da ya faru a Kaduna yayin da jigon ADC ya magantu kan wannan takardar gayyatar da aka tura masu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com