'Za a Yi Kwanaki 5 ana Malala Ruwa,' Gwamnati Ta Jero Jihohi 14 da za Su Gamu da Ambaliya

'Za a Yi Kwanaki 5 ana Malala Ruwa,' Gwamnati Ta Jero Jihohi 14 da za Su Gamu da Ambaliya

  • Ma’aikatar Muhalli ta fitar da gargaɗin ambaliya ga jihohi 14 da wurare 43 a Najeriya daga 4 zuwa 8 ga Satumba, 2025
  • Jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Ebonyi, Kano, Zamfara, Taraba, Abia sai kuma Yobe, Plateau da wasunsu
  • Gwamnatin kasar Sin ta ba da tallafin dala miliyan 1 don taimaka wa waɗanda ambaliyar ta rutsa da su a Arewa.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ma’aikatar Muhalli ta Najeriya ta fitar da gargaɗin ambaliya ga jihohi 14 tare da wurare 43 da ake san za su fuskanci mamakon ruwan sama.

Ma'aikatar ta ce akwai hasashen za a samu ruwa mai yawa daga ranar 4 zuwa 8 ga Satumba, 2025 a wasu daga cikin jihohin kasar nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci

An yi hasashen ambaliya a jihohi 14
Wasu yankuna da aka yi ambaliya a Najeriya Hoto: Dan Alheri/Mustapha Moh'd Gujba banker
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ce ruwaito cewa Hukumar Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa ce ta yi gargadin a ranar Alhamis, ta cikin sanarwar da daraktan sashen kula da ambaliya da yankunan bakin teku, Usman Abdullahi Bokani ya fitar.

Gwamnati ta yi gargadi game da ambaliya

Daily Trust ta wallafa cewa jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Ebonyi (Afikpo), Kuros Riba a (Edor, Ikom, Itigidi, Akpap), Kano (Gwarzo, Karaye), da Zamfara (Anka, Gummi, Kaura Namoda, Maradun, Shinkafi, Bukkuyum).

Sai kuma jihohin Taraba (Dampar, Duchi, Garkowa, Gassol, Gembu, Gun Gun Bodel, Kambari, Mayo Ranewo, Mutum Biyu, Bandawa, Ngaruwa) da Abia (Eziama, Umuahia).

Sauran jihohin su ne Yobe (Geidam, Kanama, Potiskum), Plateau (Langtang, Shendam, Wase) da Borno (Ngala), Imo (Okigwe, Otoko), Niger (Sarki Pawa).

Sai kuma jihohin Sakkato (Sakkwato, Wamakko, Isa, Shagari, Makira), Kaduna (Kafanchan) da Akwa Ibom (Oron).

Ambaliya ta taso Najeriya a gaba

Kara karanta wannan

Burkina Faso ta tsaurara doka, gwamnatin Soja ta dauki mataki a kan auren jinsi

Rahotanni sun ce ambaliya na daga cikin manyan matsalolin muhalli da ke addabar Najeriya, inda ake samun asarar gidaje, gonaki, da kuma yaduwar cututtuka.

Shekaru da dama da suka gabata, ruwan sama mai yawa ya haddasa lalacewar kayayyaki da rasa rayuka a sassa daban-daban na ƙasar.

Gwamnati ta yi gargadi a kan ambaliya
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar sauyin yanayi da rashin ingantattun magudanar ruwa, lamarin da ke ƙara barazana ga al’ummomi.

A halin da ake ciki, gwamnatin kasar Sin ta ba da tallafin Dala miliyan 1 don taimaka wa wadanda ambaliyar ta rutsa da su musamman a Arewa.

Ambaliya: Manyan Arewa sun kawo mafita

A wani labarin, kun ji cewa ACF ta bukaci gwamnati da jama’a musamman a yankunan da ake yawan fama da ambaliya su dauki matakan kariya domin rage illar bala’in da ake hasashen zai auku.

Wannan kira na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ACF na ƙasa, Farfesa Tukur Muhammad, ya fitar, inda ya jaddada bukatar daukar matakan gaggawa.

Kungiyar ta ce hasashen da Hukumar Kula da Madatsun Ruwa ta Ƙasa ta fitar ya nuna cewa garuruwa 1,249 a cikin kananan hukumomi 176 da ke cikin jihohi 30 da Abuja na fuskantar barazana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng