Malamin Addini na Fuskantar Tuhume Tuhume 16, Kotu Ta ba da Ajiyarsa a Gidan Yari
- Kotu ta ba da umarnin tsare wani matashin malamin addini a gidan gyaran hali bisa zargin yunkurin kisan kai da haddasa gobara
- Yanayin da ake zarginsa da 'malantar karya,' an ce matashin yana fuskantar tuhume tuhume 14, ciki har da ɓata suna da sata
- Da farko, kotu ta bayar da belin 'malamin' kan laifin bata suna, amma daga bisani ta ba da umarnin tsare shi kan wasu laifuffuka
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ebonyi - Wata Kotun Majistare da ke Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, ta ba da umarni a tsare wani malami mai suna Nwebonyi Unadinma a gidan yari bisa zargin yunkurin kisa da haddasa gobara.
Har ila yau, malamin addini Kiristan mai shekaru 24, yana fuskantar wasu laifuffuka 14, ciki har da ɓata suna, lalata dukiya da kuma sata.

Source: UGC
Jaridar Premium Times ta rahoto Lilian Aliede, lauya mai shigar da kara na 'yan sanda, ta shaida wa kotun cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mista Unadinma ya aikata laifuffukan ne a yankunan Offianka Inyima, Agharaoza, Affiauku da kuma Ochiohu Inyegu da ke cikin kananan hukumomin Izzi da Ikwo na jihar Ebonyi."
Malamin addini ya yi isharorin karya
Kafin zuwansa kotu, an zargi Mista Unadinma da fitar da abin da mutane da yawa suka kira “isharorin karya” a yankin Izzi da ke cikin jihar.
A wani misali, an zargi malamin da yin ishara cewa wani ɗan kasuwa ɗan asalin jihar Ebonyi, Emeka Mgbore, matsafi ne.
An ce Mista Unadinma ya yada bidiyon wannan "isharar karyar” a shafukan sada zumunta.
Bayan bullar bidiyon, wasu fusatattu sun kai wa dan kasuwan, wanda ke zaune a jihar Ogun hari, inda suka yashe dukkanin kayan da ke cikin shagunansa.
Ana tuhumar malami da laifuffuka 16
Bugu da kari, a wani lamari makamancin haka, malamin, ya yi kalaman cin mutunci ga wasu mazauna yankin, ciki har da Linus Uguru da Njoku Iziogo, a unguwar Offianka Inyima, kamar yadda Lilian ta shaida wa kotun.
A ranar Litinin ne ‘yan sanda suka gurfanar da Mista Unadinma a gaban kotu, bisa zarge-zarge 16, waɗanda suka haɗa da kararrakin shari’a hudu.
A lokacin sauraron karar, lauyan wanda ake kara, Emeka Anosike, ya nemi a bayar da belin wanda yake karewa kan dukkanin shari'o'in hudu.
Sai dai, jaridar Punch ta rahoto mai gabatar da kara, Mista Aliede, ta yi adawa da bukatar belin, inda ta bayar da hujjar cewa laifuffukan suna da girma sosai.

Source: Twitter
Kotu ta ba da ajiyar malami a gidan yari
Duk da haka, Alkalin Kotun, Sandra Ifeanyi-Oyibe ta bayar da belin wanda ake kara kan laifuffukan ɓata suna biyu, a kan kudi Naira miliyan hudu.
Amma, ta ki bayar da belinsa a kan sauran laifuffukan, ciki har da yunkurin kisan kai, haddasa gobara, da lalata dukiya.
Sandra Ifeanyi-Oyibe ta ce sauran shari'o'in sun fi karfinta, don haka ta ce za a ci gaba da tsare malamin har zuwa lokacin da za a gabatar da kararsa gaban wani alkalin.
Kotu ta yanke wa malami hukuncin kisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, babbar kotun jiha a Osun, ta yanke wa wani malamin addini, Kabiru Ibrahim hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Mai shari’a Lateef Adegoke, ya ce hujjojin da masu kara suka gabatar sun tabbatar da tuhumar da ake yi wa Kabiru Ibrahim, ta kashe wani Lukman Adeleke.
'Yan sanda sun ce, Kabiru ya kai jami'ansu inda ya birne gawar Adeleke, bayan ya yi mata gunduwa0gunduwa, suka gabatar da hotunan gaban kotu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


