Bauchi: Kotu ta tsare wani dan kasuwa don ya ci mutuncin alkalin kotun shari'a

Bauchi: Kotu ta tsare wani dan kasuwa don ya ci mutuncin alkalin kotun shari'a

Cif Majistare na kotu ta II a Bauchi a ranar Alhamis ta tsare wani mai treda mai shekaru 27, Gaddafi Abdulmumin a gidan gyaran hali saboda cin mutuncin wani alkalin kotun shari'a dandalin sada zumunta na Facebook.

Masu shigar da kara, Sufeta Yusuf Usman ya shaidawa kotu cewa wanda ake zargin ya ci mutuncin alkalin kotun shari'a na Liman Katugum, Muhammad Sunusi Babaji ta hanyar rubuta kalaman cin mutunci da zage-zage a shafinsa na Facebook da ka iya bata wa alkalin suna.

Usman ya shaidawa kotu cewa wanda ya shigar da karar ya sanar da kwamishinan 'yan sanda a ranar 26 ga watan Fabrairun 2020 asalin rikicin lokacin wata mata mai suna Jessica Basil ta yi karar wanda ake zargin, Gaddafi Abdulmumin a ranar 19 ga watan Satumban 2019.

Bauchi: Kotu ta tsare wani dan kasuwa don ya ci mutuncin alkalin kotun shari'a
Bauchi: Kotu ta tsare wani dan kasuwa don ya ci mutuncin alkalin kotun shari'a
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a Kano a kan batanci ga Annabi Muhammad

Takardan karar da alkalin ya shigar wa 'yan sandan ta ce, "Na saurari shari'ar su a ranar 21 ga watan Oktoban 2019. Daga bisani sun nemi a basu dama su sasanta kansu kuma na amince tunda doka ta bayar da daman hakan.

"Bayan sun sulhunta kansu, sun nemi kotu ta amince da sulhun da su kayi kuma kotu ta amince kamar yadda doka ta bayar da dama bayan nazarin yarjejeniyar da suka cimma.

"Daga baya wanda aka yi kararsa, Gaddafi Abdulmumin ya wallafa wasu rubutu a Facebook na zagi da cin mutuncin alkalin da ka iya bata min suna."

Dan sanda mai shigar da karar ya ce wanda ake zargin ya amsa laifukan a rubuce, kuma abinda ya aikata laifi ne da ya ci karo da sashi na 24 (1) (a) da (b) na dokar hana aikata laifuka ta yanar gizo na 2015 da sashi na 391 da 392 na Penal Code.

A yayin zartar da hukunci, Majistare Safiya Doma ta dage cigaba da sauraron shari'a zuwa ranar 30 ga watan Maris a yayin da ta ke sauraron shawara daga Ma'aikatar Shari'a na Jihar.

Ta bayar da umurnin a tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali na jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164