Mulkin El Rufai: Lokuta 5 da Aka Samu Hare Haren 'Yan Bangar Siyasa a Kaduna
Kaduna - Sanata Shehu Sani, ya zayyana jerin hare-haren cin zarafi da aka kai kan ‘yan adawa, ‘yan jarida da 'yan kwadago a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sanata Shehu Sani ya fito da wannan bayani ne bayan El-Rufai ya ce a cikin shekara takwas da ya yi a kan mulki, ba a taba hana ‘yan adawa yin taro ko kai musu hari ba.

Source: Facebook
Harin siyasa: Shehu Sani ya 'karyata' El-Rufai
A wata hira da Channels TV ranar Lahadi, El-Rufai ya yi Allah-wadai da dakatar da taron jam’iyyar ADC a Kaduna, yana mai dora laifin a kan gwamnatin APC mai ci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Na shafe shekara takwas matsayin gwamnan jihar, kuma ban taba hana kowace jam’iyyar adawa yin taro, ko hana a ba su wurin gudanar da taro ba. Lallai abin da ake yi yanzu ya wuce gona da iri ne."

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun gayyaci El Rufai da wasu ƴan siyasa 6 kan abin da ya faru a Kaduna
- Malam Nasir El-Rufai.
Sai dai a wata wallafa mai tsawo da ya yi a shafinsa na X, Shehu Sani ya ce akwai tarihin “tada rigima da hare-haren siyasa” da aka kai wa 'yan adawa a lokacin mulkin El-Rufai.
Legit Hausa ta yi nazari kan bayanai da Sanata Shehu Sani ya gabatar, tare da bincikar ko da gaske hare-haren sun faru, ko kuma ba su faru ba.
Mulkin El-Rufai: Hare-haren siyasa a Kaduna
1. Harin ofishin mazaba (Disamba, 2016)
Shehu Sani ya ce ‘yan bindiga sun kai hari ofishin mazabarsa, inda suka jikkata ma’aikata da magoya bayansa tare da sace wayoyi da wasu muhimman kayayyaki.
Bincike:
Rahoton jaridar Daily Trust na ranar 4 ga Disamba, 2016, ya tabbatar da cewa 'yan daba sun farmaki ofishin Shehu Sani, lokacin yana ganawa da magoya bayansa.
An ce 'yan dabar sun farmaki ofishin da ke No1 Junction road, kusa da sha-tale-talen filin wasanni na Kaduna, a ranar 3 ga Disamba, 2016.
'Yan dabar sun shiga ofishin dauke da makamai, ciki har da bindigogi biyu, takubba da adduna, inda suka ci zarafin magoya bayan sanatan su 25, suka kore su daga ofishin, bayan kwace wayoyinsu, kamar yadda muka ruwaito.
Mai ba Sanata Shehu Sani shawara na musamman, Suleiman Ahmed ya ce wannan harin siyasa ne, domin dakile farin jinin sanatan.
2. Harin sakatariyar NUJ (Yuli, 2017)
Shehu Sani ya ce ‘yan daba dauke da makamai sun farmaki ‘yan siyasa da ‘yan jarida a ofishin NUJ na Kaduna, a ranar 30 ga Yulin 2017.
Bincike:
A ranar 31 ga Yulin 2017, jaridar Punch ta rahoto cewa, wasu ’yan dabar siyasa sun farmaki sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Kaduna a ranar 30 ga Yuli, 2017.
Sun ji wa ’yan jarida rauni, sun lalata kadarori, tare da tarwatsa taron manema labarai da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar suka shirya.
An ruwaito cewa ’yan daban sun rinjayi ’yan sanda da ke bakin ƙofar sakatariyar NUJ, inda Sanata Shehu Sani da Suleiman Hunkuyi suka gudanar da taron manema labarai don nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen wakilan jam’iyyar.
Jim kadan bayan farmaki, El-Rufai (lokacin yana gwamna) ya yi Allah wasdai da harin, tare da umartar jami'an tsaro su gaggauta gudanar da bincike kan lamarin.
3. El-Rufai ya la'anci sanatoci 3 (Mayu, 2018)
Sanata Shehu Sani ya ce a ranar 10 ga Mayu, 2018, El-Rufai ya la'anci sanatocin Kaduna uku, a wajen taron APC a filin Ranchers Bees.
Bincike:
Binciken Legit Hausa ya gano cewa, El-Rufai ya la'anci 'yan majalisar dattawan a ranar Juma'a, 4 ga Mayun 2018, sabanin ranar 10 ga Mayu da Shehu Sani ya ce.
Mun rahoto cewa, a wajen taron APC da aka gudanar a filin Ranchers Bees, El-Rufai ya la'anci sanatocin saboda sun hana majalisar dattawa ta amince ya karbi sabon rancen $350m daga Bankin Duniya.
"Bankin Duniya ya yanke shawarar ba mu rancen $350m don mu gudanar da ayyukan raya al'ummar Kaduna. Amma makiyan jama'armu, wadannan makiyan Kaduna uku (sanatoci), da ke a majalisar dattawa, sun dakile hakan. Allah ya tsine masu!"
- Nasir El-Rufai.
Sai dai, Legit Hausa ta fahimci cewa, ba a samu tashin hankali ko wani harin ta'addanci a wannan furuci na El-Rufai ba, don haka, ba za a kira shi da hare-hare ba, sabanin jadawalin Shehu Sani.

Kara karanta wannan
Baba Ahmed ya fadi abin da ya kamata a yi wa El Rufai kan zargin ba 'yan bindiga kudi
4. Harin otel din NUT (Afrilu, 2018)
Sanata Shehu Sani ya yi ikirarin cewa ‘yan daba sun kai hari wajen taron siyasa da Sanata Suleiman Hunkuyi ya jagoranta a otel din NUT a ranar 29 ga Afrilu, 2018.
Bincike:
Jaridar The Nation ta tabbatar da wannan ikirari, a rahoton da ta fitar ranar 30 ga Afrilu, wanda ya ce 'yan daba 10 ne suka mamaye wajen taron.
Abin bai tsaya a nan, sun farfasa gilassan motocin da ke ajiye a harabar otel din, kafin daga bisani ’yan sanda su tarwatsa su.
Ko da yake babu wanda ya rasa ransa, amma mutane biyar sun jikkata, inda aka garzaya da su Asibitin Kwararru na Barau Dikko da ke cikin babban birnin jihar.
Sai dai, Legit Hausa ba ta iya cin karo da wani rahoto da ya nuna cewa wani matashi mai suna Labaran Umar daga Badarawa ya rasa ransa a harin ba, kamar yadda Shehu Sani ya yi ikirari.

Source: Twitter
5. Harin zanga-zangar NLC (Mayu 18, 2021)
Shehu Sani ya ce ‘yan daba sun kai hari kan 'yan kwadago, lokacin da suka yi zanga-zangar nuna adawa da matakin El-Rufai na korar dubban ma’aikata.
Tsohon sanatan ya ce NLC ta zargi hadimin gwamna da jagorantar ‘yan daban, inda kungiyar ta bukaci a kama shi, amma daga baya gwamnatin jihar ta ayyana shugaban NLC, Ayuba Wabba, a matsayin wanda ake nema bisa zargin “zagon kasa ga tattali.”
Bincike:
Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Ayuba Wabba (a wancan lokacin), ya ce gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Nasir El-Rufai ta ɗauko hayar motoci 50 cike da ’yan daba domin kai hari ga ma’aikatan da ke gudanar da zanga-zanga a jihar.
Wabba ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 19 ga Mayu, 2021, yayin da yake magana a shirin Sunrise Daily na tashar Channels TV a Abuja.
Ya zargi El-Rufai da ba kowanne matashi N500 domin su tarwatsa zanga-zangar ma’aikatan da suka fito nuna adawa da korar dimbin ma’aikata a jihar.
“Mun tsira daga wadannan” - Shehu Sani
Yayin da yake tunawa da abubuwan da suka gabata, Shehu Sani ya rubuta:
“Cikin hukuncin Ubangijiji, mun tsira daga dukkanin wadannan. Ana iya tabbatar da wadannan abubuwa ta hanyar binciken Google ko kuma kowanne dandali na yanar gizo.”
Kaduna: 'Yan sanda sun gayyaci El-Rufai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan Kaduna ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai domin amsa wasu tambayoyi.
Sashen binciken laifuffukan ta'addanci na rundunar ne ya gayyaci El-Rufai da wasu manyan shugabannin ADC a Kaduna, kan wata kara da aka shigar da su.
Rundunar 'yan sandan ta ce ta gayyaci El-Rufai da mutane shida din ne kan zargin aikata laifuffukan da suka shafi tayar da zaune tsaye, lalata kadarori da sauransu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



