Yan daba sun kai hari ofishin kamfen Shehu Sani a Kaduna
- Mun gode Allah wurin akwai jama’a kuma akwai yan sanda ko da yaushe
- Mai magana da yawun Sanatan ya fada ma Jaridar Premium Times
Jaridar Premium Times ta bada rahoton cewa wasu yan bindiga sun kai hari ofishin kamfen Sanata Shehu Sani inda mutane da dama sun jinkita.
Shaidu sun bayyana cewa magoya bayan sanatan na ganawa ne a ofishin kamfen yayinda yan bindigan suka fara harbinsu ,wasu da dama sun jinkita.
KU KARANTA: DSS ta saki makusancin Buhari bayan watanni 5 a tsare
Ma’aikacin sanatan, Suleiman Sule, ya bayyana cewa wasu mabiyan maigidansa suna ganawa ne abun ya faru.
Mai magana da yawun Sanatan ya fada ma Jaridar Premium Times yace jami’an yan sanda sun tabbatar da tsaro.
Idanuwan Shaidu sun ce: Sun zo da muggan makamai kuma suka wuce inda ofishin yan sandan suka watsa mutanen da ganawa.
Mun gode Allah wurin akwai jama’a kuma akwai yan sanda ko da yaushe. Kafin abun yayi muni ,yan daban suka gudu.
A lokacin da ake tattara wannan labari, ba’a san samu rahoton dalilin da yasa aka kai harin ba, amma an san cewa Shehu Sanin a rikici da gwamnan Mallam Nasir El-Rufai.
Ku biyo mu shafin m na Tuwita @naijcomhausa.
Asali: Legit.ng