Yanzu Yanzu: Yan daba sun tarwatsa zanga-zangar NLC da ke gudana a Kaduna
- ‘Yan daba sun tarwatsa zanga-zangar lumana da kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) ke gudanarwa a jihar Kaduna
- Wasu daga cikin maharan sun rufe fuskokinsu dauke da wukake da sanduna
- Sai dai shugaban kunggiyar kwadago ta kasa, Ayuba Wabba ya zari gwamnan jihar, Nasir El-Rufai da turo yan barandan
Wasu ‘Yan daba da aka yo haya sun tarwatsa zanga-zangar lumana da kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) ta fara a jihar Kaduna, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A yayin da zanga-zangar ke gudana, sai wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka shigo wajen a motoci biyu da adaidaita sahu inda suka fara jifan masu zanga-zangar.
Wasu daga cikin maharan sun rufe fuskokinsu dauke da wukake da sanduna.
KU KARANTA KUMA: Wata kungiyar jama’a ta caccaki MURIC, ta ce Musulmi ba zai gaji Buhari ba
“Sun zo ne a cikin mota suka fara jifan ma’aikatan da ke zanga-zangar. Sai mutane sun fara gudu amma ma’aikatan sun sami damar korarsu,” wani ganau ya shaida wa jaridar.
Channels TV ta kuma ruwaito cewa Ma’aikatan sun hallara a sanannen hanyar shataletale na NEPA da ke cikin babban birnin na Kaduna don ci gaba da zanga-zangar su a rana ta biyu lokacin da yan daban suka mamaye yankin suka fara jifan su da duwatsu da wasu muggan makamai.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa ba a san wanda ya aiko maharan ba a zahiri, amma Shugaban NLC, Ayuba Wabba ya nuna yatsa ga gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.
Da yake magana da gidan Talabijin na Channels a yayin zanga-zangar, Wabba ya ce ya sanar da DSS ne bayan ya samu labari tun farko game da shirin hargitsa zanga-zangar.
“Yau rana ce ta bakin ciki a tarihin dimokiradiyya a Najeriya. Da sanyin safiyar yau, mun sami sahihan bayanai cewa El-Rufai ya yi hayar wani Alhaji Hassan da wasu yan baranda don su kawo mana hari.
“Yayin da muke nan, sun zo amma Alhamdulillahi mun kore su saboda muna da yawa. Mu ba 'yan daba bane kuma ba ma amfani da 'yan daba mu ma'aikatan Najeriya ne," in ji Wabba.
KU KARANTA KUMA: INEC ta koka, ta ce babban zaben 2023 na iya samun matsala
Jami'an tsaro sun tarwatsa 'yan bindigar da barkonon tsohuwa.
Wabba shine kan gaba a rana ta biyu na zanga-zangar NLC duk da cewa gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana neman sa ruwa a jallo.
A baya legit.ng ta kawo cewa Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya alanta neman shugaban kungiyar kwadagon Najeriya NLC, Kwamred Ayuba Wabba, da sauran shugabannin da suka shiga jihar zanga-zanga ruwa a jallo.
El-Rufa'i ya yi alkawarin bayar da kyautar kudi ga duk wanda ya san inda wadannan shugabannin kwadago suke boye.
Ya tuhumcesu ne da laifin fito-na-fito da tattalin arzikin jihar Kaduna kuma hakan ya sabawa doka.
Asali: Legit.ng