Karshen Alewa: Ƴan Sandan Najeriya Sun Cafke Yusuf, Fitaccen Mai Garkuwa da Mutane
- Rundunar ’yan sandan Benue da Enugu sun cafke jagoran ’yan bindiga, Yusuf Muhamed, bayan dogon lokaci yana addabar jama'a
- Shugaban karamar hukumar Ogbadibo, Sunday Ajunwa, ya tabbatar da cewa Yusuf ya kasance yana azabtar da wadanda ya sace
- Ajunwa ya ce yanzu yankin ya samu saukin rashin tsaro, amma dokar hana fita daga 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe tana nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue - Rundunar ’yan sandan jihohin Benue da Enugu tare da hadin gwiwar matasan 'yan banga sun cafke wani da ake zargin shugaban kungiyar ’yan bindiga ne.
An rahoto cewa jami'an tsaron sun cafke Yusuf Muhamed a kauyen Orokam, karamar hukumar Ogbadibo ta jihar Benue.

Source: Twitter
An cafke mai garkuwa da mutane a Benue
Bisa ga bayanan mazauna yankin, Yusuf da tawagarsa sun shafe lokaci suna addabar garuruwa da dama a karamar hukumar, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna yankin sun ce wannan ne dalilin da ya sa shugaban karamar hukumar ya sanya dokar hana fita domin dakile matsalar.
Wani mazaunin yankin mai suna Mike Agbo ya bayyana cewa an cafke jagoran ’yan bindigar tare da wasu daga cikin mabiyansa a makon nan.
Ya bayyana cewa wadanda aka taba sacewa sun tabbatar da cewa Yusuf shi ne mutum mafi tsanani wajen azabtar da wadanda aka sace a sansanin ’yan bindigar.
Yadda aka kama mai garkuwa da mutane
A cewarsa, an gano shi ne cikin sauki saboda akwai wani babban tabo a hannunsa na hagu, wanda ya zama tamkar wata shaida ta gane shi.
Shugaban karamar hukumar Ogbadibo, Sunday Ajunwa, ya tabbatar da kamen, inda ya ce:
“Hakika an cafke Yusuf ta hanyar hadin gwiwar ’yan sanda daga Makurdi da Enugu, tare da 'yan banga na yankin.
"Ya yi yunkurin tserewa, amma matasa suka bi shi suka kamo shi. Wadanda aka sace sun tabbatar da yadda ya azabtar da su lokacin da suke hannun dabarsa."
Jaridar This Day ta rahoto Ajunwa ya kara da cewa Yusuf tare da wasu mutum 21 suna hannun ’yan sanda a halin yanzu.

Source: Original
'Yan sanda sun yi magana a Benue
Duk da yake ya nuna damuwa kan matsalar tsaro da ta dade tana addabar al’ummar yankin, ya ce an samu dan sauki bayan daukar matakai.
“Yanzu tsaron yankin Orokam ya dan inganta, duk da cewa dokar hana fita daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe tana nan daram.
"Sai dai ina tunanin janye ta bayan ganawa da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki."
- Sunday Ajunwa.
Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar Benue, DSP Udeme Edet, ta bayyana cewa ba ta samu cikakken rahoto kan lamarin ba tukuna.
“Har yanzu ban tabbatar da rahoton ba. Idan na samu cikakken bayani, za a sanar da jama'a.”
- DSP Udeme Edet.
An cafke mai garkuwa da mutane a Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an DSS sun cafke Yahaya Zango, wani mai garkuwa da mutane da ake nema ruwa a jallo, yana shirin tafiya aikin Hajji ta Abuja.
Yahaya Zango ya nemi ɓoye kansa a sansanin alhazan Abuja, amma jami'an DSS suka gano shi, tare da cafke shi cikin gaggawa.
Jama’a sun caccaki lamarin a intanet, inda wasu ke tambayar Yahaya abin da zai fadawa Allah game da zuwa Hajji da kudin ta'addanci.
Asali: Legit.ng


