'Yakin ba na Sojoji Kadai ba ne,' Janar Buratai Ya Kawo Dabarar Murkushe 'Yan Ta'adda

'Yakin ba na Sojoji Kadai ba ne,' Janar Buratai Ya Kawo Dabarar Murkushe 'Yan Ta'adda

  • Tsohon babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya ba gwamnati shawara kan murkushe 'yan ta'adda a Najeriya
  • Buratai ya ce akwai bukatar gwamnati ta yi amfani da tsarin da ta yi amfani da shi a lokacin COVID-19 wajen dawo da tsaro
  • Ya jaddada cewa haɗin kan jama’a, wayar da kai da tsare-tsaren dogon lokaci ne kaɗai za su taimaka wajen murkushe ‘yan ta’adda

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanal Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya ba gwamnatin Najeriya shawara kan murkushe 'yan ta'adda.

Janar Buratai ya ce akwai bukatar a ɗauki irin tsarin da aka yi amfani da shi a lokacin kulle na COVID-19, domin yaƙar 'yan ta’addanci, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Tsohon hafsan sojojin kasa, Tukur Buratai ya kawo dabarar murkushe 'yan ta'adda a Najeriya.
Tsohon hafsan sojojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai (mai ritaya) a wajen wani taro. Hoto: Tukur Buratai
Source: Facebook

Tsohon hafsan sojojin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Channels a shirin Sunrise Daily a safiyar Juma’a.

Kara karanta wannan

'A jira mu," Gwamnatin Tinubu za ta wallafa sunayen masu daukar nauyin ta'addanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dabarar murkushe 'yan ta'adda' - Tukur Buratai

Janar Tukur Buratai ya ce bai kamata a bar batun tsaro ga sojoji kaɗai ba, yana mai cewa dole a ɗauke shi a matsayin matsalar ƙasa baki ɗaya da ke buƙatar sadaukarwa daga dukhan ‘yan Najeriya.

“A duk lokacin da ƙasa ta shiga wani hali, to dole ne mu tashi gaba ɗaya, ba wai a bar aikin ga sojoji kaɗai ba,” inji Buratai.

Ya kara da cewa

“Mu waiwaya lokacin COVID-19, kuɗaɗe nawa aka kashe, kuɗaɗe nawa aka saka a fannin bayanai, sadarwa, tallace-tallace, tallafin kayan abinci da matakan kariya?
“An kulle ƙasar baki ɗaya saboda COVID-19. To yanzu ma za mu iya yin hakan. Za mu iya kulle ƙasar nan domin tabbatar da cewa kowa ya mai da hankali wajen kawar da wannan annobar ta ‘yan ta’adda."

Buratai ya dade da gargadin gwamnati

Tsohon babban hafsan soja, wanda ya rike mukamin jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, ya ce ya dade yana jan hankalin gwamnati game da yaƙi da ta’adda.

Kara karanta wannan

Al'umma sun samu sauƙi: Sojoji sun damƙe hatsabibin ɗan bindiga, yaransa 13

Ya ce ya sha nanata wa gwamnati cewa yaƙi da ta'addanci na iya ɗaukar lokaci mai tsawo fiye da yadda ake zato idan ba a ɗauki tsare-tsare na dogon lokaci ba.

“Tun kafin in bar ofis, kuma jim kaɗan bayan an naɗa ni jakada a Jamhuriyar Benin, na aika da gargadi cewa wannan yaƙin zai iya ɗaukar lokaci mai tsawo. Ba abin da za ka zura ido, ka ce za ka yi addu’a ba ne kawai. Muna buƙatar tsari na dogon lokaci."

- Laftanal Janar Tukur Buratai.

Ya tuna da lokutan da ‘yan Najeriya suka haɗa kai a lokacin bala’in ambaliyar ruwa da ta auku a Maiduguri, inda ya ce irin wannan haɗin kai zai iya ƙarfafa yaƙin da ake yi da rashin tsaro a yanzu.

Tukur Buratai ya ce dole ana bukatar hadin kan jama'a da wayar da kansu domin magance matsalar tsaro
Tsohon hafsan sojin kasa, Tukur Buratai a kan doki ranar da aka yi masa nadin sarautar Betaran Biu. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

An kashe mutane 50 a mako guda

Maganganunsa sun zo ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a ƙasar, musamman jihohin Arewa ta Yamma.

Hukumar NHRC da ke kare haƙƙin bil’adama ta ƙasa, a sabon rahotonta, ta nuna damuwa kan ƙaruwar take hakkin rayuwa da ’yancin dan Adam, inda ta ce sama da mutane 50 aka kashe a hare-hare daban-daban cikin sati guda.

Kara karanta wannan

EFCC ta baza koma, tana neman surukin Atiku Abubakar ruwa a jallo

Buratai ya jaddada cewa, banda yaƙin sojoji, dole a samu ci gaba da haɗin kan jama’a ta hanyar wayar da kai da kuma shiga tsakani.

Abin da ke jefa matasa a ta'addanci

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon hafsan sojojin kasa, Janar Tukur Buratai, ya yi magana kan abubuwan da ke kara ta'addanci a Najeriya.

Buratai ya jaddada cewa rashin gwamnati a yankunan da ba a kula da su na taimakawa wajen daukar matasa cikin kungiyar ta’addanci, musamman Arewa.

Tsohon shugaban sojojin ya ce tilas ne a karfafa matasa domin su zama ginshikan ci gaba, ba barazana ba ga zaman lafiya da makomar Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com