Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar Buratai a matsayin Ambasada

Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar Buratai a matsayin Ambasada

- Laftanan Janar Buratai ya koma cikin gwamnati bayan yan kwanaki da ritaya

- Majalisa ta amince da nadinsu bayan zaman tantancesu da akayi

Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da tsaffin hafsoshin tsaron Najeriya a matsayin sabbin jakadun Najeriya zuwa kasashen waje.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana hakan a zauren majalisa a ranar Talata, 23 ga Febrairu, 2021.

Ahmad Lawan ya bayyana cewa wadannan sabbin jakadu sun yiwa Najeriya bauta iyakan kokarinsu.

"Wadannan mutane da muka tabbatar sun bautawa kasar nan kwarai da gaske. Muna musu fatan nasara matsayin jakadu," Lawan yace.

"Mun tabbatar da Janar Abayomi G Olonisakin (Mai ritaya) matsayin Jakada"

"Mun tabbatar da Lafatanan Janar Tukur Buratai (Mai ritaya) matsayin Jakada"

"Mun tabbatar da Vice Admiral Inok- Ete E (Mai ritaya) matsayin Jakada"

"Mun tabbatar da Air Marshal Sadique B. Abubakar matsayin Jakada"

"Mun tabbatar da Air Vice Marshal Muhammad S. Usman matsayin Jakada"

KU KARANTA: El-Rufai: Najeriya ta fi kowace kasa a duniya yawan talakawa

Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar Buratai a matsayin Ambasada
Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar Buratai a matsayin Ambasada Credit: @NGRSenate
Source: UGC

KU KARANTA: Direbobin keke napep sun dage yajin aiki a jihar Kano

KU KARANTA: El-Rufai: Najeriya ta fi kowace kasa a duniya yawan talakawa

A ranar Alhamis, 18 ga Febrairu, 2021, tsaffin hafsoshin tsaro da shugaba Muhammadu Buhari ya zaba a matsayin sabbin jakadu sun dira majalisar dattawa don tantancesu da tabbatar da su, Vanguard ta ruwaito.

Mambobin majalisar sun fara tantancesu amma an hana yan jarida shiga.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng

Online view pixel