Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi Sun Raba Naira Tiriliyan 2 a Yuli

Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi Sun Raba Naira Tiriliyan 2 a Yuli

  • Asusun FAAC ya raba jimillar Naira tiriliyan 2.001 ga gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi a matsayin kason Yuli, 2025
  • Rahoton ya nuna an samu Naira tiriliyan 1.282.872 daga kuɗaɗen da aka tatso, Naira biliyan 640.610 daga VAT, da sauran bangarori
  • Gwamnatin tarayya ta samu biliyan 735.081, jihohi sun samu biliyan 660.349, ƙananan hukumomi sun samu biliyan 485.039

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Naira tiriliyan 2.001 ne jimillar kudaden da asusun FAAC ya rabawa gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi a Yulin 2025.

An gudanar da rabon kuɗaɗen ne a taron watan Agusta 2025 na kwamitin rabon kudin asusun haɗin gwiwar tarayya (FAAC) a birnin Abuja.

FAAC ta raba sama da Naira tiriliyan 2 ga gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da gwamnonin Najeriya a babban birnin tarayya Abuja. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

FAAC ta tattara Tiriliyan 2 a Yuli, 2025

Wannan na kunshe ne a cikin wani rahoto da NTA News ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma'a, 22 ga Agusta, 2025.

Kara karanta wannan

Farashin litar mai ya haura N1000, NBS ta bayyana jihohi 3 da fetur ya fi araha

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa jimillar kuɗaɗen da aka raba sun haɗa da Naira tiriliyan 1.282.872 na kuɗaɗen da aka tatso da Naira biliyan 640.610 na kuɗin VAT.

Sauran kuɗaɗen sun fito ne daga Naira biliyan 37.601 na kuɗin harajin EMTL, da Naira biliyan 39.745 na banbancin musayar kuɗi.

Sanarwar kwamitin FAAC ta bayyana cewa jimilllar kuɗaɗen da suka samu a watan Yulin 2025 sun kai Naira tiriliyan 3.836.980.

FAAC: Banbancin kudin Yuli da Yuni, 2025

Jimillar abin da aka cire na tattara kuɗaɗen sun kai Naira biliyan 152.681, yayin da aka ware Naira tiriliyan 1.683.471 domin tura kuɗi, tallafi, maido da kuɗi da kuma ajiya.

A cewar sanarwar, jimillar kuɗaɗen da aka samu a watan Yulin 2025 sun kai Naira tiriliyan 3.070.127, wanda ya ragu da Naira biliyan 415.108 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 3.485.235 da aka samu a watan Yunin 2025.

Jimillar kuɗin VAT da aka samu a watan Yulin 2025 ta kai Naira biliyan 687.940, fiye da Naira biliyan 678.165 da aka samu a watan Yunin 2025 da Naira biliyan 9.775.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta rufe shafukan 'yan Najeriya miliyan 13 a Facebook, Instagram da TikTok

Gwamnatin tarayya ta tashi da N735bn, jihohi N660bn, kananan hukumomi N485bn a Yuli, 2025 daga FAAC
Shugaba Bola Tinubu, ministoci na tattauna wa a wani taro. Hoto: @FMINONigeria
Source: Twitter

Kudaden da gwamnatoci suka samu daga FAAC

Asusun FAAC ya kuma bayyana cewa daga cikin jimillar Naira tiriliyan 2.000.828 da aka raba, gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 735.081, jihohi sun samu Naira biliyan 660.349.

Ƙananan hukumomi sun samu Naira biliyan 485.039, yayin da aka raba Naira biliyan 120.359 (kashi 13% na kuɗaɗen ma’adanai) ga jihohin da abin ya shafa a matsayin kuɗin ribar ma’adanai.

A watan Yuli 2025, kuɗin harajin ribar man fetur (PPT), kudin haya na man fetur da iskar gas, harajin EMTL da kudin harajin cikin gida sun ƙaru sosai, yayin da VAT da kudin shigo da kaya suka ƙaru kaɗan.

Sai dai kuɗin harajin kamfanoni (CIT) da kudin CET sun ragu, kamar yadda rahoton jaridar The Nation ya nuna.

Zamfara za ta daina dogaro da FAAC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya yi ƙarin haske kan yadda ɓangaren ma'adanai na jihar ke tafiya.

Kara karanta wannan

Gidaje miliyan 2.2 za su samu kudi a sabon shirin tallafin gwamnatin Tinubu

Alhaji Dauda Lawal ya bayyana cewa jihar Zamfara ba ta samun ko sisin kwabo daga fannin a halin yanzu, amma ya ce zai bunkasa fannin a mulkinsa.

Gwamnan ya bayyana cewa fannin ma'adanai kawai zai sa jihar Zamfara ta daina dogaro da kudin da FAAC ke rabawa gwamnatoci a kowane wata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com