Isra'ila a Najeriya: Gumi Ya Ce a Fara Tsammanin Kashe Shugabanni Musulmai

Isra'ila a Najeriya: Gumi Ya Ce a Fara Tsammanin Kashe Shugabanni Musulmai

  • Sheikh Ahmad Gumi ya nuna rashin jin daɗi kan zuwan mataimakiyar ministar harkokin wajen Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz Najeriya
  • Malamin ya yi zargin cewa Isra’ila na iya amfani da wannan ziyara wajen cutar da shugabannin Musulmi a kasar nan
  • Haskel ta gana da manyan shugabannin Kiristoci a Abuja tare da tattaunawa kan haɗin kai da alaƙar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kakkausar suka ga ziyarar mataimakiyar ministar harkokin wajen Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz, Najeriya.

Sheikh Gumi ya bayyana damuwarsa cewa Isra’ila na iya amfani da wannan ziyara wajen aiwatar da manufofinta da za su iya cutar da Musulmi a Najeriya.

Malamin addini, Sheikh Gumi yayin da ya ke wa'azi
Malamin addini, Sheikh Gumi yayin da ya ke wa'azi. Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa malamin ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

'Gwamnan CBN na iya fin shugaban kasa albashi,' Gwamnati za ta kara wa jami'ai kudi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A gefe guda, gwamnatin Isra’ila ta ce ziyarar ta shafi ƙarfafa alaƙa tsakanin ƙasashen biyu da kuma bunƙasa ci gaba ta fuskar fasaha da ɗorewar tattalin arziki.

Taron jami’an Isra’ila da Kiristoci a Abuja

Rahoton Jewish News Syndicate ya nuna cewa Sharren Haskel-Harpaz ta gana da shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya, Daniel Okoh, a gidan jakadan Isra’ila a Abuja, Michael Freeman.

Taron ya kuma samu halartar manyan shugabannin Kirista kamar Faith Emmanuel Benson Idahosa II, Fasto Poju Oyemade da Fasto Paul Enenche.

Ma'aaktar harkokin waje ta wallafa a X cewa Bianca Odumegwu-Ojukwu ma ta gana da Haskel inda ta bayyana bukatar ƙarfafa haɗin kan Najeriya da Isra’ila.

Isra’ila ta yi bayanin manufarta a Najeriya

A jawabin da aka fitar, Haskel ta bayyana cewa Najeriya da Isra’ila suna da ƙalubale iri ɗaya, kuma haɗin kan ƙasashen biyu zai iya samar da zaman lafiya da ci gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta biya wa Kiristoci rabin kudin kujerar ziyara zuwa Isra'ila

Ta ce Isra’ila za ta yi amfani da fasahar zamani da kirkire-kirkire wajen ba da gudunmawa a sassa daban-daban da suka haɗa da ci gaban dorewa.

Haka kuma, an sanar da cewa tawagar Isra’ila za ta ci gaba da ziyarar Afirka, inda za su je Sudan ta Kudu a matsayin tarihi na farko na irin wannan tattaunawa.

Gumi ya nuna damuwa da hadarin ziyarar

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi tsokaci mai tsauri kan wannan ziyara inda ya yi gargadi kan ziyarar.

Ya bayyana cewa:

“Mossad na Abuja!? Ya kamata mu fara sa ran hallaka wasu shugabannin Musulmi”

Gumi ya tuna cewa tsohon shugaban kasa Sani Abacha ya rasu kwatsam a daren da ya karɓi Yasir Arafat a Najeriya, yana mai zargin cewa hakan na iya da alaƙa da shisshigin Isra’ila.

Ministar harkokin wajen Najeriya a wani taro
Karamar ministar harkokin wajen Najeriya a wani taro. Hoto: @NigeriaMFA
Source: Twitter

Gargadin Gumi ga gwamnatin Najeriya

Sheikh Gumi ya ƙara bayyana cewa ba da dama ga Isra’ila a Najeriya ba zai amfanar da gwamnatin Bola Tinubu ba.

Ya ce Isra’ila ƙasa ce da take da tarihi na wariyar launin fata da take adawa da Musulunci, don haka bai dace Najeriya ta ba ta damar shiga cikin harkokin cikin gida ba.

Kara karanta wannan

Akpabio ya bayyana ana rade radin shugaban majalisa yana kwance a asibitin Landan

Gumi ya jaddada cewa shawarar da aka bai wa shugaban kasa kan karɓar Isra’ila ba ta da amfani, yana mai cewa “zai jawo masa hasara fiye da abin da zai iya samu.”

Kiristoci sun samu tallafin zuwa Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NCPC ta bayyana cewa a watan Satumba za ta fara jigilar Kiristoci zuwa Isra'ila ibada.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Najeriya ta sanya wa Kiristoci tallafin kashi 50 na kudin zuwa ibadar.

Baya ga haka, shugaban hukumar ya bayyana cewa 'yan majalisa kusan 100 ne za su yi tarayya da su wajen zuwa ziyarar da za su yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng