Sabuwar Zanga Zanga Ta Barke a Birnin Gusau, An Toshe Kofar Shiga Gidan Gwamnati

Sabuwar Zanga Zanga Ta Barke a Birnin Gusau, An Toshe Kofar Shiga Gidan Gwamnati

  • Daruruwan mazauna kauyuka 30 a Zamfara sun gudanar da zanga-zanga don nuna fushinsu kan hare-haren ‘yan ta’adda
  • Mata da yara ne suka fi yawa a masu zanga-zangar, inda suka rika kira ga Gwamna Dauda Lawal da Bello Matawalle su kai masu dauki
  • Masu zanga-zangar sun bayyana cewa sun karar da duk wasu kadarori da suka mallaka don karbo 'yan uwansu daga masu garkuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Daruruwan mazauna kauyuka 30 a gundumomin Dan-Isa da Kagara a karamar hukumar Kaura-Namoda, jihar Zamfara sun gudanar da zanga zanga.

Mazauna kauyukan sun mamaye titunan Gusau, babban birnin jihar Zamfara a ranar Talata, don nuna fushinsu kan karuwar ayyukan 'yan ta'adda a yankunansu.

Mata da yawa sun gudanar da zanga zanga a Gusau kan matsalar tsaro
Yadda mata da yara suka mamaye titunan Gusau a matakin zanga-zanga kan matsalar tsaro. Hoto: @secmxx
Source: Twitter

Mata da yara sun yi zanga-zanga a Gusau

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa mata da kananan yara ne mafi akasarin wadanda suka gudanar da zanga zangar a birnin Gusau.

Kara karanta wannan

Jiragen yaki sun kona 'yan bindiga kurmus suna bikin aure a dajin Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce masu zanga zangar sun rika jerin gwano a titunan Gusau dauke da kwalaye da aka rubuta sakonni daban daban a kansu.

A jikin wasu kwalayen, an rubuta, "Muna bukatar zaman lafiya a kauyukan Kaura-Namoda," "Muna rokon Gwamna Dauda Lawal da Matawalle su cece mu," da kuma "Ana kashe mutanenmu kullum."

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Lawal Kamilu daga gundumar Dan-Isa ya yi magana da manema labarai a gaban gidan gwamnatin jihar a Gusau.

'Yan bindiga sun kashe daruruwan mutane

Lawal Kamilu ya ce sun shirya zanga zangar ne domin mika kokensu ga gwamnati biyo bayan shekarun da suka kwashe suna fuskantar hare-haren 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da barayin shanu.

"Mun fito ne daga kauyuka 30. Mafi akasarinmu a nan mata ne da yara saboda da yawan mazajen garuruwan an kashe su ko 'yan bindiga sun yi garkuwa da su."

Kara karanta wannan

Babu dadi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata yayin wani hari a Zamfara

- Lawal Kamilu.

A cewarsa, 'yan ta'adda sun hallaka daruruwan mutane a garuruwansu, yayin da har yanzu wasu ke hannun masu garkuwa, inda ake neman miliyoyin Naira na kudin fansa, inji rahoton TVC.

Lawal ya kara da cewa:
"Mun sayar da gonakinmu da duk wasu kadarori da muka mallaka domin biyan kudin fansar 'yan uwanmu da aka yi garkuwa da su."
Masu zanga-zangar sun ce 'yan bindiga sun hallaka daruruwan mutane a garuruwansu na Zamfara
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Zamfara a Arewa maso Yammacin kasar nan. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masu zanga-zangar sun roki gwamnati

Masu zanga zangar dai sun yi kira ga Gwamna Dauda Lawal da karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da ma Shugaba Bola Tinubu da su gaggauta magance matsalar tsaro da ke neman gamawa da su a jihar Zamfara.

"Muna rokon dukkanin hukumomin da abin ya shafa da su ceto mu daga kangin da 'yan bindiga suka sanya mu. Mutanen Zamfara sun mika lamuransu ga Allah."

- Lawal Kamilu.

An rahoto cewa an jibge jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda a zagayen gidan gwamnatin da kuma wasu muhimman wurare a Gusau domin ganin an yi zanga-zangar lafiya.

Kara karanta wannan

Kano: Mata sun gaji, ɗaruruwa sun fito zanga zanga kan yawaitar faɗan daba

'Yan bindiga sun taso garuruwa 35 a Zamfara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun karbi N800,000 daga kowane kauye daga cikin ƙauyuka 35 da ke karkashin gundumar Ɗan Isa a Zamfara.

Hakimin Ɗan Isa, Malam Hassan Yarima ya tabbatar da hakan, ya ce sai da suka karɓi kudin sannan suka bar manoma suka fara zuwa gona.

Malam Hassan ya ce idan Allah ya kaimu aka gama noman daminar bana, ƴan bindigar sun nemi a ƙara masu makamancin wannan kudi, jimilla N56m kenan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com