Gobara Ta Yi Barna a Tashar Lantarki, An Samu Matsalar Wuta a Yankuna 6
- Mummunar gobara ta tashi a tashar wutar lantarki ta Egbin da ke Legas, wadda ta janyo lalacewar na'ura mai karfin 150MVA
- Kamfanin TCN ya rahoto cewa gobarar ta tashi ne a kan layin wuta na 33kV CT/VT, inda ya kama da wuta tare da lalata na'urar
- Wannan ya jawo an samu karancin wuta a yankuna kusan shida na Legas, yayin da TCN ya ce yana kokarin kawo sabuwar na'ura
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya bayyana cewa gobara da ta tashi a tashar samar da wuta ta Egbin a jihar Legas.
Gobarar ta haifar da cikas mai tsanani a bangaren rarraba wutar lantarki, bayan da daya daga cikin manyan na'urorin wutar, mai karfin 150MVA ta lalace.

Asali: Getty Images
Gobara ta tashi a tashar wutar Egbin
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na safiyar ranar Litinin, 5 ga Agusta, 2025, a tashar wutar lantarki ta Egbin, a cewar sanarwar da aka wallafa a shafin TCN na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta kara da cewa gobarar ta kama wasu layukan wuta na 33kV CT/VT da kamfanin Egbin Power Plc ya girka.
TCN ta ce layin wutar na CT/VT ya kama da wuta kuma hakan ne ya haddasa lalacewar babbar na'urar wuta mai karfin 150MVA da ke dauke da man fetur a cikin tankinta, inda aka samu zubar man fetur sanadiyyar fashewar tankin.
Wutar lantarki ta ragu a yankunan Legas
Sakamakon gobarar, an samu raguwar karfin rarraba wuta zuwa yankuna da dama da suka hada da Ikorodu, Odogunyan, Sagamu Line 1 da 2, da kuma Maryland Line 2 a cikin jihar Lagos.
Wadannan wurare su ne yankunan da kamfanonin IKEDC da IBEDC ke ba su wuta ta hanyar kananun tashoshin wuta masu karfin 132/33kV.
Kamfanin TCN ya bayyana cewa karancin wutar na ci gaba da yin muni, wanda ya tilasta amfani da tsarin karbi-in-karba na wuta a wadannan yankuna.
TCN ya nemi afuwa, ya ce ana kan gyara
TCN ya nemi afuwar jama’a bisa wannan cikas da aka samu, tare da tabbatar da cewa yana kokarin maye gurbin na'urar da ta kone da kuma dawo da wutar yadda ya kamata cikin gaggawa.
“Mun sanar da IKEDC da EKEDC don taimakawa wajen tsara amfani da wutar da ake iya samarwa yanzu. A halin yanzu, muna kan hanya wajen samo sabuwar na’urar da za ta dauki kaya masu nauyi,” inji sanarwar TCN.
Kamfanin TCN ya kara da cewa irin wannan gobara na yawan faruwa ne sakamakon lodi da ke yi wa na'ura yawa da kuma matsaloli na amfani da kayayyaki daga kamfanonin da ba a saba amfani da su ba.
Tashar wutar lantarkin Najeriya ta lalace
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tashar wutar lantarki ta kasa ta fuskanci matsala, lamarin da ya haddasa katsewar wuta, musamman a jihar Legas.
Gwamnati tana murnar kai wutar lantarki zuwa 6,000MW, amma rahotanni sun nuna cewa samar da wutar ya ragu zuwa kasa da 1,000MW.
A zantawarmu da wani matashi, Gaddafi Musa, ya ba 'yan Najeriya shawarar komawa amfani da 'solar' domin samun wutar lantarki daga hasken rana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng