Sojojin Najeriya Sun Fafata da Ƴan Bindiga, An Cafke Wani Baƙon Ɗan Ta'adda a Yobe

Sojojin Najeriya Sun Fafata da Ƴan Bindiga, An Cafke Wani Baƙon Ɗan Ta'adda a Yobe

  • Sojojin Operation Hadin Kai sun kama wani da ake zargi ɗan ta’addan Nijar ne a jihar Yobe tare da kashe wasu ‘yan bindiga da dama
  • A jihar Borno, iyalan ‘yan ta’adda biyu sun mika wuya ga sojoji, yayin da aka kashe ‘yan bindiga biyu a Sokoto, kuma aka kwato bindigogi
  • A Ondo, sojoji sun kama masu safarar makamai, sannan kuma bankado maboyar IPOB a jihar Delta tare da kama mutane bakwai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Yobe - Dakarun Operation Hadin Kai, a ranar Litinin, sun cafke wani da ake zargin ɗan ta’adda ne daga ƙasar Nijar yayin da yake ƙoƙarin shiga kwaryar Yobe.

Sojojin sun kuma kashe ‘yan ta’adda da dama, sun kama wasu, tare da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su a wasu hare-hare daban-daban.

Kara karanta wannan

Fitinannen uban daba a Kano, Barga ya faɗa komar ƴan sanda

Dakarun sojojin Operation Hadin Kai sun cafke wani da ake zargin dan ta'adda ne daga Nijar a jihar Yobe
Dakarun sojojin Najeriya sun yi sahu sahu, wasu a kan babura, da shirin fita kai samame. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

An cafke wani da ake zargin dan ta'adda ne

Wata majiya mai ƙarfi ta shaida wa Kamfanin NAN cewa wanda ake zargin ya gaza yin magana da kowane irin harshe na Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce wannan ne ya ja hankalin dakarun sojin, inda suka ci gaba da bincike don gano yiwuwar alakarsa da kungiyoyin ta’addanci a Najeriya da ƙasashen waje.

An ruwaito cewa rundunar hadin gwiwa ta bataliya 120 da ke Katarko, ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe ce ta kai samamen, tare da kama wanda ake zargin.

A jihar Borno, majiyar ta bayyana cewa wasu iyalan ‘yan ta’adda biyu; Babbar mata da ƙaramin yaro, sun miƙa wuya da kansu ga sojojin bataliya ta 202 da ke Bama, bayan sun tsere daga yankin Churchur.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Sokoto

Wannan lamarin, a cewar majiyar, alama ce ta matsin lamba da sojojin Najeriya ke ci gaba da yi wa sansanonin ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Cakwakiya: Asirin amarya ya tonu, ƴan sanda sun kama ta watanni bayan ɗaura aurenta

A jihar Sokoto kuwa, sojojin 8 Division Garrison sun kashe ‘yan bindiga biyu a musayar wuta mai zafi da ta auku a kauyukan Tsamaye da Mai Lalle da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni.

Majiyar ta ce an gano bindigogi kirar AK-47 guda uku da babur ɗaya a wurin da aka yi artabun.

A jihar Kebbi, majiyar ta ce sojojin 1 Battalion Rear sun dakile yunkurin sace shanu a kauyen Sauna da ke ƙaramar hukumar Argungu.

Ya ƙara da cewa ‘yan fashin sun tsere da suka ji luguden wuta tare da barin shanu 251 da suka sata, wadanda daga bisani aka mayar da su ga masu su.

Sojojin Najeriya sun gudanar da ayyuka a Zamfara, Sokoto, Delta da Ondo
Wasu sojojin Najeriya suna tattaunawa karkashin bishiya a wani kauye. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Ayyukan sojoji a jihohin Ondo da Delta

A jihar Ondo, majiyar ta bayyana cewa sojojin bataliya ta 323 da suka kware a manyan makamai (AR) da ke aiki a Igbara-Oke, ƙaramar hukumar Ifedore, sun kama wasu da ake zargin masu safarar bindigogi ne yayin da suke ƙoƙarin sayen makamai.

A cewar majiyar, mutanen da aka kama suna aiki ne da umarnin wani da ke gidan yari na Kirikiri a Lagos, wanda ake zargin yana da hannu wajen tsara cinikin makaman don tallafa wa aikata laifuka a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Rigiji gabji: 'Yan sanda sun kama sojoji a wajen da ba a tsammani

Jaridar The Punch ta rahoto majiyar ta shaida cewa:

“A wani samame da aka kai a jihar Delta, sojoji sun gano adaidaita sahu da aka cika da man dizal fiye da lita 200 da ake zargin an tace shi ba bisa ƙa’ida ba, a hanyar Jeddo–Omadino da ke ƙaramar hukumar Warri ta Kudu."

Majiyar ta jaddada cewa rundunar sojin Najeriya tana ci gaba da kara kaimi wajen yakar 'yan ta'adda a sassa daban daban na kasar nan.

Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojoji sun dakile wani hari da ‘yan ta’adda suka kitsa kai wa jihar Neja, inda suka hallaka miyagu da dama a fafatawar.

Sojoji sun sha gaban 'yan ta'addar ne bisa sahihan bayanan sirri da aka tattara, tare da goyon bayan rundunar sojin sama, inda aka kwato bindigu da sauran makamai.

Sai dai, duk da wannan nasarar, wani soja daga cikin dakarun ya rasa ransa a yayin artabun, yayinda rundunar ta tabbatar da kudirinta na ci gaba da yaki da ta’addanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com