Za a Caɓa: Gwamnatin Tinubu Ta Fara Ɗiban Matasa Aiki domin Rage Zaman Banza

Za a Caɓa: Gwamnatin Tinubu Ta Fara Ɗiban Matasa Aiki domin Rage Zaman Banza

  • Gwamnatin Tarayya ta fara rajista mataki na biyu na shirin RHEI don rage rashin aikin yi da koyar da matasa sabbin dabaru
  • Darakta-Janar na NDE, Silas Agara, ya ce rajistar za ta gudana ta yanar gizo daga 28 ga Yuli zuwa 11 ga watan Agustan 2025
  • Za a koyar da fiye da sana’o’i 30 na zamani da na hannu bisa bukatun kowace jiha, domin habaka damarmaki a cikin gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Hukumar Kula da Ayyuka ta Kasa (NDE) ta kaddamar da rajistar mataki na biyu domin rage yawan rashin ayyukan yi.

Hakan na daga cikin shirin 'Renewed Hope Employment Initiative' (RHEI) da gwamnatin Bola Tinubu ta fito da su.

Gwamnatin Tinubu ta fara daukar matasa aiki
Gwamnatin Tinunu ta bude yanar gizo domin ɗiban matasa aiki. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: UGC

An fara diban matasa aiki a gwamnatin Tinubu

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da kashe sama da N712bn a yi wa filin jirgin Legas kwaskwarima

Mr. Silas Agara, Darakta Janar na NDE, ya sanar da hakan yayin kaddamar da sabuwar dandali ta yanar gizo a ranar Litinin a Abuja, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa dandalin na zamani zai taimaka wajen aiwatar da shirin cikin gaskiya da adalci ga kowa da kowa.

Ya ce:

“Bayan nasarar mataki na farko, mun inganta tsarinmu domin mataki na biyu ya zama cikakke ta yanar gizo.
“Muna da na'urori na zamani, kayan aiki da sadarwa a jihohi 37 da Abuja domin tabbatar da saukin gudanarwa."

NDE: Tsare-tsaren da ake bi domin neman aikin

Agara ya bayyana cewa rajistar na bukatar NIN da zama a kowace jiha, ba tare da la’akari da asalin jiha ba domin rage aikin yi a tsakanin matasa.

“Masu nema dole ne su kasance daga shekara 18 zuwa 45 kuma za su samu horo a fiye da sana’o’i 30.
“Horarwar ta bambanta daga jiha zuwa jiha. Abin da ya dace a Abia na iya bambanta da Adamawa.

Kara karanta wannan

Abin da DSS suka yi wa ɗan TikTok da ake zargin ya ce Tinubu ya mutu sanadin guba

- Silas Agara

Za a samarwa matasa aikin yi a Najeriya
Gwamnatin Tinubu za ta samarwa matasa aikin yi. Hoto: UGC.
Asali: UGC

Yaushe aka bude dandalin domin diban matasa aiki?

Dandalin rajista (www.nderegistrationportal.ng) zai kasance a bude daga ranar 28 ga Yuli zuwa 11 ga Agusta, 2025.

Za a fara tantance aikace-aikace daga 12 zuwa 22 ga Agustan 2025, Agara ya ce ba za a kara lokaci ba, rahoton Punch ya ruwaito.

Ya gargadi jama’a da su guji yaudara, yana mai cewa su bi hanyoyin da hukumar NDE ta ware kawai.

Ya kara da cewa:

“Ba a bukatar kudi domin shiga shirin, A kai rahoton duk wani shiri da ba a yarda da ita ba ga ofishinmu na jiha ko na kasa, mun kafa cibiyoyin aikin yi a dukkan jihohi 37 har da Abuja."

Legit Hausa ta tattauna da wani matashi

Umar Abubakar wanda ya yi rijista da hukumar NDE fiye da shekaru biyu ya koka kan lamarin .

Ya ce:

"Ina tsammanin na fi shekaru 3 da cika wasu sana'o'i da aka bude a hukumar NDE har yanzu shiru.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Kamfanin NNPCL ya yi magama kan sayar da matatar Port Harcoirt

"Idan har za a rika daukar lokaci mai tsawo babu wani tasiri da hakan zai yi ga matasa."

Umar ya shawarci gwamnati ta tabbatar da aiwatar da shirin da wuri domin amfanin matasa.

Matasa miliyan 1 za su samu aikin yi

A baya, kun ji cewa Gwamna Hyacinth Alia ya ce jihar Benue za ta taimaka wa Najeriya ta zama jagaba a fitar da waken suya zuwa kasashen duniya.

Sabon shirin ƙara samar da waken suya zai samar da aikin yi miliyan 1 tare da Naira tiriliyan 3.9 na kudin shiga ga jihar da kasa baki daya.

An gabatar da shirin ne a wani taron na musamman da aka yi a Abuja, kuma manyan jami'an gwamnati da kamfanoni sun halarta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.