Fatima Alkali Ta Ki Karbar Mukamin da Tinubu Ya ba Ta, Majalisa Za Ta Tantance Farfesa Yusuf
- Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Farfesa Yusuf Muhammad Yusuf a matsayin kwamishinan NLRC domin maye gurbin Fatima Alkali
- Tinubu ya aike da wasiƙa zuwa majalisar dattawa, inda ya bukaci a tabbatar da nadin Yusuf bisa tanadin dokar NLRC ta shekarar 2022
- Kwamitin shari’a na majalisa ya ce Fatima Alkali ta ƙi gabatar a kanta don tantancewa, inda ya ba da shawarar a nemo madadinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Yusuf Muhammad Yusuf a matsayin kwamishinan Hukumar Sauya Dokoki ta Najeriya (NLRC).
Nadin Farfesa Yusuf Yusuf ya biyo bayan ƙin amincewar da Fatima Alkali ta yi da tayin da shugaban kasar ya yi mata a watan jiya.

Source: Twitter
Tinubu ya gabatar da sunan Yusuf ga majalisa
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar shugaban ƙasa a zaman majalisar na ranar Laraba, inji rahoton The Punch.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare, majalisa ta amince Tinubu ya kinkimo bashin Naira tiriliyan 32.2
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Godswill Akpabio ya sanar da sauyin sunan da kuma bukatar da Tinubu ya gabatar na gaggauta tabbatar da tantance Yusuf.
A cikin wasikar, Shugaba Tinubu ya ce:
“Na rubuto wannan wasiƙa ne domin neman amincewar majalisa a kan naɗin kwamishinan Hukumar Sauya Dokoki ta Najeriya, bisa tanadin sashe na 2(1) na dokar NLRC ta shekarar 2022.
“Na naɗa Farfesa Yusuf Muhammad Yusuf kuma ina fatan majalisar dattawa za ta tabbatar da nadinsa a matsayin kwamishinan hukumar NLRC."
Wasikar da Tinubu ya aikawa majalisar dattawa
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa an naɗa Farfesa Yusuf ne domin ya maye gurbin Farfesa Fatima Alkali, wadda ta ƙi gabatar da kanta ga majalisar domin tantancewa bayan naɗinta a watan Yuni.
“Mai girma shugaban majalisa da sanatoci masu daraja, an naɗa Farfesa Yusuf Muhammad Yusuf domin maye gurbin Farfesa Fatima Alkali, wadda na gabatar da sunanta a wasiƙata ta 22 ga Yunin 2025, amma ta ƙi bayyana don tantancewa da tabbatarwa.
“Yayin da nake fatan majalisa za ta yi la’akari da kuma gaggauta tabbatar da nadin Farfesa Yusuf, da fatan za ku karɓi tabbacin girmamawa ta mafi ƙololuwa.”
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
The Cable ta rahoto cewa Akpabio ya mika sunan Yusuf zuwa kwamitin majalisa mai kula da shari’a, haƙƙin ɗan adam da kuma lamuran doka domin ci gaba da aikin tantanewar.

Source: Facebook
Fatima Alkali ta ki karbar mukamin NLRC
A watan Yunin 2025 ne Tinubu ya naɗa Farfesa Dakas Dakas a matsayin shugaban NLRC, tare da Uchenna Okolocha da Fatima Alkali a matsayin kwamishinoni.
Sai dai yayin gabatar da rahoton tantancewar, shugaban kwamitin shari’a na majalisa, Sanata Adeniyi Adegbonmire, ya sanar da sanatocin cewa Fatima Alkali, wadda za ta wakilci yankin Arewa maso Gabas, ta ƙi karɓar nadin.
“A ranar Laraba, 25 ga Yuni, 2025, mutum biyu daga cikin su sun bayyana a gaban kwamitin, amma ta uku wato Farfesa Fatima Alkali, ta ƙi karɓar tayin mukamin.”
Sanata Adegbonmire ya ƙara da cewa kwamitin ya bada shawarar a maye gurbin Farfesa Fatima Alkali da wata mace daga Arewa maso Gabas domin tabbatar da daidaito tsakanin jinsi.
Tinubu ya nada 'dan IBB shugaban BoA
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Muhammad Babangida a matsayin shugaban hukumar bankin noma (BoA) bayan an farfado da shi.
Muhammad Babangida, ɗan tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Babangida, ya samu ƙwarewa daga jami’o’i a Turai da kuma makarantar kasuwanci ta Harvard.
A cikin sababbin nade-naden gwamnati, mutane takwas daga sassa daban-daban na ƙasa sun samu manyan mukamai don bunƙasa shugabanci da inganta aikace-aikace a hukumomi.
Asali: Legit.ng

