Ranar mata ta duniya: Fadar shugaban ƙasa ta lissafa mata 50 da ke riƙe da madafan iko a gwamnatin Buhari

Ranar mata ta duniya: Fadar shugaban ƙasa ta lissafa mata 50 da ke riƙe da madafan iko a gwamnatin Buhari

Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi ta saki sunayen mata da ta yi wa lakabi da 'matan Buhari' a cikin shagulgulan bikin ranar mata na kasa da kasa, wato International Women’s Day, IWD.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa a kowanne ranar 8 ga watan Maris na shekara ne ake bikin na IWD. Maudu'in ranar matar ta 2021 shine 'Choose ta Challenge'.

Ranar mata ta duniya: Fadar shugaban ƙasa ta fitar da sunayen mata 50 da Buhari ya naɗa muƙami
Ranar mata ta duniya: Fadar shugaban ƙasa ta fitar da sunayen mata 50 da Buhari ya naɗa muƙami. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

A sanarwar da kakakin Buhari, Femi Adesina ya fitar a Abuja, ya lissafa mata 50 cikin matan Nigeria da suke rike da madafan iko a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: BUK ta fara karatun digiri a sabbin kwasa-kwasai 8

A cewar hadimin shugaban kasar, bikin ya bada damar a yi duba kan yadda gwamnatin Buhari ke karama mata.

Ya ce: "Ga jerin sunayen, 'Matan Buhari', kadan daga cikinsu:

1. Zainab Ahmed, Ministan Kudi, Kasafin Kudi da Tsarin Kasa

2. Sadiya Umar Farouq, Ministan Harkokin Agaji da Jin Kai

3. Pauline Tallen, Ministan Harkokin Mata

4. Mariam Yalwaji Katagum, Karamar ministan Masana'antu, Cinikayya da Saka Hannun Jari

5. Sharon Ikeazor, Karamar Ministan Muhalli

6. Gbemisola Saraki, Karamar Ministan Sufuri

7. Ramatu Tijjani Aliyu, Karamar Ministan Abuja (FCT)

8. Folashade Yemi-Esan, Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya

9. Mariam Uwais, Mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa

10. Jumoke Oduwole, Mashawarciyar shugaban kasa ta musamman kan masana'antu, cinikyaya da saka hannun jari, kuma sakatariyar cibiyar saukaka yin kasuwanci ta shugaban kasa PEBEC.

11. Mojisola Adeyeye, Shugaban hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna, NAFDAC.

12. Hadiza Bala-Usman, Shugaban hukumar tashohin jiragen ruwa na Nigeria, NPA.

13. Abike Dabiri–Erewa, Shugaban hukumar yan Nigeria mazauna kasashen ketare

14. Chioma Ejikeme, Babban sakatariya na hukumar fansho ta PTAD

15. Patience Oniha, Direka janar na Ofishin Kula da Basusuka na Kasa

16. Aisha Dahir-Umar, Shugaban hukumar fansho ta kasa

17. Jummai A.M. Audi, Shugaban hukumar yi wa dokoki garambawul, (NLRC)

18. Yewande Sadiku, Sakataren hukumar inganta saka hannun jari Executive Secretary, (NIPC)

19. Gloria Akobundu, Shugaban hukumar hadin gwiwa don cigaban Afirka (NEPAD)

20. Nnenna Akajemeli, Shugaban hukumar sauraron korafin abokan hulda, SERVICOM

21. Folashade Joseph, Shugaban Hukumar Inshora na Noma, (NAIC)

22. Cecilia Gaya, Shugaban kwallejin horar da masu tafiyar da mulki, (ASCON)

23. Ronke Sokefun, Shugaban hukumar inshora ta NDIC

24. Aishah Ahmad, Mataimakiyar gwamnan babban bankin duniya, (CBN)

25. Stella Ojekwe-Onyejeli, Shugaban Nigeria Sovereign Investment Authority (NSIA)

26. Adejoke Orelope-Adefulire, Babban mataimakiyar shugaban kasa na musamman kan Sustainable Development Goals (SDGs)

27. Oge Modie, Babban mataimakiyar shugaban kasa na musamman kan sadarwa na musamman

28. Moji Rhodes. Babban mataimakiyar shugaban kasa na musamman kan harkokin cigaba da jin kai

29. Toyin Adeniji, Shugaban Kananan Kamfanoni da Bankin Masana'antu, (Oversees the Government Enterprise and Empowerment Programme, GEEP)

30. Stella Okotete, Shugaban bankin cigaban kasuwanci, NEXIM Bank

31. Omolola Abiola, Edewor, Shugaban Deposit Insurance Corporation (NDIC)

32. Imaan Sulaiman-Ibrahim, Shugaban hukumar yaki da fataucin mutane (NAPTIP)

33.Lauretta Onochie, Mataimakiyar shugaban kasa a dandalin sada zumunta kuma zababbiyar kwamishina na INEC

34.Dr. Yosola Akinbi – Babban mashawarciya kan tattalin arziki na kasa (NEC) (Ofishin mataimakin shugaban kasa)

35.Dr. Balikisu Saidu, Babban mataimakiya na musamman kan harkokin shari'a, bincike da ka'idoji, (OVP)

36.Prof. Fatima Waziri-Azi – Babban mataimakiya na musamman, bangaren bin ka'idoji (ofishin mataimakin shugaban kasa)

37. Foluso Idumu, Babban mataimakiya na musamman, bangaren gudanar da mulki (ofishin mataimakin shugaban kasa)

38.Lanre Shasore, Babban mataimakiya na musamman fanin tsare-tsare (ofishin mataimakin shugaban kasa)

DUBA WANNAN: Wike: Ni nayi addu'a kada a samu tsaro a Nigeria saboda abinda Buhari ya yi wa Rivers a 2016

39.Dr Ebi Awosika, Babban mataimakiya na musamman bangaren tuntubar jama'a (ofishin mataimakin shugaban kasa)

40.Olaolu Beckley, Babban mataimakiya na musamman, ajiye bayanai (ofishin mataimakin shugaban kasa)

41.Edewede Akhidenor, Babban mataimakiya na musamman, bangaren gudanar da mulki (ofishin mataimakin shugaban kasa)

42.Nkoli Anyaoka, Babban mataimakiya na musamman, bangaren gudanar da mulki (ofishin mataimakin shugaban kasa)

43.Dr. Lilian Idiaghe, mataimakiya na musamman, Shari'a (ofishin mataimakin shugaban kasa)

44.Tolani Alli, mataimakiya na musamman, isar da rubutattun sakonni (ofishin mataimakin shugaban kasa)

45.Toyosi Onalapo, mataimakiya na musamman tuntubar jama'a

46.Haijya Halima Bawa, mataimakiya na musamman tuntubar jama'a

47.Nonye Ojekwe, mataimakiya na musamman tuntubar jama'a

48.Koko Iyamusa, mataimakiya na musamman, bangaren gudanarwa (Ofishin mataimakiyar shugaban kasa)

49.Fakorede Omotayo Basirat, mataimakiya na musamman kan ayyuka na musamman

50.Omotayo Rachael Omowunm, mataimakiya na musamman kan harkokin gida da bukukuwa

A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel