Buhari ya nada Jummai Audi a matsayin shugabar hukumar NLRC, Mohammed Ibraheem a matsayin kwamishina
- Shugaba Buhari ya aika wasiku zuwa majalisar dattijai a ranar Talata
- A cikin dukkan wasikun, shugaba Buhari ya bukaci majalisar ta amice tare da tabbatar na nadin mutanen da ya bawa mukamai
- A ranar Litinin ne shugaba Buhari ya nada Mohammed Shehu a matsayin babban sakataren hukumar kasafin kudin haraji (RMAFC)
Majalisar dattijai ta tabbatar da samun wasikar shugaban kasa, Muhammad Buhari, a kan neman amincewa da nadin Jumai Audi a matsayin shugabar hukumar NLRC (Nigerian Law Reform Commission).
Kazalika, shugaba Buhari ya nemi majalisar ta amince na nadin Ebele Chima, Bassey Abia, da Mohammed Ibraheem a matsayin kwamishinoni da zasu wakilcin yankunan da suka fito a hukumar NLRC.
A wata wasikar da Buhari ya aikawa majalisar, ya nemi amincewarta da Diana Okonta (daga kudu maso kudu), Ya'ana Yaro (daga arewa maso gabas) a matsayin darektoci a hukumar NDIC (Nigeria Deposit Insurance Corporation).
Yahaya Abdullahi, barden majalisar dattijai, ya bukaci majalisar ta gaggauta amincewa da tabbatar da sunayen dukkan mutanen da shugaba Buhari ya aiko.
A ranar Litinin ne Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin Mohammed Bello Shehu, a matsayin sakataren hukumar kasafin kudaden haraji da gwamnatin tarayya ta samu.
Shehu, wanda nadinsa ya fara aiki a ranar 19 ga watan Maris, zai shafe zangon farko mai wa'adin shekaru biyar a hukumar RMAFC tare da zabin sabunta nadinsa a zango na biyu idan shugaban kasa ya ga dama.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Willie Bassey, darektan yada labarai a ofishin sakataren gwamnatin tarayya. Sanarwar ta fito ne da yammacin ranar Litinin.
DUBA WANNAN: Amurka ta amince da bukatar FG ta bincken asusun Jonathan, Dame Patience, Diezani, Lukman da sauransu
A cewar sanarwar, shugaba Buhari ya sake amincewa da nadin Bitrus Danharbi Chinoko a matsayin babban darektan CMD (Centre for Management Development) Lagos.
Nadinsa zai fara aiki daga ranar 27 ga watan Afrilu.
Kafin nadinsa a matsayin babban darekta mai cikakken iko, Mista Chinoko ya kasance mukaddashin babban darektan CMD.
"Shugaba Buhari ya tayasu murna tare da bukatar su yi amfani da kwarewarsu domin kawo sauye - sauye masu amfani da muhimmanci a hukumomin da zasu jagoranta," a cewar sanarwar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng