A Karon farko, Jingir Ya Yi Baram Baram da Gwamnan Plateau kan Tsaro, Ya Kawo Mafita
- Shugaban kungiyar Izalah ta JIBWIS, Sheikh Sani Jingir, ya yi magana game da shawarar dauke sojoji a jihar Plateau
- Jingir ya soki kudirin janye sojoji daga wuraren rikici a jihar, yana cewa hakan barazana ne ga rayukar Bayin Allah
- Gwamnatin Plateau ta bukaci janye dakarun bayan harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 27, tana cewa sojojin sun kasa dakile farmaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Shugaban kungiyar Izalah ta JIBWIS, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya gargadi hukumomi kan dauke sojoji a Plateau.
Jingir ya yi gargadin cewa kiran da ake yi na janye sojoji daga wuraren rikici a jihar Plateau barazana ne ga rayuka da dukiyoyi.

Source: Facebook
Sheikh Jingir ya soki shawarar gwamnan Plateau
Malamin Musuluncin ya bayyana matsayinsa ne a yayin taron manema labarai a Jos ranar Talata, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Jingir ya bukaci hukumomin da abin ya shafa su yi watsi da wannan kira domin kare rayukan mutane.
Gargadin Sheikh Jingir na zuwa ne bayan bukatar da gwamnatin jihar Plateau ta gabatar na cewa a janye dakarun sojoji daga wuraren da ake rikici a jihar.
Bukatar gwamnatin Plateau game da dauke sojoji
Majiyoyi sun ce wakilin musamman kan zaman lafiya da tsaro ga Gwamna Caleb Mutfwang, Farfesa Chris Kwaja, ya nemi gwamnati ta maye gurbin sojoji da ‘yan sandan (Mopol).
Gwamnatin jihar ta bukaci hakan ne kwanaki biyu bayan harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 27 a yankin Tahoss na karamar hukumar Riyom.
Sheikh Jingir ya ce:
“Ba mu goyi bayan kiran da ake yi na janye sojoji daga wuraren rikici ba. Wannan ba zai amfanar da al'umma ba.”

Source: Twitter
Sheikh Jingir ya yabawa kokarin sojoji a Plateau
Sheikh Jingir ya kara da cewa tun lokacin da rikice-rikicen suka barke a jihar, sojoji na bakin kokarinsu wajen dawo da zaman lafiya da doka da oda.

Kara karanta wannan
Batan maciji ya birkita ƴan Kano, Sanusi II ya roƙi kwamishinan ƴan sanda alfarma
“Shekaru da dama kenan muna da kwarin gwiwa ga duka hukumomin tsaro na tarayya, ciki har da ’yan sanda.
“Ba mu goyi bayan cire sojoji ko ’yan sanda ba. Maimakon haka, muna maraba da hadin gwiwar dukkan hukumomin tsaro, kamar OPSH.
“Muna yaba wa gwamnatin tarayya da shugabannin tsaro bisa ci gaba da wannan aiki. Aikin na dauke da jami’an tsaro daga kowane yanki.”
- Cewar Sheikh Jingir
Sheikh Jingir ya bukaci daukacin al’ummar jihar Plateau da su zauna lafiya da juna ba tare da la’akari da banbancin kabila ko addini ba.
Sheikh Jingir ya yabawa Gwamna Mutfwang
Mun ba ku labarin cewa shugaban Izalar Jos, Sani Yahaya Jingir ya yabawa gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang bisa kokarin da yake a muhimman ɓangarori uku.
Sheikh Jingir ya ce gwamnan yana matuƙar kokari wajen samar da zaman lafiya, haɗin kai da kuma gudanar da mulkin adalci a Plateau da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Malamin ya yi wannan yabon ne da Gwamna Mutfwang ya kai maza ziyarar ta'aziyya bisa rasuwar Sheikh Sa'eed Hassan Jingir wanda ya kasance aminin Jingir.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
