Tinubu Ya Ɗauko Ɗan IBB da Wasu Ƴan Arewa 7, Ya ba Su Manyan Muƙaman Gwamnati

Tinubu Ya Ɗauko Ɗan IBB da Wasu Ƴan Arewa 7, Ya ba Su Manyan Muƙaman Gwamnati

  • Bola Tinubu ya naɗa Muhammad Babangida shugaban Bankin Noma, wanda aka farfaɗo da shi domin ƙarfafa tattalin arzikin gona da raya karkara
  • Babangida, ɗan tsohon shugaban soja, Ibrahim Babangida, ya na da ilimi mai zurfi daga jami’ar Turai da makarantar kasuwanci ta Harvard
  • A jerin sababbin naɗe-naɗen, mutane takwas daga jihohi daban-daban sun samu mukamai a hukumomin gwamnati don ƙarfafa shugabanci da inganta ayyuka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Muhammad Babangida, ɗan tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Babangida muhimmin nadi.

An rahoto cewa Shugaba Tinubu ya nada Muhammad Babangida a matsayin sabon shugaban hukumar Bankin Noma (BoA) da aka sake farfaɗo da shi.

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Muhammad Babangida, dan IBB da wasu mutum 8
Tinubu ya naɗa ɗan IBB, Muhammad Babangida matsayin shugaban hukumar BoA. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu ya nada dan IBB shugaban BoA

Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da gwamnan da ya sauya sheƙa zuwa APC, an samu bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar Onanuga ta ce:

"Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Muhammad Babangida, ɗan tsohon shugaban mulkin soja, a matsayin shugaban Bankin Noma da aka farfaɗo da shi.
"Shugaba Tinubu ya amince da wannan naɗin a yau, tare da wasu mutane takwas. Wasu daga cikinsu za su yi aiki a matsayin shugabanni ko manyan daraktoci na hukumomin gwamnatin tarayya."

Takaitaccen bayani kan Muhammad Babangida

Wannan naɗin dai na ɗaya daga cikin naɗe-naɗe takwas da Shugaba Tinubu ya amince da su, wanda ya haɗa da shugabannin wasu hukumomin gwamnatin tarayya.

Muhammad Babangida, mai shekaru 53, yana da digiri a fannin kasuwanci da kuma digiri na biyu a fannin hulɗar jama'a da sadarwa ta kasuwanci (PRBC) daga Jami'ar Turai da ke Montreux, Switzerland.

Har ila yau, ɗan IBB ya kammala shirin horo a kan ayyukan gudanar da sha'anin gwamnati a makarantar kasuwanci ta Harvard a shekarar 2002.

Shugaba Tinubu ya karrama IBB, ya dauko dansa ya ba shi mukamin gwamnati
Shugaba Bola Tinubu ya rusuna, yana musabaha da Ibrahim Badamasi Babangida, IBB. Hoto: @PBATMediaCentre
Source: Twitter

Sauran naɗe-naɗen Tinubu a hukumomin tarayya

Kara karanta wannan

Hoton yadda Aisha Buhari ta rungume tutar da aka lulluɓo gawar mijinta ya ja hankali

Sanarwar ta kuma bayyana naɗin wasu fitattun mutane zuwa muƙaman shugabanci a hukumomin tarayya daban-daban, kamar haka:

  1. Lydia Kalat Musa (Kaduna): Shugabar hukumar OGFZA.
  2. Jamilu Wada Aliyu (Kano): Shugaban hukumar NERDC.
  3. Hon. Yahuza Ado Inuwa (Kano): Shugaban hukumar SON.
  4. Sanusi Musa (SAN) (Kano): Shugaban Cibiyar IPCR.
  5. Prof. Al-Mustapha Alhaji Aliyu (Sokoto): Darakta Janar na hukumar DTCA.
  6. Sanusi Garba Rikiji (Zamfara): Darakta Janar na hukumar NOTN
  7. Mrs Tomi Somefun (Oyo) Manajan Darakta ta hukumar (HYPPADEC).
  8. Dr Abdulmumini Mohammed Aminu-Zaria (Kaduna) Babban Darakta na hukumar NIWRMC.

Waɗannan naɗe-naɗe sun zo ne a daidai lokacin da ake kira da a sake fasalin da inganta ayyukan hukumomin gwamnati, musamman waɗanda ke da alaƙa da ci gaban tattalin arziki, kasuwanci, da sarrafa albarkatu.

Ana sa ran sababbin jami'an da aka naɗa za su kawo sabon tsarin shugabanci mai cike da ƙarfin gwiwa da kawo ci gaba ga cibiyoyinsu daban-daban.

IBB ya nemi yafiyar iyalan MKO Abiola

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Lekan Abiola, ɗan marigayi MKO Abiola, ya ce tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida, ya nemi gafarar iyalan Abiola bisa soke zaben 1993.

Kara karanta wannan

Ficewa daga PDP: Hadimin Atiku ya yi wa ministan Tinubu wankin babban bargo

Yayin da yake ganawa da ’yan jarida, Lekan ya ce IBB ya yi wannan roƙon gafara ne a ɓoye, yana mai bayyana cewa hakan ya nuna Babangida ya gane kuskurensa.

A cewarsa, iyalansu sun karɓi wannan mataki da farin ciki, ganin yadda Babangida ya nuna ƙwarin gwiwa wajen bayyana kuskuren da ya aikata shekaru da suka gabata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com