Da dumi-dumi: Tawagar motocin ‘dan IBB sun yi hatsari, wasu sun rasa ransu
- Mohammed Babangida, yaron tsohon Shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota
- Mummunan al’amarin da ya faru a ranar Litinin, 31 ga watan Mayu, ya lakume rayukan akalla jami'an tsaro uku wadanda ke cikin ayarin Mohammed
- Motar da ke dauke da jami’an wadanda dukkansu sojoji ne, ta yi karo da tirela kan hanyar Minna zuwa Abuja a Neja
Akalla sojoji uku da ke tare da Mohammed Babangida, dan tsohon shugaban sojojin Najeriya, Ibrahim Babangida, ne suka mutu a wani hatsarin mota akan hanyar Minna zuwa Abuja.
A cewar jaridar Leadership, an bayyana jami'an tsaron a matsayin, Afolabi, Tanko, da Jibril.
KU KARANTA KUMA: Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki
Hakan ya faru ne bayan daya daga cikin motocin da ke cikin jerin gwanon ta yi karo da tirela dauke da kayan lambu a ranar Litinin, 31 ga Mayu.
Mohammed Babangida, wanda ya tsallake rijiya da baya, yana cikin motar bas tare da wasu dangi a bayan motar da abin ya shafa, jaridar The Sun ma ta ruwaito.
Daya daga cikin sojojin da suka samu munanan raunuka sakamakon hatsarin a yanzu yana karbar kulawa a asibitin kasa da ke Abuja.
KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun nemi a biya kudin fansa naira Miliyan 50 domin sakin wadanda aka sace a Neja
Wani dan gidan da ya yi magana kan matsayin Babangida game da ibtila'in ya ce:
“Lamarin ya taba Mai girma kwarai da gaske, yana iya cikawa da duk wanda ke cikin wannan ayarin, tuni an binne su.”
A wani labarin, 'Yan bindiga da suka sace daliban makarantar Salihu Tanko Islamiyya da ke garin Tegina a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja sun tuntubi shugabannin makarantar.
'Yan bindigan sun tuntubi shugaban makarantar, Alhaji Abubakar Alhassan, da misalin karfe 4 na yamma a ranar Litinin, inda suka nemi ya biya N110m a matsayin kudin fansa don sakin daliban.
Da yake magana da manema labarai ta wayar tarho a ranar Talata, Alhassan ya ce 'yan bindigan sun yi ikirarin suna da yara 156 a hannunsu.
Asali: Legit.ng