Rikicin aure: Mun daidaita tsakanina da Muhammad Babangida, 'yar gidan biloniya, Rahma Indimi

Rikicin aure: Mun daidaita tsakanina da Muhammad Babangida, 'yar gidan biloniya, Rahma Indimi

- Diyar fitaccen mai kudi Rahma Indimi ta bayyana cewa ta daidaita da tsohon mijinta

- Ta bayyana hakane bayan wani rubutu da aka yi a kanta a shafukan sadarwa

- Sai dai har yanzu ance akwai sauran rikici dake tsakaninsu a kotu kan yaransu

Rahama Indimi ta bayyana cewa ta daidaita da tsohon mijinta, Muhammed Babangida.

A shekarar 2016, labarai sun yadu cewa auren su da suka shafe shekaru 14 suna tare, tsakanin 'yar gidan fitaccen mai kudin nan Mohammed Indimi, da Muhammed dan gidan tsohon shugaban kasar mulkin soja, Ibrahim Babangida, ya rabu.

Duka su biyun sunyi ta shiga kotu tun lokacin kan rikicin wanda zai rike yaran.

Rikicin aure: Mun daidaita tsakanina da Muhammad Babangida, 'yar gidan biloniya, Rahma Indimi
Rikicin aure: Mun daidaita tsakanina da Muhammad Babangida, 'yar gidan biloniya, Rahma Indimi
Asali: Facebook

Sai dai kuma a lokacin bikin Sallah babba da aka gabatar a watan Yuli, 2020, Rahma taje gidan Ibrahim Babangida, inda 'ya'yanta da kuma 'ya'yan matar tsohon mijinta, Umma, suka dauki hoto da kakansu.

Rahma ta wallafa wannan hoto a shafinta na Instagram, inda wani shafin yada labarai na yanar gizo ya bayyana cewa ta yanke hoton 'ya'yan Umma kafin ta wallafa hoton.

Da take martani akan wannan rubutu, Rahma tayi watsi da zargin, inda kuma ta bayyana cewa ita da tsohon mijin nata tuni sun daidaita.

KU KARANTA: Barayi sun sace mai jego kwana hudu bayan ta haihu a jihar Taraba

"Daga yaya wannan ya zama labari ma kaiiii, za abi kowacce hanya ayi kudi, da farko akwai uku daga cikin 'ya'yana a hoton ba biyu ba, na biyu bani da hurumin da zan wallafa hotunan 'ya'yan matar tsohon mijina, haka kuma Muhammed ya bayyana mini banda sanya hoto a shafukan sadarwa. Ni da Muhammed tuni mun daidaita mun koma zaman lafiya, saboda haka ku daina irin wannan shirmen." cewar rubtun da ta wallafa.

Jaridar Linda Ikeji ta ruwaito cewa tun a shekarar data gabata ne dai Muhammed da Rahma suka daidaita, kuma suna tattaunawa su gani ko zasu koma su cigaba da zaman aure. Duk da dai har yanzu ana kotu kan maganar 'ya'yan nasu, nan da mako biyu za a koma kotu don cigaba da shari'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng