Kai Tsaye: Yadda Jana'izar Muhammadu Buhari ke Gudana a Gidansa na Daura
APC ta sauka a Katsina don ta'aziyyar Buhari
Jam'iyyar APC ta sauka a jihar Katsina domin miƙa sakon ta'aziyya kan rashin tsohon shugaban kasa kuma jigo a cikinta, Muhammadu Buhari.
Wannan na kunshe a cikin wani gajeren saƙo da APC ta wallafa a shafinta na X a yammacin Talata.
Muƙaddashin shugaban APC na ƙasa, Hon. Bukar Dalori da ƴan kwamitin gudanarwar jami'yyar sun isa jihar Katsina.
Dikko Radda ya fashe da kuka wajen birne Buhari
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya gaza rike hawaye yayin da aka ajiye gawar Muhammadu Buhari za a birne ta.
Wani bidiyo da tashar Channels ta wallafa a X ya nuna gwamna Radda na kuka yana zubar da hawaye a cikin jama'a.
A birne shugaba Muhammadu Buhari
Bayan sallar jana'iza da aka yi wa marigayi shugaba Muhammadu Buhari, an birne shi a gidan shi da ke Daura.
Wani rahoto da tashar TVC ta fitar ya nuna yadda shugabannin Najeriya suka taru wajen birne tsohon shugaban kasar.
An kawo gawar Buhari inda za a binne shi
Sojoji sun ɗauko gawar Muhammadu Buhari zuwa inda za a binne shi a cikin gidansa.
Tashar Channels tv ta sanya bidiyon yadda aka ɗauko gawar zuwa kabarin da aka gina, inda a nan ne za a binne tsohon shugaban ƙasan.
An hau sahu don jana'izar Buhari
Mutane sun jeru domin gudanar da sallar jana’izar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Zagazola Makama ya wallafa cewa da zarar an kammala sallatar gawar ne za a birne tsohon shugaban kasar.
Gawar Buhari ta isa gidansa a Daura
Gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta isa gidansa da ke Daura, garinsa na haihuwa a jihar Katsina.
Daily Trust ta ruwaito cewa gawar, da ta tashi daga Birtaniya tun da safiyar Talata, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya karɓe ta a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa da ke Katsina.
Gawar Buhari ta isa Daura
Gawar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ta isa.mahaifarsa Daura a jihat Katsina sa'o'i kaɗan bayan isowa Katsina.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, mataimakinsa, Kashim Shettima, gwamnan Katsina, Dikko Raɗɗa na cikin tawagar da ta yiwa gawar rakiya zuwa Daura.
A yau za a birne Muhammadu Buhari a cikin gidansa da ke Daura, bayan an masa sallar jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada, TVC News ta rahoto.
Bidiyon yadda aka fito da gawar Buhari
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya karbi gawar marigayi Muhammadu Buhari daga wurin tawagar mataimakinsa, Sanata Ƙashim Shettima.
Iyalan Buhari na zubar kwalla da hawayen jimami a lokacin da sojoji ke fito da gawar Buhari daga cikin jirgin sama a filin jirgin Umaru Musa Ƴar'adua.
An tafi da gawar Buhari zuwa Daura
An tafi da gawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zuwa.mahaifarsa da ke Daura.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa an tafi da gawar Buhari ne a mota zuwa garin Daura domin yi masa jana'iza tare da binne shi.
Gawar Buhari ta iso Katsina daga London
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettim ya isa jihar Katsina da gawar shugaba Muhammadu Buhari.
Daga filin jirgin saman Umaru Musa Yar'adua Bola Tinubu zai karbi gawar kafin a wuce da ita Daura.
Shugaba Tinubu ya isa Katsina
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya dura jihar Katsina yayin da ake shirye shiryen tarbar gawar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Bola Tinubu zai karɓi gawar magabacinsa, Muhammadu Buhari kafin wucewa zuwa Daura, inda za a masa jana'iza kuma a birne shi a gidansa yau Talata.
Amaechi ya isa gidan Buhari na Daura
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya isa gidan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da Daura domin halartar jana'izar marihayin.
Amaechi, tsohon gwamnan jihar Ribas ya yi aiki a matsayin minista a gwamnatin Buhari na tsawon shekaru takwas.
Gwamnoni da Ɗangote sun isa Katsina
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, takwaransa na Ogun, Dapo Abiodun da attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Ɗangote sun isa Katsina.
Wannan tawaga ta ina Katsina ne domin halartar jana'izar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a Landan.
Uwargidan Tinubu ta dura Katsina
Mai ɗakin shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu tare da tawagarta sun isa Katsina domin ta'aziyyar rasuwar Muhammadu Buhari.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa da mai ɗakinsa, Hajiya Zulaihat ne suka tarbi Sanata Oluremi Tinubu a filin jirgin sama da ke birnin Katsina.
Mai magana da yawun gwamnan Katsina, Ibrahima Kaulaha Mohammed ne ya tabbatar da hakan a wata sanarws da ya wallafa a Facebook.
Mata sun yi karatun Ƙur'ani da addu'a ga Buhari
Wasu mata sun shirya karatun littafin mai tsarki watau Alƙur'ani tare da addu'o'in Allah Ya gafartawa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura.
Matan waɗanda wataƙila ƴan uwan marigayin ne suka taru a gidansa yayin da ake shirye shiryen zuwa gawarsa domin yi masa suutura.
Uwargidan Tinubu Ta Tafi Abuja Don Jana'izar Buhari
Uwargidan Shugaban Kasan Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta bar Abuja domin halartar jana'izar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Buhari, wanda ya yi ritaya a matsayin Manjo Janar kuma ya jagoranci kasar sau biyu—na farko a matsayin Shugaban Soja a shekarun 1980, sannan kuma a matsayin zababben shugaban kasa daga 2015 zuwa 2023—ya rasu ranar Lahadi a Burtaniya.
Ana sa ran gawarsa za ta isa jihar Katsina yau domin binne shi bisa ga koyarwar addinin Musulunci.
Kalli bidiyon uwargidan shugaban kasar a kasa:
Akpabio ya tafi Daura jana'izar Buhari
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya tashi daga Abuja zuwa Katsina domin jana'izar Muhammadu Buhari.
Wani bidiyo da tashar Arise ta wallafa a X ya nuna cewa Akpabio ya tashi daga Abuja ne tare da wata tawaga ta musamman.
An baza jami'an tsaro a gidan Buhari
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an baza jami'an tsaro a garin Daura da ke jihar Katsina yayin da ake shirin jana'izar Muhammadu Buhari.
Rahoton Daily Trust ya ce ana dakon gawar Buhari zuwa Daura domin jana'izarsa bayan wakilan gwamnatin tarayya sun dauko ta daga London.
Kwamitin Jana'izar Buhari sun dura Katsina
The Cable ta wallafa bidiyon isowar kwamitin shugaban ƙasa na shirya jana'izar girmamawa ga Muhammadu Buhari a jihar Katsina
Tawagar kwamitin wacce ta kunshi ministoci da manya manyan ƙusoshin gwamnati, za ta sa ido kuma ta tsara jana'izar ƙasa ga marigayi Buhari a Baura.
Gawar Buhari ta baro Landan zuwa Daura
Gawar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta baro birnin Landan na Ƙasar Birtaniya a jirgin sama zuwa Daura, Jihar Katsina.
Ana sa ran isowar gawar Buhari da misalin ƙarfe 12:00 na tsakar rana yau Talata domin yi masa jana’izar ƙasa a matsayin girmamawa a mahaifarsa.
Channels tv ta kawo rahoton cewa an ɗauko gawar marigayin shugaban ƙasa ne cikin jirgin saman Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) a safiyar Talata kafin ƙarfe takwas na safe.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, tare da wasu manyan jami’an gwamnati ne suka ɗauko gawar zuwa Najeriya.