Kalaman Buhari 12 da Suka Yi Amo a Najeriya kuma za Su Sa a Rika Tunawa da Shi
Ayyuka da kalaman marigayi Muhammadu Buhari sun kasance ginshiƙai a tarihin Najeriya, daga lokacin soja har zuwa shugabancin dimokuradiyya.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
A ranar Lahadi aka sanar da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a London bayan rashin lafiya.
Shugaba Buhari ya yi wasu kalamai da suka dade suna daukar hankali a Najeriya a tarihin rayuwar shi.

Source: Facebook
A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu daga cikin kalaman da shugaba Buhari ya yi daga lokacin mulkin soja zuwa dimokuradiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Bayanin Buhari kan gyara Najeriya
“’Yan Najeriya na yanzu da ma waɗanda ke zuwa a gaba, ba su da wata ƙasa face Najeriya. Za mu zauna a nan tare, mu gyara ta.”

Source: Twitter
The Cable ta wallafa cewa Buhari ya furta haka ne a jawabi na farko da ya yi a matsayin shugaban soja a Disambar shekarar 1983.
2. Buhari ya goyi bayan shari'a a Najeriya
“Zan ci gaba da nuna cikakken goyon baya ga tsarin Shari’a da ke yaduwa a Najeriya. Da yardar Allah, ba za mu daina fafutukar aiwatar da ita gaba ɗaya ba.”
Punch ta wallafa cewa Buhari ya fadi haka ne a wani taron Majalisar Shari’a ta Kasa a watan Agustan 2001.

Source: Depositphotos
3. Buhari ya nuna adawa da Boko Haram
“Mutanen banza ne, masu kashe jama’a, masu garkuwa da mutane.”
Ya furta wannan kalma ne a lokacin yakin neman zaɓe na 2011, yana bayanin abun da ya dame shi game da Boko Haram.

Source: UGC
4. Maganar Buhari ranar rantsar da shi
“Ni na kowa ne, amma ba (zan nuna son kai) ga kowa ba.”
Ya furta wannar magana ne a lokacin rantsuwar da ya yi a ranar 29 ga Mayu, 2015, a Eagle Square, Abuja. Jawabin ya sanyaya a zukatan mutane.

Source: Facebook
5. Buhari ya yi magana kan cin hanci
“A kan cin hanci, babu rudani kan matsaya ta. Ba za a samu gurbi ga masu almundahana a gwamnatin nan ba.”
Bincike ya nuna cewa marigayi Muhammadu Buhari ya faɗa haka ne lokacin yakin neman zaɓe a shekarar 2015.

Source: Twitter
6. An yi wa Buhari fatan mutuwa
“Mutane da dama sun yi fatan na mutu a lokacin rashin lafiya ta. Wasu ma sun fara rokon mataimakina da ya zabe su mataimakansa.”
Ya furta haka ne Poland, Disamba 2, 2018, yayin magana a kan zargin da ake yi masa kan rashin lafiyar da ya yi.

Source: Facebook
7. Maganar Buhari kan yakin basasa
“Yawancin masu fitintinu a yanzu ba su san bala’in da ya faru a lokacin yakin basasa ba. Mu da muka yi yaki na tsawon wata 30, za mu koya musu hankali.”

Source: Facebook
An rubuta wannan a shafin X a 1 ga Yuni, 2021 yayin tsokacin da ya yi a kan matasa da basu san tarihin yakin ba Biyafara suke tayar da kayar baya, amma an goge rubutun a shafinsa.
8. Matsalar cin hanci a Najeriya
“Cin hanci cuta ce mai lalata gwamnati kuma tana rushe al’umma. Dole ne mu yaƙi hakan da dukkan abin da muke da shi.”
Ya furta wannan a lokacin murnar ranar ’yancin kai, 1 ga Oktoba, 2016. Wannan magana ta zama ginshiƙi ga yakin sa kan cin hanci.

Source: Twitter
9. Magana kan Aisha Buhari
“Ban san jam’iyyar da matata ke ciki ba, ita mai lura min da madafi ne wajen dafa abinci, dakin zama da dakin kwanciya.”
Buhari ya furta wannan a Jamus a Oktoba 2016, a taron manema labarai. Jawabin ya sa mutane dariya sosai.

Source: UGC
10. Buhari ya nemi gafarar 'yan Najeriya
“Ina fatan duk wanda ya ji cewa na cutar da shi, ya yafe min. Mu mutane ne, za mu iya yin kuskure.”
Ya furta wannar maganar ne a fadar shugaban ƙasa, 21 ga Afrilu, 2023, yayin bikin bankwana da tsofaffin jami’an gwamnati.

Source: UGC
11. Magana kan farin cikin 'yan Najeriya
“Zan yi murna sosai idan na ga farin ciki a fuskokin da aljihun ’yan Najeriya.”
Ya furta wannan a taron gabatar da littafi a Nuwamba 16, 2017. Maganar ta bayyana cewa ba shi da sha’awar ɗaukaka, sai son jin dadin mutane ne.

Source: Facebook
12. Buhari ya yi bankwana da mulki
“Zan koma gida Daura bisa gamsuwa da cewa mun kafa tubalin sake gina Najeriya. Ina fatan gwamnati mai zuwa za ta yi sauri wajen cigaba da aikin da muka fara.”
Wannan na cikin jawabin bankwana ne da Muhammadu Buhari ya yi a Abuja, 28 ga Mayu, 2023, a fadar shugaban kasa.

Source: Twitter
Za a yi jana'izar Buhari ranar Talata
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta sanar da cewa a ranar Talata, 15 ga Yuli za a yi jana'izar shugaba Muhammadu Buhari.
Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya bayyana haka yayin da ake tsammanin isowar gawar marigayin a yau Lititin.
Manyan 'yan siyasa da sauran shugabanni ne ake sa ran za su isa Daura da ke jihar Katsina domin yi wa Buhari jana'iza.
Asali: Legit.ng



