Da Ɗuminsa: Shafin Twitter Ya Goge Gargaɗin Da Buhari Ya Yi Wa 'Ƴan IPOB'

Da Ɗuminsa: Shafin Twitter Ya Goge Gargaɗin Da Buhari Ya Yi Wa 'Ƴan IPOB'

- Shafin Twitter ya goge wani sashi na gargadin da Shugaba Buhari ya yi wa masu tada kayan baya

- Buhari ya yi gargadin ne bisa irin hare-hare da kisa da masu tada kayan bayan ke yi musamman a hukumomin gwamnati

- Sai dai mutane da dama sun soko kalaman na Buhari musamman duba da cewa ya ambaci yakin basasar Nigeria

Dandalin sada zumunta na Twitter ya goge wani rubutu da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa inda ya yi barazanar cewa zai bi da wasu yan Nigeria da ke 'tada zaune tsaye' ta 'irin harshen da suke fahimta'.

A sakon da Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, Buhari ya yi magana kan abin da ya faru a lokacin yakin basasa ya kuma yi barazanar 'yin maganin' wadanda ke son ganin bayan Nigeria ta hanyar 'tada kayan baya'.

Da Ɗuminsa: Shafin Twitter Ya Goge Gargaɗin Da Buhari Ya Yi Wa 'Ƴan IPOB'
Da Ɗuminsa: Shafin Twitter Ya Goge Gargaɗin Da Buhari Ya Yi Wa 'Ƴan IPOB'. Hoto: @Mbuhari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe AIG Christpher Dega a Jos

"Irin mu da muka shafe watanni 30 a filin daga, yayin yaki, za mu bi da su ta hanyar da suke fahimta," in ji shi.

Sai dai shafin na Twitter ta goge rubutun a ranar Laraba bayan sukar da aka yi game da rubutun a dandalin sada zumunta.

Twitter ta ce rubutun na Buhari ya saba dokokinta.

A halin yanzu dai ba a san idan shafin zai dauki wani mataki kan shugaban kasar ba bayan hakan.

Buhari ya wallafa rubutun ne yayin da ya ke gargadin 'wadanda ke tada zaune tsaye a wasu sassan kasar' musamman kudu maso gabashin kasar inda ake yawaita kaiwa hukumomin gwamnati hari.

KU KARANTA: An Kashe Sufetan Ƴan Sanda Da Wasu Mutane Shida a Ƙauyen Katsina

Yan Nigeria da dama sun soki kalaman na shugaban kasa, na ambaton yakin basasa - inda miliyoyin yan Nigeria suka rasa rayyukansu mafi yawanci yan kabilar igbo - a matsayin barazanar aikata abubuwan da suka saba hakkin bil adama.

Wasu na kira ga Twitter ta dakatar da shafin na shugaban kasa suna ikirarin ya saba dokokin hukumar.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164