Buhari na neman a kafa kotun yaki da cin hanci da rashawa a Afrika

Buhari na neman a kafa kotun yaki da cin hanci da rashawa a Afrika

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira da a kafa kotun yaki da cin hanci da rashawa a Afrika
  • Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari shine zakaran yaki da cin hanci da rashawa na nahiyar Africa
  • Muhammadu Buhari ya yabawa shugabannin Afirka bisa nasarorin da aka samu akan cin hanci da rashawa a nahiyar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda shi ne zakaran yaki da cin hanci da rashawa na nahiyan Afrika, ya bukaci a kafa wata kotun kasa da kasa da za ta hukunta masu laifi. Rahoton Daily Nigeria

Ya kuma bukaci shugabannin kasashen Afirka da su kara zage damtse wajen yaki da cin hanci da rashawa, tare da samar da karin abubuwan da za su hana satar kudaden jama'a.

Garba Shehu, mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Alhamis a Abuja, ya ce Buhari na magana ne a cikin jawabin da ya rubuta na bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta nahiyar Afrika.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi Da Musulmi Kaddara Ce Daga Allah, Shugaban APC, Adamu

Buhari
Buhari na neman a kafa kotun yaki da cin hanci da rashawa a Afrika : FOTO Daily Nigeria
Asali: Facebook

Shugaban ya yabawa shugabannin Afirka bisa nasarorin da aka samu kawo yanzu, yana mai gargadin cewa dole ne a kara kaimi wajen hukunta masu laifi da kuma dawo da dukiyoyin Afrika da aka ajiye a wasu kasashe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau

A wani labarin, mun ji cewa tsohon dan takarar gwamnan jihar Plateau karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), David Victor Dimka, ya yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu ne zai lashe zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel