An Gano Wani Otel da Ake Safarar 'Yan Mata da Tilasta Su Yin Karuwanci a Katsina

An Gano Wani Otel da Ake Safarar 'Yan Mata da Tilasta Su Yin Karuwanci a Katsina

  • Jami’an NAPTIP a Katsina sun bankaɗo ƙungiyar da ke safarar 'yan mata daga Kudu zuwa Arewa inda ake tilasta su yin karuwanci
  • Hukumar ta ce an ceto mata 3 masu shekaru tsakanin 21 zuwa 26, tare da cafke mutane 3 da manajan wani otal da ake zargi a harkallar
  • Shugabar NAPTIP, Binta Bello, ta yabawa jami’anta tare da bayyana cewa za a gurfanar da otel ɗin bisa taimakawa aikata safarar mutane

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Jami’an hukumar yaki da fataucin mutane (NAPTIP), reshen Katsina, sun bankaɗo wata ƙungiyar masu safarar mutane tsakanin jihohi.

Jami'an NAPTIP sun kuma samu nasarar ceto wasu 'yan mata guda uku da aka yi safararsu kuma aka tilasta masu yin karuwanci.

Hukumar NAPTIP ta ceto mata 3 da aka yi safararsu daga Kudu zuwa Katsina, aka tilasta su yin karuwanci.
Shugabar NAPTIP, Binta Bello ta ce za a dauki mataki kan otel din da ke taimakawa safarar mata a Katsina. Hoto: @naptipnigeria/X, Sani Hamza/Staff
Source: UGC

An ceto mata 3 a dakin otel din Katsina

Kara karanta wannan

"Ina lalata da maza 600 a wata": An ji ta bakin budurwa da ke karuwanci a Katsina

Vincent Adekoye, mai magana da yawun NAPTIP, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 9 ga Yulin 2025, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NAPTIP ta ce ta kuma cafke wasu mutane uku da ake zargi da kasancewa mambobin kungiyar, wadanda ke dauko mata daga Kudu zuwa Arewacin Najeriya.

Sanarwar Vincent Adekoye ta nuna cewa wannan kungiyar ta kware a safarar mata daga sassa daban-daban, tare da tilasta su yin karuwanci a Katsina da jihohin Arewa.

Sanarwar ta bayyana cewa an kama waɗanda ake zargi ne a wani shahararren otel a cikin birnin Katsina (wanda ba a bayyana sunan ba), inda aka kuma ceto matan uku.

Hukumar ta cafke manaja da wasu ma’aikata biyu na otal ɗin a yayin samamen. Sanarwar ta ce matan da aka ceto, waɗanda shekarunsu ke tsakanin 21 da 26, sun fito ne daga jihohin Benue da Ribas.

NAPTIP na aiki don dakile safarar mutane

A cewar hukumar, wannan samame ya biyo bayan wani umarni da shugabar NAPTIP, Binta Adamu Bello, ta bayar na ƙara ƙaimi wajen sa ido da tattara bayanan sirri domin dakile yawaitar safarar mutane tsakanin jihohi.

Kara karanta wannan

APC: 'Yan siyasar Arewa sun fara neman kujerar Ganduje gadan gadan

Jaridar Punch ta rahoto Vincent Adekoye ya ce:

“Shugabar hukumar ta bayar da umarni tun da farko cewa jami’an NAPTIP su mayar da hankali kan abin da ke faruwa a otel-otel, wuraren shan giya a birane domin bankaɗo hanyoyin aikata wannan laifi.”

Ya ƙara da cewa a lokacin samamen, an gano matan a wasu ƙananan ɗakuna marasa tsafta, sanye da kaya masu fitar da tsiraici a cikin otal ɗin.

An jinjinawa jami'an NAPTIP kan bankado masu safarar mutane a Katsina
Wasu daga cikin jami'an hukumar NAPTIP yayin da suke sauraron jawabi daga shugabarsu, Binta Bello. Hoto: @naptipnigeria
Source: Twitter

NAPTIP za ta gurfanar da otel din Katsina

Shugabar NAPTIP, Binta Adamu Bello, ta yi Allah-wadai da rawar da wasu masu otel ke takawa wajen sauƙaƙa aikata safarar mutane.

“Ina so in yaba wa jami’an NAPTIP a Katsina kan wannan samame da kuma ceto waɗannan matan. Labarinsu yana da raɗaɗi kuma abin takaici ne.
“An ruɗe su, aka ɗauke su, aka yi safararsu, aka kuma tilasta musu shiga karuwanci. Duk da azabar da suke fuskanta kullum, waɗanda ke cin moriyar lalata da su na zaune a otal ɗaya da su suna more rayuwa."

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda sun gwabza fada da 'yan bindiga a Katsina, an rasa rayuka 36

- Binta Bello.

Ta ƙara da cewa za a ɗauki matakin doka kan otel ɗin da ya kasance cikin wannan aiki.

An kama mai safarar 'yan mata don karuwanci

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar shige da fice ta kasa (NIS), ta kama wata mata da ta shahara wajen safarar yan mata zuwa kasashen waje domin sana’ar karuwanci.

Hukumar ta ce matar da aka cafke a kan iyakar Najeriya da kasar Benin ta saba yaudarar yan mata tana kaisu kasar Benin da sunan sama musu aikin yi, amma sai su buge da karuwanci.

An ce a duk lokacin da 'yan matan suka yi yunkurin tserewa ko barazanar zuwa wajen hukuma, sai matar ta yanki gashin gabansu, hammata da kansu ta yi masu asiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com