Yanzu-yanzu: An ceto 'yan matan Najeriya 30 daga kasar Mali

Yanzu-yanzu: An ceto 'yan matan Najeriya 30 daga kasar Mali

Mata 30 ne 'yan Najeriya suka dawo daga kasar Mali bayan shekarun da suka dauka a can. Jaridar The Nation ta gano cewa wata kungiyar taimakon kai da kai ta kasashen duniya mai suna International Organization for Migration ce ta tallafa wajen dawo da matan bayan mummunan kalubalen da suka fuskanta a Mali.

Wasu daga cikin matan sun bayyana yadda aka hana su fita kasar tun daga filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas bayan an zargi cewa safararsu za a yi.

Wakilin jaridar The Nation ya gano cewa wasu daga cikin 'yammatan sun je har kasar Mali a mota ne kuma sun sa ran tsallakawa Turai ne amma aka yaudaresu aka ajiye su nan. A kasar kuwa suka fada miyagun hannu inda aka tirsasa su yin karuwanci.

DUBA WANNAN: Kotu ta yankewa tsohon kwamishina hukuncin shekaru 19 a gidan gyaran hali

Wani babban jami'in hukumar shige da fice wanda ya tabbatar da dawowar 'yammatan ya ce sun shigo Najeriya amma ba a riga an mika su ga hukumomin da suka dace ba don shawara tare da mika su ga danginsu.

Amma kuma ya ce a ranar 23 da 24 na watan Janairu 2020 ne aka hana wasu 'yan Najeriya 9 barin kasar a filin sauka da tashin jragen sama da ke Legas, a hanyarsu ta tafiya kasar Lebanon da Dubai.

Ya yi bayanin cewa ana samun irinsu da yawa amma ba dole jami'an hukumar shige da fice su kama su duka ba, sai dai suna sa ido a kan masu safarar jama'a.

Ya yi bayanin cewa akwai bukatar wayarwa da matasa kai tare da ganar da su cewa hakan zai iya gurbata rayuwarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel