Dubun mai safarar mata zuwa Turai ya cika

Dubun mai safarar mata zuwa Turai ya cika

Dubun wata ta da ta yi kaurin suna wajen safarar 'yan mata zuwa kasashen Turai domin yin karuwanci ya cika, matar mai suna Franca Asemota na yaudarar ‘yan mata zuwa Turai da karairayi, daga karshe ta mayar da su karuwai.

Jaridar Daily Mail ta Ingila ce ta bayar da labarin kama Franca Asemota ‘yar asalin Benin jihar Edo, ‘yar shakara 38, wacce ke safarar ‘yan mata daga Najeria zuwa Turai ta filin jirgin saman Heathrow.

Dubun mai safarar mata zuwa Turai ya cika
Franca da jami'an tsaro a lokacin da ake iza keyarta zuwa Najeriya
Dubun mai safarar mata zuwa Turai ya cika
Franca da jami'an tsaro a Ingila a lokacin da ake iza keyarta zuwa Najeriya
Dubun mai safarar mata zuwa Turai ya cika

Antie Franca kamar yadda ake kiranta, ta yi safafar sama da ‘yan mata 40 zuwa kasashen Turai ta Ingila, a inda ta ke dauko ‘yan matan daga gaban iyayensu a kauyukan Najeriyada zimmar cewa za ta samar musu kyakkyawar rayuwa a Turai, amma da zaran ta raba su da gida, sai ta jefa cikin kangin karuwanci da bauta.

Dubun mai safarar mata zuwa Turai ya cika
Dubun mai safarar mata zuwa Turai ya cika

Wata kotu a Ingila ce ta samu Franca da laifukan da ake tuhumarta da su guda takwas, wandanda suka hada da safarar mutane, da kuma cin zarafi; dubun ta ya cika ne a watan Satumbar shekarar 2011 a inda a lokuta daban-daban yi safarar mata zuwa rukuni-rukuni.

Mai gabatar da kara ya bayyana cewa Franca na tirsasa ‘yan mata ne idan sun isa kasar waje ta hanyar barazana ga rayuwarsu da amfanin da boka sa tsibbu idan ba su bata hadin kai ba. An kuma iza keyar ta  zuwa Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel